shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-15 $ 16

rayuwar-fauziya.jpg

15RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (15) Cigaba 15.
Kwarjini da tsananin iya yaudara irin na
Nuraddeen bazasu bari lkc guda ka iya zartar da
'kudurin cin mutunci ga Nuraddeen ba. Cikin
shigar mutunci da kamala yake hannunsa ri'ke
da Amir d'an autanmu yanata faman fara'a,
wanda yasa zuciyata tafara kokwanto akansa,
cikin ladabi yatsuguna yagaida Mama tare da
tambayar yasamemu lfy da km me jiki amir km
ya juya ya fita, aciki ciki ta amsa wanda bama
Nuraddeen ba duk wanda yasan yadda Mama
take gaisawa da Nuraddeen ada yagansu yanzu
yasan akwai wata a'kasa, amma Nuraddeen d'an
duniya gaba d'aya ya'ki nuna fahimtarsa ga
hakan, suna cikin gaisawa aka fara shigo da
kayayyaki kala-kala dangin abinci abinsha da km
tsarabobin khairo da atarihin aurensa da Fa'iza
bai ta6ayin irinsu ba, Mama takai kallonta kan
kayan ta watsar alokaci guda nayaba mata
'kwarai da hakan don nasan bazai wuce
yaudaraba, yayi gyaran murya da alamun jikinsa
yad'anyi sanyi amma ya dake batare da wani ya
fahimci hakanba, yace " Mama Alhmdllh naji duk
abindayafaru amma ina ro'konki da karki zartar
da hukunci cikin fushi, wllh tallahi sharrin
mahassadane dabasa 'kaunar cigabana...
Nuraddeen ban tambayeka abinda kake fad'a ba
kake surutu idan ba kama kai ba 'ba rami meya
kawo maganar rami?' Mama nasan komai munyi
maganar da Fa'iza banda masaniya adukkan
laifukan da ake tuhumata dasu, na yarda kiyi
bincike tun daga cikin gidanmu har khairo idan
kinji tabbaci to na amince zan rabu da Fa'iza har
abada, yana maganar cikin tsananin nutsuwa da
zaka bada hujjar gsky akansa tun baka bincika
ba, naso muzauna da Fa'iza don tattauna wasu
maganganu masu muhimmanci amma ganin
yanayinki na tabbatar bazan samu hakan ba,
Mama koda aurena da Fa'iza ko babu ke Uwace
agareni don kinyimin karamcin da bazan ta6a
mantawa ba, nazo da albishir alkcn da bakin
alqalami ya bushe, amma duk da hk bazan fasa
niyyata ta alkhairi ba, Mama na kammala ginina
komai na zuba aciki idan ALLAH yayi komawar
Fa'iza to komai na tsohon gida mallakinkine ko
tsinke bazamu d'auka ba, idan km bata komaba
hkALLAH yaso dama kayantane, sannan ga
500,000 zakkace na fitar na wnnn shekarar na
mallaka miki ga mabuqatan da kike dasu, wnnn
mukullin Motane na Fa'iza ga tsarabartacan idan
ta samu lfy ALLAH yasa tahaihu sai tayi amfani
da ita tun lkcn dana samu tabbacin samun
cikinta nayi mata alkawari sbd hk babu abinda
zai sa nafasa, ga 100,000 nan km arabawa yara
da wnnn nake neman afuwa agareki data
'ya'yanki zan wuce dukkan abinda aka zartar
ashirye nake da kar6arshi, ni kaina jikina yayi
sanyi ballantana Mama data rasa abin cewa,
kana ganinta kaga jin kunya da tausayi 'karara
afuskarta, nayi 'karfin hali nace "Nuraddeen
katsaya akirawo Fa'izan ku gaisa" ya juyo ya
kalleni idonsa yayi jajawur yace rabu da ita
Fauziyya nasan tayi bacci ya fita abinsa, dama
mu 3 ne afalon ni da shi da Mama, nadawo
nazauna nasha jinin jikina, don nasan tabbas
reshe zai iya juyewa da mujiya, Fauziyya Mama
takira sunana cikin jimantawa, ta kalleni tace
anya kuwa maganarnan gsky ce? Abinfa yabani
tsoro wllh musammanma ayanzu nan
yafawwalawa ALLAH komai, ki duba mutunci da
kamala da dattako irinnasa wllh yabani tausayi
sosai km naji kunya, nima dai Mama natsorata
wllh amma hujjojin zaki duba, kai Fauziyya gsky
maganarnan sharrine banajin akwai 'kamshin
gsky acikinta, ki ajiye maganarnan koda wasa kar
naji kin 'kara kamanta irinta, nace to Mama
insha ALLAHU yanzunma kuskurene da sharrin
shaid'an, haka muka gama zantukanmu muka
tashi, ni km na'kuduri aniyar d'aukar mataki ga
FAROUK don nasan wata'kila yayi hakanne don
yana gaba da shi km maganarsace taqara
'karfafamin gwiwa, har yakeso muma yasa
muraba hanya da shi, amma km ina Mamakin
wnnn al'amari nasan FAROUK farin sani banta6a
kamashi da 'karya komai 'kankantartaba
ballantana magana makamanciyar wnnn, amma
duk da hk saina tuhumi Farouk ba makawa.
16RAYUWAR FAUZIYYA Part (16) Cigaba 16.
Nakira Farouk awaya har gida yau ba 6oye-6oye
nace ya sameni agida yace "to" cikin zumud'i
don bashi da burin da yakai nabashi dama
yagabatar da kansa wajen Mama ni km inaso
yagama kammala komai na aure tukunna sai asa
ranar d'an 'kankanin lkc, yana zuwa yakirani
awaya nasanar da Mama na fita idon Fadila
akaina, nasameshi yafito da darduma amotarsa
ya shimfid'a yana zaune na'karaso muka gaisa,
yace gani na amsa kiran Madam ALLAH yasa
alkhairine nace ameen, Farouk wata magana
nakeso kafad'amin tsakaninka da ALLAH, yace
"ina jinki" maganar da mukayi rannan akan
Nuraddeen, ya kalleni cikin mamaki mezan fad'a
miki akan hakan? Farouk tsakaninka da ALLAH
abinda ka fad'i gsky ne? Fauziyya wnnn wace
irin tambayace? Haka kawai zanzo na'kagi zance
nad'orawa mutum don na birgeki? Wllh danasan
akan maganar wnnn d'an iskan kika kirani bazan
zoba, meye tsakaninki dashi har da zaki dameni
da maganarsa wata qilama saurayin kine bana
'kawarkiba, kawai yami'ke afusace wnnnyasa
nake kallonsa kamar me borin kunya, Assalamu
Alaikum barka da zuwa, muryar Fadila natsinta
tana maganar, yawwa sannunki Fadila ko?
Farouk ya tambaya, au dama kasanni amma ni
ba'a bari nasanka ba? Yace ba laifina bane yana
maganar yana kokarin shiga mota, wai har zaka
wuce da wuri haka? Yace eh dama wani uzurine
yakawoni, inbadamuwa bari nazo ka ajiyeni bakin
titi Mama ta aikeni yace ba matsala shigo,
gabana ya yanke yafad'i ina masifar tsoron
sharrin Fadila, banason yin magana Farouk
yafad'amin marar dad'i Fadila ta samu 'kofa, nai
fuska nanad'e darduma na mi'ka cikin motar tare
da d'aga musu hannu, yaja motarsa afusace yai
gaba, azuciyata nace kai kasani sarkin kishi da
borin kunya, amma fa zuciyata ta cika ma'kil da
taraddadi Fadila ta tafi da Farouk wai meyasa
na6atawa Farouk rai akan abinda bani da
tabbas? Dana ha'kura kawai watarana gsky zatai
halinta to amma hakanma ba laifi bane indai
mutum yana da gsky bazai damuba, ni kad'ai
nake zantukana cikin zuciyata. Saida Fadila
tashafe awa 2 da wani abu kafin ta dawo har
Mama tafara fad'an kota tafi yawontane, ta
shigo tanata faman rangaji da ledodi fal
ahannunta, Mama ta kalleta cikin takaici tace
daga ina kike? tayi murmushi ta kalleni ta watsar
Mama Farouk ne yace narakashi unguwa, waye
Farouk kuma? Mama ta tambayeta wanda yazo
Wajen Fauziyya au kema bakisan shiba? Tana
maganar tana ya mutsa fuska, naji wani kullulun
ba'kin ciki nace 'karya take Mama cewa tayi ke
kika aiketa, eh da nace miki bata aikeni bane
sarkin had'a gurmi? Fadilance ta dawomin da
tambaya cikin gadara, Mama tace ina
sa'konnawa? Tace Mama saida mukaje Country
Mall sannan muka samu gashi, Farouk ne yabiya
kud'in har ya'kara mana wasu kayan, ta
mi'kawa Mama kayan tashige d'aki wai ta gaji,
Mama ta kar6a tana gdy sannan ta zauna tana
tambayata game da komai akansa, tabani goyon
baya amincewa akan naturoshi, naji dad'i kwarai
da farin ciki mara misaltuwa, nashige d'aki
zuciyata cike da farin ciki amma ina tantamar
wane irin surutai Fadila tayi masa,duk da nasan
mawuyacine tasamu fuska awajensa, naso
kiransa awaya amma nad'anja aji zuwa dare.
Bansan meyabiyo bayaba kawai naji ana cewa
wai Fa'iza zata koma gidanta cikin satinnan, aka
gama shirin komai da komai ayanzu gidanmu
gwanin sha'awa, muna ta murna mukaje mukaga
gida ALJANNAR DUNIYA bazan iya kamanta
fasalta muku irin kyan gidannanba, komai
anshigo dashi daga waje "safe contain ne" falo 3
a 'kasa biyu asama kowanne da irin kayan
alatunsa, d'akuna biyu a'kasa a cikin babban
falon suma anshiryasu da gadaje da komai na
gayu, asama kallo ya'kare d'akunansu duk suna
sama har na yarinya mace an shirya mata da
kayan wasa da komai harda toilet komai pink
colour wataqila sunyi scanning sun san abinda
zasu haifa, komai nasu yana ciki tsakar gidane
kawai da d'akin me aiki da me gadi awaje, gida
yayi kyau iya kyau.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive