shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 22 October 2015

RAYUWAR***FAUZZIYA-2

rayuwar-fauziya.jpg

2RAYUWAR (FAUZIYYA)part (2)
Cigaba. Mahaifina Alh. Tukur muhammad Naira,
shahararran mai kud'ine km d'an siyasa , ya ri'ke
kwamishina shekara7 yanakan mi'kamin ALLAH
yai masa rasuwa, tun kafin yazamo d'an siyasa
dama yana da kud'insa, hakama mahaifiyarmu
Haj. Khadija Tukur Naira metrom ce ababban
asibiti na jiha, ni Fauziyya nice babba duk da
akwai 'yar uwata wadda muka shigo duniya tare
wato fa'iza, FAUZIYYA da FA'IZA mu 'yan biyune,
sai FAHAD da yake binmu sai FADILA sannan
FAISAL sai kuma FARIDA da autanmu Amir
(Abdallah) wanda shine yazamo bare arukunin
sunayen gidanmu na F, mu bakwaine uwarmu
d'aya ubanmu d'aya, tsananin kamar da muke da
Fa'iza yasa mutane da dama basa iya ganemu,
tad'an fini 'kiba kad'an amma dukkanmu bamu
da girman jiki, dake Fahad namijine yafimu girma
nesa ba kusa ba, hakama FADILA wadda take
yarinya 'karama akanmu itama ta taso da tsaho
da 'kibarta, gata kyakkyawa fara kallo d'aya zaka
yiwa FADILA kasan ta amsa sunan kyakkyawar
mace me diri da sauti mai dad'i A manyan
makarantu masu tsada mukai karatunmu
Abbanmu bai ta6a raba mana komai ba,
tsakanina da Fa'iza komai iri d'aya hatta
makaranta aji d'aya muke tafiya har muka shiga
JAMI'A course d'aya, halinmu yabanbanta da
Fa'iza mace ce mai rawar kai da son nuna ita
watace ga ji da kai, shiyasa kullum munfi shiri da
Abba don nice 'yar tsurkunsa duk abinda yafaru
agida nizan bashi lbr tun muna yara, babu irin
fad'an da mama batamin harda duka akan saina
dena fad'awa Abba abinda ake agida amma
na'ki, sbd wataran suna abubuwa marasa kyau
harda fita unguwa bai saniba, tun yana kautar da
idonsa har yafara nuna gajiyawarsa, alkc guda
kuma yafito da nuna soyayyarsa 'karara akaina,
har yana ikirarin duk yaransa ni nagaji halinsa da
nutsuwarsa, ga tausayi idan ya bamu kud'i muyi
amfani ni kad'ai nake dawo masa da chanji
amma banda sauran, ko sunyi yun'kurin
kawowama mamace zata 'kwace wnnn yabasu
dama suka cire tausayin Abba aransu, duk da be
rage musu komai ba. Tunda muka shiga JAMI'A
d'abiun Fa'iza suka 'kara 'karfi nikuma ALLAH
ya jarabceni da tsoronta, bata karatu kullum tana
tare da samari da wayayyun 'yan mata, kuma
tana mai gargad'in karna sake nafad'awa Abba
ko da wasa, haka nake kama bakina nayi shiru.
Muna shekara ta 2 a jami'ar Fa'iza tasamu
withdraw sakamakon kamata da manyan laifuka
da akayi ciki kuwa harda takardar satar amsa
dumu-dumu ahannunta, ga lambar da aka basu
na shed'anun d'alibai, lkcn da lbr yasamu Abba
nakorar Fa'iza yayi mamaki da takaici, don shi
mutumne da baya neman alfarma da kud'i ko
mi'kaminsa, haka dole yaje makarantar don jin
ba'asi tare da taimakon masifa da bala'in da
mama take mishi wai inda nice da tuni yaje ko ta
halin 'kaka an maidani, nidai nace bansan komai
ba akan korarta, haka yaje akadinga lissafa masa
abubuwan da take aikatawa, ransa ya6aci sosai
tun daga lkcn Abba yafara had'uwa da 6acin rai,
yace km ba abinda zai yi mata saidai ta zauna
agida, kllm cikin nasiha yake akaina tare da
addu'ar fatan alkhairi, yana mai gargad'ina akan
karna biyewa halinmahaifiyata dana Fa'iza duk
rintsi duk wahala, na kuma daga da kokari akan
nunawa 'yar uwata hanyar tsira.
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive