shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 31 October 2015

AL'AMARIN ZUCI 16--------20

al-a-marin-zuci.jpg

[4:46PM, 10/3/2015] Billygiro: A-AMARIN ZUCINa Bilky giro

16Yaya Hafiz dama kasan yaya ya dawo?a'a nima yanzu na ganshi...Mimi kenan kamar yadda kika ganni bazata shima haka ya ganni.

Amma yaya shine kaki karasowa kayi fakin nesa damu, to ai kin hango ni duk da nesa nake daku....yaya....Mimi yakoyi yanayin yanda tayi magana ne, a shagwabe ,su dukansu sai da abin yabasu dariya,
Mimi sai faman kallon sa take yayi kyau,ya kara haske dagani yana cikin koshin lapiya.

Meye tambayar ki mimina?yaya meya sa kadawo tun lokacin dawo war ka bai yiba?kece Mimi.....ni kuma...daga kansa yayi alamar eh,to ai kace min nayi hakuri,haka ne.

Mimi nakasa jurewa ne, ace kin nemi alfarma ban miki ba,Mimi a duk duniya bani da wani buri sama da inga na faranta miki,Mimi fata na a kullum ki kasansce cikin farin ciki da walwala babu wata damuwa a tattare da ke.
na gode yaya na gode kwarai da kulawar ka a gare ni Allah kuma yasaka ma da Aljannat fiddausi,ameen Mimi Allah yasa mu dukan mu mukasance a cikinta.
su dukansu suka amsa da Ameen.


Written by Bilkeesu giro

[4:54PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMRIN ZUCINa Bilky giro

1l7Bayan sun dawo ne,Mimi tayi wanka tayi kyau sosai kamar ba indiya,sanye take da riga da siket English wear ta yafa wani karamin gyale Kalar kayan,tana saukowa ne zuwa falo,anan ta sami mommy zaune.


Mommy nah,ashe yaya faruk ya fita,to zai zauna ne yayi ta jiranki har sai kinfito,yadai ce ki same shi a dakin sa,to mommy bari naje.


Kwance yake yana sauke gajiyar tafiya daga shi sai singlet da shortniker,bacci yanason ya dan dauke shi.
Sallamar Mimi yaji,Mimi ina zuwa, sai da yasaka jallabiyar sa,sannan ya bude daki, tsaye yayi yana kallonta ba tare da ya bata hanya ta wuce ba.


Kwata,kwata ta canza masa domin wani irin kyau yaga ta kara, sai murmushi take dimple dinta na lutsawa...my Mimi tsokanan ya isa haka,wannan murmushin ai sai in manta hanyar gidanmu...aah yaya,to ai a cikin gidan naku kake,kaga baza ka manta ba.

Yaya, aka ce kace insameka,dama abinci naso kikawo min amma har naci,sai dai barci da nake sonyi,ok yayi bari naje wurin kaka musha fira kenan,ayi barci lafiya,ok bye my Mimi.
Ta tafi shiko yashiga dakinsa.

Written by Bilkeesu giro

[4:54PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

18kakaaaa!!!....gani a bayan ki yau baza ki tsorata ni ba,ai ba tsorata ki zanyiba,nayi ta sallama ne baki amsa ba shine nakira da karfi ko zaki ji.


Kaka ina Alhaji yayi wai, bacci yake,watakilma kin tashe shi da wannan kuwar taki,kaka ai gara ma ya tashi ya ga amaryashi sabon jini,takarasa maganar ne tare da shiga daki.


Alhajina ashe ka tashi da barcin...an wuni lafiya,lafiya Kalau mimi,ina abokin ki,barci yake,koda yake bai jima da shigowa ba.cewar Alhaji.


Shi ne ni kika zo kika tayarnmin da miji amma shi kin barshi yana bacci?eh kaka, shi dan hutu ne....ai kuwa shima yanzu zanje in tashe shi tana magana ne tare da dauko maya finta.

Koda Mimi taga dagaske take ta rirrike kaka tana cewa kaka don Allah yi hakuri Allah ya gaji dayawa,cikin marai rai cewa take magana.
to zaki sake tada min maigida? a'a amma ai kinsan nima matar sa ce,...kamar yadda shima din faruk mijina ne ba,kaka kenan nikadai ce matarsa bana zama da kishiya......

Written. By Bilkeesu giro

[4:54PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro

19Domin tuni na sa yayana ya miki saki ukku....ayya ai ni bana sakuwa....Sallamar Hafiz da Ali ce ta katse musu fira,kuma da alama Hafiz ya ji abinda suke cewa sbd yanayin fuskarsa yanuna.
Kaka ce ta amsa sallamar,bayan sun gaisa ne Mimi ke tambayar Ali, "yaya Ali ina takwarata,ina fatan lafiya kalau take,lafiya lau, tace ma a gaida ke,ina amsawa,shi yaya Hafiz yaki gaya muna wacece antinmu...hmm Mimi kenan kena ke so amma a cikin rashin sani na fada sonki domin dana san faruk ke sonki da bazan fara ba,sai dai saukin abin ban furta miki ba....yaya yadai naga ka zurfafa, tunanin me kake,ba komai Mimi.

Kaka ni zan tafi,to a gaida mutan gida,za suji inshaAllah.

Daddy inaso inje shan ice cream na dade ban je ba,Mimi ni bana iya yawon nan yau ki je faruk ya kaiki...shan zakin ne yata shi ko...mommy pls ki banni inje,ai baxan hana kiba jeki tunda daddyn ki, yace kije...thank u my mom tayi mata kiss a kumatu ta fita a guje.

Da isar ta,ta banki kofar dakin bako sallama.

Written by Bilkeesu giro

[4:55PM, 10/3/2015] Billygiro: AL-AMARIN ZUCINa Bilky giro
20Ya fito daga wanka kenan yaji an banki kofar dakinsa bako sallama,dagowar da zai yi yaga waye, sukayi ido hudu da Mimi.
Da sauri ta dauke idanunnta akansa domin bata saba ganin sa,a haka ba.
Dagashi sai towel ga gashin kirjin sa duk ya kwanta luf ,luf dashi,gabanta sai dukan uku,uku yake domin tasan yau fada ne rabonta.

Wai ke Mimi! yaushe ne zaki yi hankali ki daina gudu!da har zaki shigo min daki ba sallama!bayan kinsan ba abinda na tsana irin a shigo min daki ba sallama,sai kace dakin arna,get out of my room!stupid girl kawai.

Gabaki daya ta rasa natsuwar ta,da kyar ta samu ta iya cewa "yaya am so sorry pleasedajin maganar ta yasan kuka take,nan take yaji bai kyauta ba.

Mimi kuka kikeyi?yi hakuri raina ne ya baci da yawa,gaya min me ke tafe dake, tayi shiru ba amsa,
yaxo dab da ita Mimi magana fa nake miki,am sorry fadamin mekike so, dama....
ta sakeyin shiru hawaye na zuba a idanunta domin ta tsani fada a rayuwar ta har gara ma a daketa da ayima ta fada.

Written by Bilky giro
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive