shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 31 October 2015

AL'AMARIN ZUCI 6---15

al-a-marin-zuci.jpg

[11:14PM, 10/1/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCI Na Bilky giro

11Amma akwai ki da abin dariya mimi,kinga yadda kika Fuske...ya baxan fuske ba kina min zance marar dadin ji, wanda ko a mafarki bana so haka ta faru.....da wasa nake miki fah,ya zanyi wanann tunanin nace yayan ki bazai aure ki ba, wannan soyayya haka...ni dai zancen ya isa haka,ko abin motsa baki ban kawo miki ba,duk kin bi kin birkita min lissafi,afwan cewar Zainab.


Momy ce zaune a falo Mimi kwance a saman kafafunta tana game a waya,nikuwa Mimi yaushe zaku fara waec da neco?a wannan watan mommy...amma baki da abinyi sai danne,dannen waya,ai Mommy duk dare kafin nayi barci sai nayi karatu,haba mommy na, ai kinsan bana wasa da karatu,haka kam amma ki kara dagewa kinji,inshaAllah mommy.

Abba!wai wa zai kaini school yau,kasan fa jarabawa ce damu bana so nayi latti,yayanki zai kaiki,wanne daga cikinsu?Hafiz kuma a kullum shi xai rika kaiki..Abba why?shi ya zabi haka,hmm lai ma yaya Hafiz yayi hakanne don yana tunanin zan soshi,to meye abin yi
tadan yi shiru kadan kafin ta samo amsa...yes hakan zanyi yayi dai dai.
...Tana magana ne a cikin zuciya.
Kome zata yi oho,muje zuwa....


Written by Bilkeesu giro

[11:14PM, 10/1/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

12Tafe suke ba mai magana a cikinsu.

Hafiz ya katse shirun,yadai Mimi shirun fah,ina dan revising ne shi ne kaji shirun yayi yawa...ok yayi Allah ya taimaka,ameen yaya shima murmushi yayi yaci gaba da driving dinsu.

Haka suke kullum basu cika wani surutu ba soboda revising dinda take yi,kuma tayi hakanne domin kar ya takura ta,amma shi abun yana dan damunsa sai dai yabar abun ne a zuciyar batare da ta fahimci hakan ba.

Kamar kullum yau ma zai kai ta school yake tambayar ta.
Mimi meyasa kullum bita kike kamar wacce bata karantu ba
,bayan nasan ba haka kike ba, da kinyi karatu zaki fahimta, basai kin sake ba,amma yanxu kullum sai kinyi bita...uhm ..eh.. am ina so ne in kara fahimta.

Yanayin maganar ta ya gane cewa da gangan take bita kullum,kaddai ace yarinyar nan bata sona shiyasa take min haka..a'a dama haka take bata cika son damuwa ba idan za'a je school,
dayan bangaren zuciyarsa ne ke bashi amsa.

Zee!!..ya akayi,mimi mutumen ki ya fara gano ni...kamar ya ya Mimi? kinsan nace miki kullum revising nake a mota har mu iso,to ya fahimci yi ne kawai nake don kar ya ta kurani,gaya miki yayi?

Written by Bilkeesu giro

[11:19PM, 10/1/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

13A'a yanayin fuskar sa ne ya bani amsa...nikuwa Mimi me zai hana ki fito fili ki fada mashi cewa faruk ke sonki,na tabbata idan yaji zai hakura.

Kinsan bai riga da yace yana sona ba....amma ai duk wanda yaga yanda yake baki kulawa yasan akwai so mai tsanani,gsky ni kaina tausayi yake bani ranar da zai furta min ince a'a,ina jin nauyi sosai a matsayin sa na yayana.

Kinga kawata ga shawara,yaushe ne yaya faruk zai dawo?kesan daga shekara sai shekara yake kawo muna ziyara saboda yanayin aikinsa,inaga yayi wata 7 da kawo muna last ziyara,kenan saura wata biyar kafin yazo....tab amma da saura dai kika ce,kuma kinsan kafin wannan lokaci zai iya furta miki,
abinda nayi tunani ki matsa ma yayanki akan yadawo kina son ganinsa,na tabbata a yanda yake sonki zai dawo..zee kinsan ban cika son matsa mishi ba...kinkuwa san dalilin haka,sai kin fada.

Ba makawa yanayin yadda kuke gudanar da soyayyar ku da yaya faruk, idan Hafiz ya gani zai fahimci Ku masoya ne, na gaske,kwarai kuwa zee shawarar tayi,kinga abu yazo cikin sauki.

Written byBilkeesu giro

[11:20PM, 10/1/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

14 Allah ya biyaki zainab,shiyasa nake sonki...Ameen Mimi.

Kwance take a daki ta na tunanin yadda zata bullowa yayanta faruk ba tare da ta, takura mishi ba....karar wayar ta ya katse mata tunani koda ta duba faruk ne wani sassayyan ajiyar zuciya tayi tare da murmushi kamar yana ganin ta.

Hello yayana,hy my mimi,ya exam, Alhamdulillah,ki na dai karatu sosai ko? eh yaya sosai.

Sai da suka dan taba fira take cewa "yaya ni gsky nayi missing dinka da yawa idan kai bakayi missing dina ba...haba! Mimi Allah nima nayi missing dinki, ai nakusa na dawo...to amma yaya har wata 5 fa,haka ne Mimi yau da gobe cikin ikon Allah sai kiga har lokaci yayi.

Amma kiyi hkr kinji Minima
to yayi yaya Allah ya kaimu lokacin ameen my Mimi shiyasa nake sonki kina saurin fahimta.

Haka suka cigaba da firar su ta masoya kamar ba zasu aje waya ba.

Written by Bilkeesu giro

[11:22PM, 10/1/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

15Mimice da Zainab a karkashin wata bishiya suna jiran azo a dauke su daga makaranta.

Hafiz ne tafe a cikin mota ya iso inda suke yayi fakin,mimice ta tashi tana cewa "yaya sannu da zuwa,yauwa...barka da wuni yauwa sannu zainab.
Yaya faroooook!!!! da gudu ta tafi ta fada jikinsa shima haka rungumeta yayi,yana cewa my Mimi!!!
Sai faman sauke numfashi take tare da janye jikinta.
Yaya da wani yace min ga ka can da sai nayi gardama kafin na juyo,sai Allah yasa nice na fara hango ka,
Mimi kenan wannan gudu haka baki ji ciwo ba dai ko?a'a yayana...ai ko naji ciwo bazai dame ni ba tunda gaka a gabana.....su Hafiz ne da Zainab suka karaso,Hafiz ya mika ma faruk hannu suka gaisa.

Ita ko Zainab sai cewa takeyi ai ke har kin bamu tsoro wlh.....yaya faruk sannu da zuwa yauwa Zainab ya exam mun gode Allah,to Allah ya bada sa'a, ameen.

Hafiz ashe har yanxu mimi bata san ta girma ba...Allah na sani yaya .. to meyasa kikayi gudu haka idan kika jiwa kanki ciwo fa ...ai kaine yaya kamin bazata,tana magana ne a cikin shagwaba, shi ko faruk sai kallonta yake yanayin yanda take shagwabar ta,yana birge shi.

Written by Bilkeesu giro
Share:

1 comment:

  1. pls me yasa ake wuce wasu pages babu 5-10 labarin baya dadi haka.

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive