shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 31 October 2015

AL'AMARIN ZUCI 1-2-3-4 & 5

al-a-marin-zuci.jpg

[12:38PM, 9/30/2015] Billygiro: AL- AMARIN ZUCI
Na Bilky Giro
1Alhj hassan,Alhj Hussain,Alhj isma'il 'yaya ne ga Alhj usman mai nera, matar sa daya tak Hajiya Zeenatu ita ce uwar 'ya'yansa. Sun kasance suna zama ne a cikin garin zamfara.

Wannan family Kansu a hade yake, hakan ne ma yasa suke zama a gida daya sai dai kowa da nashi part
Saboda gidan babban gida ne sosai , iya haduwa gidan yahadu, kasancewar Alhj usman mai nera hamshakin mai kudi ne sosai gashi ya kasance shi mutum ne mai son jama'a da taimakon talakawa.

Haka ma duk 'ya'yansa ba bare a ciki, domin ko wannesu Allah ya hore masa dukiya,dukiya kuwa abinda ake kira dukiya domin duk wanda yaga family din yasan dala ta zauna ba sai an gaya masa ba.

Alhj Hassan shi ne babba matarsa Hjy Fatima 'ya'yansa biyu maza faruk da Hafiz.
Alhj husain shi ma matar sa daya Hjy zainab, sai dai har yanzu Allah bai basu Haifuwa ba.

Alhj isma'l matansa biyu Hjy saratu da Hjy khadija 'ya'yansa hudu duk maza,Hashim,yusuf,'ya'ya ga HjySaratu.
Salim,Ali 'ya'yan Hjy Khadija.

Zaman da suke zama ne mai hade da hadin kai da kwanciyar hankali ba'a cika jin kansu ba.
Written by Bilkeesu Giro
[12:38PM, 9/30/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
2faruk shi ne mai dan girma a cikin 'yayan,akalla yanzu yana shekara 9, yana primary 5 ne a yanxu.

Amma idan yana fitar da lafuzzan turanci,kamar a secondry yake,gashi kyakkyawa fari tas dashi ga natsuwa da hankali,shiga rai shi yasa a familyn duk anfi ji da shi.

Faruk ne zaune yana jiran fitowar momy (zainab )ummanshi ce ta aiko shi da dan wake yakawo mata.
Yauwa dana, kace mata na gode,ya mika mata kulan ya fita,tayi zaune domin taci, sai dai yajin yau ba yawa, kiranta a waya tayi maman faruk ya akayi yau yajin ba yawa.....naga alamar so kike ki cutar muna da baby shiya sa na fara rage yajin,ko dan kinga mijin baya nan ne...ai bai ko san da cikin nan ba....ke haba meyasa,kinsan indiya yaje,idan nagaya masa bazai ma bari yayi abinda yaje yi ba sabida tsananin murna,kinsan mun shekara goma da aure ba haifuwa,haka ne fah Allah ya bada masu albarka,amin,amin nagode.
Written by Bilkeesu giro
[12:38PM, 9/30/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Billy giro
3Yau ne Alhj Hussain (Daddy)zai dawo daga indiya,Momy sai shirshiryen tarbonsa ta ke,ta kammala abinci ta shirya tsaf tayi kyau sosai tana sanye da wani blue din material mai ratsin fulawa pink jiran isowar sa kawai take,da yake yace mata karfe 1:00pm zasu sauko gashi yanxu daya saura, tadan kishingida
Kafin ya iso.
A cikin barcinta da bai riga yayi nisa ba taji sallamar sa,da saurin ta tashi ta rungume shi,tamai sannu da zuwa,sai kallon ta yake yanda ta kara mishi kyau....yadai kallon fa, kinga yadda kika kara kyau,haske,cika, ko ni dana je indiya albarka...um um fah,Allah kuwa,kunnensa ya tara a bakin ta, gaya min meye sirrin,ni dai ba wani sirrin muje kaci abinci akwai lbr mai dadin ji,da gaske ?eh.
Ya gama cin abinci yayi wanka suna kwance suna firar ya bayan rabuwa...yauwa baki fada min lbrn ba,to rufe idonka na gayama, tooo....,wannan wane irin lbr ne haka da sai na rufe idona, kai dai nace ma ka rufe,to na rufe, Allah ya karbi addu'ar mu da muka dade munayi domin yanxu ina dauke da juna biyu .....da gaske!! Allah kuwa,tana magana ne a cikin jin kunya,rugumar ta yayi yana mata kiss ta ko ina,yayi sujjada yana mai cewa "Allah na gode ma da kasa zan ga kwai na a dunya,Allah ka bamu masu yawa masu albarka, kuma kasa muna da yawancin rai.
Written by Bilkeesu giro
[12:38PM, 9/30/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
4Amin mjina.....bari naje na gayama family wannàn abin farinciki....ai kowa ya sani,ya akayi su ka sani, domin na san ki da kunya baza ki iya fada ba ,zazzabi ne mai tsanani nayi kamar bazan yi rai ba,sai da muka je asibiti,bayan an dubani suka ce ina dauke da juna biyu,baka ga yanda family ke murna ba hardai Hajiya da Alhaji....to ni meyasa ba'a gayamin ba sai yanxu?

Saboda ina so ne na baka surprise,zaka fi farin ciki, kuma nasan idan na gayama baza ka bari ka, karasa
abinda kaje yi....Allah kuwa da ranar zan dawo ba shiri.

Haka rawu taci gaba domin yanzu momy haifuwa yau ko gobe.

Faruk ne da sallamar sa tare dan rissinawa ya gai da momy,ta amsa sallamar tare da amsa gausuwar.
Written by Bilkeesu giro
[12:38PM, 9/30/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
5 Halan dai anzo ayi magana ne da kanwar?eh mommy.
Da yake tun lokacin da cikin mommy ya fara girma kusan kullum sai ya zo ,wai magana su ke yi da kanwarshi ta cikin cikin,ni Billy giro abin har mamaki ya ke bani.

ya naga kamar ranka a bace faruk,wasu ne suka bata min rai a school wai baza ki haifa min kanwa ba sai dai Kane,ni kuma ai nasan Allah shi ne maiyi ......kuma a kullum nayi sallah sai na roki Allah ya bani kanwa...to kasan da haka kake bata ranka a banza faruk, ni ma kawai na tsinci kai na ne da ance kane zaki haifa min sai inji raina ya baci tunda kannaina duka maza ne ina so na sami kanwa.......haka ma wasu na can na neman da namji,basu samu ba....to Allah dai ya ba ka kanwa amin mommy.
Hanun sa ya dora a cikin momy,yana mai cewa.
"Kanwa ta wai sai yaushe xaki fito a daina mun gori,mu rika yawo tare'yan ajinmu su dai na minkurin kanwa,nima na rama...hmm kai dai kullum baka gajiya kana magana da abinda bai ko xo duniya ba.... lah kinga umma tana motsi ...duk abin nan da akeyi a idon daddy ne sai dai ba wanda ya ganshi,murmushi kawai ya keyi,ya jingina a bakin kofar.

Umma ce ta fara hango shi tsaye yana kallon su cike da sha'awa....a'a Alhj kai ne a tsaye sai faman kallon mu kake nida dana....danki mai kanwa
..ai inaganin idan baki haifi 'ya mace ba,bansan ya faruk zai yi ba.

Allah dai ya taimaka ki haifo macen,amin ya Allah.

Written by Bilkeesu giro

www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive