shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-31 32 33 34

rayuwar-fauziya.jpg

[8/16, 3:41 PM] Abba~Gana: 30RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (30). Fauzy karki
damu da yaddar ALLAH itama zata amince da
samun farin cikinki, kidena fidda rai da samun
farin ciki ko jindad'i ke dabance ALLAH
yanasonki kuma Mama ma zatasoki da yaddar
ALLAH, "Farouk ka amincewa maganata wllh
zuwa wajen Mama babu abinda zai haddasamin
sai tashin hankali da baqin ciki tare da bankwana
da kai, "Fauzyna kidena zubar da hawaye komai
ya wuce, na amince muje wajen Abban, don
ALLAH kidena tashin hankalinki kllm ina burin
naganki cikin farin ciki, haka muka dinga hira
cikin tarairaya da fahimtar juna. Farin ciki bazai
misaltuba cikin raina, haka nasanar da Aunty
Sadiya duk yadda mukai tayi murna sosai
tadinga bani hkr akan nadaure na koma wajen
Mama, kawai na amince mata da to amma badan
zan aikata ba, da yamma li'kis nai sallama da
Aunty Sadiya na tafi gidan Abba Tijjani cikin
tsananin farin ciki. Na sanar da Abba komai da
ya faru amma ban fad'a masa dalilin barina
gidan Fa'iza ba, kawai nafad'a masa nagaji km
Farouk yanaso yazo mutsaida maganar Aureyayi
farin ciki sosai da maganar Farouk amma yayi
takaici da baqin cikin halin ko inkula da Mama
take nunawa akaina, wanda har takai yau ta wayi
gari tana mai alfahari da salwantarki batare da
tasan inda zaki ba, Fauziyya tabbas bata kyauta
ba amma da kinyi hkr wata rana sai lbr, wllh
itace Mahaifiyarki baki da wata bayan ita, ina da
ikon Aurar da ke kota amince ko bata amince ba
amatsayina na wan Mahaifinki, amma bazanyi
hakan ba dole anemi amincewarta da sa
albarkarta, zanje wajenta bazanyi 'kasa
agwiwaba kuma insha ALLAHU zamu samu
nasara, ke tawace dolene nanema miki farin ciki
amma idan ta Haj. Khadija da sauran yaranne
idan nace nacire hannuna akansu ba wanda ya
isa yace sai na mayar, ki cigaba da addu'a
Fauziyya ALLAH yana tare da ke kuma shizai
dafa miki.......
[8/16, 3:42 PM] Abba~Gana: 31RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (31) Cigaba 31.
Na amincewa Abbane badon son raina ba sai
don bin umarninsa, wanda yazamo ko mahaifina
baya ja da hukuncinsa ballantana ni, mutum ne
me taka-tsan-tsan da duniya dattijon 'kwarai me
magana 1, Kwana na 2 agidan Abba gidansu
Farouk suka aiko zasu had'o komai su kawo,
haka ya amsa musu da sharad'in zai sanarwa
Mahaifiyata kafinnan, Abba ya shirya ya tafi
wajen Mama da Maganar da kowacce uwa take
burin ji, amma nasan banda tawa uwar don
nasan yafi komai ba'kin ciki awajenta, tunda
yatafi nake addu'ar ALLAH yasa alkhairi ne yake
cikin tafiyar ba akasinsa ba. Abba yafad'amin
tun sallamar da yayiwa Mama ya tabbatar da
alamun rashin nasara atare da ita, ta amsane
aciki cikin rashin girmamawa batare da tasan
maganar da yazo da ita ba, alkcn da ya tabbatar
mata cewa Fauziyya tana gidansa lkcn tafara
zazzaga bala'in shi yake zugani nake yi mata
abin danaga dama, koda ya tunkareta da
maganar Aurenmu saita sake rantsewa ko
gawata bata amince Farouk yata6a baballantana
ya aureni, ya tabbatar mata da kamala dattako
da gidan mutunci da Farouk ya fito, sbd hk bashi
da aibun da za'a hanashi aurena tunda muna
'kaunar junanmu. Amma Mama saita d'aga waya
ta kirani ina ganin kiran gabana yafad'i, cikin
tsoro na d'aga wayar tare da sallama nakira
sunanta cikin girmamawa, bata amsa sallamar
ba ballantana kiran, FAUZIYYA takira sunana da
babbar murya, na amsa cikin nutsuwa, babu ke
babu Farouk har abada narantse da girman
ALLAH babu yawuna a maganar da Tijjani yazo
da ita, idan kuma kikayi kingama samun
kwanciyar hankali arayuwarki, kuma sai kinyi
nadamar zuwa duniya don wllh bazan gagara
tsine miki da dukkan alkaba'in duniya ba, inaso
kisani Tijjani ba ubanki bane don hk bai isa yayi
takara da ni wajen gindaya miki sharud'd'aba,
ballantana har ya halasta abindana haramta
miki, ina baki umarnin ki tattaro inaki inaki kizo
inason ganinki yanzu yanzunan, idan kuma zaki
nunamin ban isaba to karkizo, wllh idan kika
sa6a maganata bazan ta6a yafe mikiba, kuma
babu ni babu ke har abada! Ta katse wayar cikin
zafi..... (kuyimin afuwar jina shiru dalilaine masu
kwari suka haddasa hakan, ina fatan ba kuyi
fushi ba km kowa yana cikin 'koshin lfy. Ina
tayaku murnar shiga sabuwar shekara, 1st
muharram. Allah ya baiyana mana alkhairan
dake acikinta, abinda ke cikinta wanda ba na
Alkhari ba, Allah yajuyamana shi zuwa na
alkhari). Ahlan wa sahlan bikum fil muharram,
wa Kul'am wa antum bikhair!!!
[8/16, 3:43 PM] Abba~Gana: 32RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (32) Cigaba 32.
Wani irin juyi naji kaina yanayi lkc guda zuciyata
ta cika da wani irin 'kunci tana tu'ku'ki atake nai
jifa da wayar ta tarwatse, na tsuguna 'kasa ina
rawaito kukan ba'kin ciki da takaici, haqiqa bani
da za6i da ya wuce nabi umarnin Mama ina da
tabbacin umarnin mahaliccina ne kawai asaman
nata, lallai Mama bata 'kaunata bata farin ciki da
farin cikina zanje gareta kamar yadda ta buqata
km zan kasance cikin bin umarninta na tabbata
mutuwata tana gaf da ni, wnnn kuwa bata isa ta
hanaba saidai tai farin ciki ma da hakan, bazan
'kara zuwa wajen kowa don kai 'karar Mama ba
har tai masa irin wannan rashin mutuncin data
yiwa Abba, bayan nuna bai isaba tazo tana kiran
sunansa gatsal cikin raini, ya ALLAH ka ganar da
Mama kasa tagane kuskurenta ta daina abin da
take. Tunda na tsuguna kuka nake ina ta karanto
wasi'kar jaki da addu'oin mafita cikin zuciyata...
"FAUZIYYA! Naji muryar Sumayya d'aya daga
cikin 'ya'yan Abba tana kiran sunana, ban
sauraretaba don banga abinda zaisauqaqamin
zuciya na iya magana ba, "kukan me kike haka?
Ban kalleta ba ballantana na tanka mata, "ga
waya Abba yace na baki, da na yanke hukuncin
'kin kar6a ballantana na amsa, don nasan wani
zafin zan 'kara samarwa zuciyata, na tabbata
magana d'aya Abba zai fad'amin itace nabar
gidansa yanzu-yanzu sbd 6acin ran Mama,
"Fauziyya ya'kara kirafa sumayya tai maganar
cikin damuwa tana kokarin kara wayar akunnena,
nadafe wayar akunne bankai ga magana ba naji
yace "Fauziyya karki daddara kibar gidannan
kizauna cikin farin ciki da aminci, Mahaifiyarki
bata isa ta hana abinda ALLAH ya halasta ba,
babu abinda bakinta zai miki sai alkhairi, ki
kwantar da hankalinki ita bata isa ta d'aura miki
aureba saida mu, ni kuwa na isa aurar da ke
batare da ita ba. Nidai kukana kawai nake ina
jiyo muryar mama tana ihun cewa wllh baka
isaba, yana cewa zakisha mamaki zan nuna miki
isata da matsayina awajen 'ya'yanki, don kinga
ana bin ta taki yasa kike abinda kikaga dama,
baki da abokin shawara ko a'kawayenki don
dabbancida ka kike komai, to wllh ALLAH yabaki
dama ne kawai ranar nadama tananan tana
tunkaroki, yana maganar cikin huci da takaici
"Fauziyya ki kwantar da hankalinki ni
mahaifinkine awnnn lkc, karki damu da abinda
yake faruwa akwai lkc, bansan lkcn dana fashe
da kuka ina fad'in Abba na hakura da auren zan
koma wajenta don ALLAH Ab... Rufamin baki
nafad'a miki karki sake kibar gidannan idan kika
fito to duk halin da kika fad'a dad'i ko wahala ba
ruwana, ina umartarki kizauna nadawo babu
abinda zai faru sai alkhairi, ya katse wayar
nasake fashewa da kuka, zuciyata ta rabu biyu
tanason kyautatawa kowanne 6angare, can kuma
wani saqone yake yawo a'kasan zuciyata akan
me zan za6i zama da Farouk akan Mama? Bayan
nasan maza basu da tabbas? Na tabbata idan na
Auri Farouk to ba ni ba Mama km saita rabani da
'yan uwana har abada, hakama baikamata na
sacewa Abba gwiwa ba, zan jira yazo in kuma
ro'keshi akan kawai ya janye na ha'kura
33RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (33) Cigaba 33.
Koda Abba yadawo nagama had'a kayana tsaf
amma idona yakasa dakatawa da zubar da
hawaye, hk ya aiko aka kirani yana falonsa, na
amsa na tafi nasameshi zaune alamun me
nazari, nayi sallama natsuguna cikin ladabi da
murya me rauni nace: "Abba sannu da zuwa,"
yawwa sannunki ya amsa yana kokarin gyara
kafet d'in da yake zaune akai. "Fauziyya! Abba
yakira sunana fuskarsa ad'an sake bakamar
farkon shigowata ba, na amsa cikin nutsuwa
kaina a 'kasa duk da hawayen ya tsagaita zuba
daga cikin idona amma akumbure suke, "Gobe
gidansu Farouk zasu kawo komai na aurenki sati
mai zuwa za'a d'aura muku aure in ALLAH
yakaimu sati na sama ku wuce, "Abba kayi
hakuri wllh na ha'kura da auren Farouk har
abada don ALLAH Abba kajanye, ina maganar
hawaye yana sauka kan kumatuna," Fauziyya ki
kwantar da hankalinki babu abinda zai biyo baya
sai alkhairi, Mahaifiyarki kawai haifarki tai amma
bata amsa sunan uwa tagari ba, babu laifi don
lkc d'aya kin kaucewa Umarninta tunda ba hani
tai da abindaya halasta ahana ba, kawai tabi son
rai da hud'ubar shaid'an da kuma amfani da
matsayin da ALLAH yabata akanki don ta
musguna miki, kisani babu abinda ya kaucewa
shari'a ballantana yazamo haramun a aurenku da
Farouk, yadda nayi bincike akansa mu'amalarsa,
tarbiyya da addininsa na tabbata batayi wnnn a
auren Fa'iza ba, idan aka biyewa shashancinta
wllh zata iya jefa ki ahalaka, shekarunki sunyi
nisa aurene yafi kamantuwa da ke ayanzu, babu
bi ga abin halitta wajen sa6awa mahalicci, ki
manta da komai kita addu'a ALLAH zai dafa
miki, Abba Mama Mahafiyyata ce ko bataimin
komai ba takawoni duniya km tasha wahalar
laulayina da na'kuda ta, ta cancanta na sadaukar
da komai na farin cikina don kyautata mata,
Abba har cikin raina na ha'kura da Farouk don
ALLAH Abba kaima ka hakura ALLAH zai kawo
lkc na... Wllh barazana take bazakibar 'kasarnan
ba sai kinje kunyi sallama, kuma zata yafe miki
Fauziyya karki yadda zuciyarki ta aminta da
barazanar mahaifiyyarki, idan har kika rabu da
Farouk na tabbatar miki bazaki ta6asamun miji
kamarsa ba, hk muka dinga musayar yawu
nafad'a ya fad'a dole tasa nai shiru don dole
badon na amince da abinda yake so ba, nakoma
cikin gida zuciyata cike da tunanin gaggauta
samun mafita. Kwanaki 4 da tafiyar Fauziyya
daga gidan Aunty Sadiya, Fadila tazo gidan tana
bata labarin cewa Fauziyya ta koma gidan Abba
Tijjani har zai aurar da ita bada izinin Mama ba,
sbd tace batason yaron da Fauziyyan takeso tace
bata yadda da tarbiyyarsa ba, Aunty Sadiya ta
nuna bata san komai ba tace tadad'ema bataga
Fauziyya ba, ta dinga surutai kala-kala harda
cewa Mama tace idan kud'i yana aiki Malamai
suna doron 'kasa auren nan bazai yi wuba, Aunty
Sadiya tace ai da Mama ta hakura tunda sun
dage ba'a san abinda ALLAH yake nufiba, tace
haka ma 'kawarta tace amma Mama ta'ki yarda,
ai Aunty Sadiya duk laifin Fauziyarne gwara
Maman tayi maganinta ta cika matsala da yawa,
zantuka dai daban-daban. Alkcn BB tana hannun
wane da wane ranar da ita Fadila taje gidan
Aunty Sadiya Q10, koda ta yaba wayar da irin
kyanta datsadarta, sai Fadilan tace Mijin Fa'iza
ne ya siyo mata, sbd halaccin da tayi masa na
zama agidansa lkcn da Fauziyya ta gujesu, wllh
Aunty Sadiya tace lkc guda gabanta yayi
mummunar faduwa, kawai ta tausayawa Mama
da iyalanta lallai Fauziyya dabance acikinsu, don
ta tabbatar bazai bata wannan wayar abanza ba,
ta kalleta da alamun rashin fahimta tace "Fadila
kawai yabaki waya? Ke da Fa'iza? Tace a'a ni
kad'ai ita ai tana da wata Nokia ahannunta,
Aunty Sadiya tai ajiyar zuciya tace "gsky ya
birgeki kice Mama tayi murna, Fadila ta kalleta
cikin zumud'i tace "murna kai yadda kikasan ita
aka bawa tadinga cimin albarka da gdy agurinsa,
tace taso Fauziyya ta gani taga arzi'kin data
gujewa, ai Aunty Sadiya Ya Nura yana da kirki
sosai abin hannunsa bai rufe masa ido ba, ita dai
Aunty Sadiya kawai kallonta take tana mai
takaicin son zuciya irin nasu.
[8/16, 3:44 PM] Abba~Gana: 34RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (34) part (34)
Tunda na baro wajen Abba na kasa samun
sukuni lissafin 'kwa'kwalwata ya gagara sai
tuwa, tsahon ranar da darenta haka nakasance
cikin damuwa ina addu'ar ALLAH ya shige min
gaba a abinda yake alkhairi, da safe naje muka
gaisa da Abba yana sake jaddadamin cewa yau
za'ayi ba'kin gidansu Farouk na amsa da to
kawai nami'ke daga gabanshi nakoma babban
falo. A kwance nake kan doguwar kujera idona
kan wani hoton Abbanmu da Abba Tijjani da
wasu 'yan uwansu sunsa mamansu atsakiya,
hoton yayi kyau sosai musamman Abbanmu da
ya yalwata fuskarshi da murmushi, kana gani
kasan suna alfahari da mahaifiyarsu, hawaye
yacika idona, ina tuno rayuwar gidanmu da
mahaifinmu mai dad'i da nishad'antarwa,da
kulawarsa ga 'yan uwansa bashi da kokarin da
ya wuce yakyautata mana, bansan tashin hankali
da damuwa ba sai bayan rasuwarsa, nasiharsa
kllm agareni nazamo mai hkr musamman akan
Mahaifiyyata bau d'add'iyar Mace ce sai na kau
da kai akanta, duk rintsi duk wahala karna 6ata
raina akanta na ri'ke'yan uwana da zumunci,
Abba Tijjani ubane awajenmu karmi wasa da duk
wani umarninsa don bazai cutar damu ba! ALLAH
sarki Abba ka barni cikin maraici da
hargitsatstsiyar rayuwa, nagaza da samun
ingantacciyar rayuwa daga mahaifiyata
ballantana 'yan uwana, lkc yayi da Mama take
baqin ciki da Farin cikina, take 'kaunar rabani da
masoyina take jaddada tsinuwarta akaina idan na
bijirewa umarninta da yazo da son ranta, Abba
inama kana da iko dakazo ka rabani da wnnn
rayuwa, kajani gareka don nisantani da irin
wannan rikicin rayuwa, na rasa mafitar dazata
kaini ga gaci, Umarnin Mama zanbi ko kuwa na
Abba Tijjani? Ya ALLAH kazamo gatana awnnn
al'amari. Ina falon Abba yashigo batare da
nakula da shigowarsa ba, sai muryarsa naji yana
kiran sunana, nad'ago na goge hawayen fuskata
na tsugunar da kaina, kukan me kike Fauziyya?
Abba bakomai, nabashi amsa, sannan nace
"amma inaso naro'keka wata alfarma, "ina
sauraronki ya samu kujera ya zauna" na sakko
'kasa cikin ladabi da girmamawa natsuguna nace
"Abba zuciyatata raunana tana neman tallafinka
da amincewarka, don ALLAH Abba ka yaddarmin
naje wajen mahaifiyata wllh bazan bari tahanani
auren Farouk ba, inaso ta yafemin ayi aurennan
da amincewarta, nasamu farin ciki kamar yadda
kowacce amarya take samu... Fauziyya na
amince miki amma da sharad'in sai an d'aura
aurenki kafin ki tafi sai kije amma ban yarda
kitafi ayanzu ba, sbd hk daga yau na yanke duk
damuwa daga gareki ki saki ranki kiyi harkar
bikinki cikin nishad'i zaki samu farin ciki fiye
dana amarya da take gaban iyayenta, yanzuma
farouk ne yake tambayar ko akwai wasu al'adu
da muke? Nafad'a masa ta 6angaren iyaye bamu
da wasu al'adu da suka sa6a nasu saidai ko
daga gareki, yakira wayarki akashe ki kunna ki
kuma amsashi kamar yadda kika saba, da yaddar
ALLAH aurenki da Farouk alkhairine kinji 'ya ta!
Yana gama fad'a yafice cikin sauri ya barni
atsugune, na tashi nakoma kan kujera ina mai
addu'ar ALLAH ya sanyaya zuciyar Mama ta
sassauta 'kudurinta, donna tabbatar Abba ya
rinjayeta. Yau itace ranar Farin ciki da nishadi
ranar da kowacce mace take alfahari da ita,
ranar da tafi kowacce rana tarihi da girmamawa,
an d'aura aurena da masoyina abin alfaharina da
jindad'ina wanda nadad'e ina burin ya zamo
uban 'ya'yana, Farouk yayirawar gani ya kashe
kud'i sosai wajen aiwatar da komai na bikin, nayi
kuka kamar raina zai fita nayi kewar mahaifina
don nasan yafi kowa buri da son ganin wannan
rana. Babu lallamin da masu fad'a aji na dangi
ba suyiwa Mama ba akan ta ha'kura ayi biki
babbar 'yarta cikin kulawarta amma ta'ki, ta
nuna gwara taga ranar mutuwarta da ganin wnnn
ranar, an aika masu da komai na kayan aure har
IV amma ta wulaqanta komai da duk wanda aka
aika wajenta. Kwana 2 da d'aura auren Farouk
yace na shirya muje muyiwa Mama sallama, sbd
komai ya kammala saura kwana 4 ya rage mu
wuce DUBAI, lallai bani da farin cikin da ya wuce
Mama ta yafemin, fatana aurennan yazamo silar
warwarar damuwata ya ALLAH ka amincemin da
hakan...
Share:

3 comments:

 1. Maryam ali ahmed5 May 2016 at 11:08

  Gsky Muma Muna Tayaki Addu'a Allah Yasa Tayafe Miki Mun Gode

  ReplyDelete
 2. Kedai rike allah

  ReplyDelete
 3. Zeenat ab mu'azu9 October 2016 at 10:21

  Allah karamu da muguwar uwa

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive