shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 22 October 2015

SIYAMA***13 & 14 {KARSHE}

siyama.jpg

: 13siyama

Shirya siyama tayi tana nazarin kalaman sakeena can ta nisa sannan tace toh sakeena idan ALLAH ya yarda zan gyara tace to ALLAH ya yarda anan dai suka sha hirarsu har mijin sakeena yace tafito su tafi haka suka rabu cikin kewar juna suna tafiya ta zauna tana ta tunanin kalaman sakeena azahirin gaskiya ba abunda siyama ta tsana irin kishiya don haka ta yanke shawarar zata gyara kuma zata koyawa zuciyarta son ya naseem tana zaune wayarsa tafara ringing tana zuwa taga ba suna kawai sai ta daga tana dauka taji mace ce sai taji tace don ALLAH naseem ka saurareni wlh inasonka kataimakawa zuciyata siyama wacce kishi yagama tsayawa a zuciyarta takasa magana kawai sai ta kashe wayar ta kwanta tafara kuka saiga shi nan ya shigo yana shigowa ya ganta tana kuka gabadaya yagama rikicewa yace siyama meyafaru cikin kuka tace yaya daman akwai wacce kake so nibasona kake ba nagode ta tashi ta tafi dakinta ta kulle kofa ya naseem wanda gabadaya jikinsa ya gama mutuwa shidai yasan baitaba soyayya ba sai akan siyama saiyaje ya dauki wayar sa ya duba last call dinsa tabbas yagane wacce takirashi wannan mayyar ce amina kawai sai yatashi yabi bayan siyama yadinga kwankwasa mata kofa amma taki bude masa itakuwa kuka kawai takeyi................

www.abbagana.pun.bz

: 14siyama

Dataga kukan bazai amfaneta ba saitakira sakeena abokiyar shawararta takira tafada mata abunda yafaru sakeena tace to kinga abunda nake fadamiki to ai ba fushi zakiyi ba zuwa zakiyi gurinsa ku sasanta kanku tace to ta tashi tasa wata riga mai shara shara wanda da ita da babu duk daya ne tashafa turarenta mai kamshi sosai sannan tanufi dakinshi tana zuwa ya taso ya rungumeta yace siyama wlh ke kadai nake so bantaba son wata ya mace ba kamar ke shiru kawai tayi ta kwanta akan kirjinsa daga nan kuma yafara mata wasu salon da ita kanta takasa gane a wace duniyar take daganan kuma suka kashe fitila ni kaina sai nabarsu nadawo falo inajiran gari yawaye
Da asuba ya tashi yayi wanka tabbas yau yana cikin farinciki mara misaltuwa ya kalleta wani irin sonta yake ji ya karu acikin zuciyarsa saikuma yaji tausayinta sbd yasan ta wahala sannan saiyakarasa inda take kwance yace honey tashi kiyi sallah tafarka yayi kissing dinta a goshi ita yanzu wata kunyarsa take ji ta tashi zata shiga toilet amma takasa tafiya daya rula da haka sai yadauketa ya kaita yasata acikin ruwa mai zafi harsaida taji dadin jikinta sannan yasata a towel ya daukota kamar wata jaririya sai yajasu sukayi sallah suka koma bacci yana rungume da ita sai 11:00 na safe suka farka tariga shi tashi ta tashi gabadaya tafiyarta ta chanja ta nufi kitchen tafara dora girki saitaji kawai an dauketa yace wayagayamiki amarya tana girki sunafitowa falo taga abinci shiyabata abaki haka suka gama cin abincin.
Bayan wata biyu ne ranar siyama ta tashi da zazzabi da ciwon kai duk ya naseem yagama rikicewa ya dauketa suka nufi asibiti suna zuwa likita yayi gwaje-gwajensa ya tabbatar data na da ciki wata biyu farinciki kuwa agurin ya naseem ba magana haka yakira yaan uwa ya sanar musu haka siyama tayi rainon cikinta ta haifi yan biyu mata aka samusu sunan Ammi wato Fatima dayar kuma aka samata sunan mahaifiya ya naseem wato halima ake kiran yaran nasreen da iftisan.

TAMMAT BIHAMDULILLAH

Follow me @

www.Abbagana.pun.bz
for more
Share:

11 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive