shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Thursday 22 October 2015

RAYUWAR***FAUZZIYA-4

rayuwar-fauziya.jpg

4RAYUWAR (FAUZIYYA) part (4)
Cigaba 4. Bazan iya misalta muku tashin hankali
da tsananin rud'un da muka tsinci kanmu cikiba.
Bayan anyi kwana arba'in komai ya lafa aka fara
tattara dukiyoyin Abba nagado, kasancewar Abba
yana da 'yan uwa maza da mata bamu kad'aine
magadansa ba, lauyansa yatsaya tsayin daka
akan fito da duk wata kadara da yasan da ita,
tallafin da gwabnati ta bamune kawai ba asashi
agado ba aka bawa Mama sbd hidimar
karatunmu da wasu bukatun, Wllh mama saida
takwashi wasu takardun ta6oye ni kaina na
ankara da hakan, narasa me Abba yake nufi da
takardun daya bani ajiya bansan wazan tunkara
da suba, don kw kansa zai gina, babu irin
tambayar da mama bataiminba akan idan nasan
inda wasu takardun suke nabata sbd idan
yashiga cikin gado baza'a bata abin arzi'ki ba,
kuma za'a barta da wahalarmu batare da kowa
yataimaka mata ba, nace mata banda masaniya
ko kad'an. Bayan tattara komai da lauya yayi ya
kira mama yana tambayarta wasu takardu na
Plaza, dana store da yake ginawa, da wani gida
dayayasiya kwanannan, mama ta gigita don
tasan basa wajenta km manyan kadarori irin
wnnn Abba bazai sakaci da su ba, lauyan yasa
aka kiramu gaba d'aya yaran yana tambayarmu
ko akwai wanda ya gansu? Ni kuwa na amsa da
eh suna wajena... Laah kaji 'yar banzar yarinya
mama ta fad'a tana ri'ke baki cikin mamaki, "ai
dole tana ba'kin cikin nafita kaso mai tsoka dole
ta sacesu Fahad ne yake maganar cikin gadara"
nidai ban tanka musu ba nad'auko takardu na
mi'kawa lauya, inajin Fa'iza tana cewa anya kwa
mama sukenan? Kinsan Fauziyya da munafurcin
tsiya... Sunata maganganunsu ban tankawa
kowa ba. Alhmdllh Lauyan yafad'a yana
kallonmu, yace to dama takardunnan basa cikin
gado kafin Alh. Ya rasu ya shaidamin cewa
mallakin manyan yaransa 3 ne kamar yadda yake
arubuce, sbd hk gasu ayadda suke Plaza ta
Fauziyya store da yake kan ginawa na Fa'iza sai
km gida na Fahad. Babu wanda yai murna kw
ransa a6ace har mama, Fa'izace mai cewa ai da
yabar min duka nari'ke, nidai azuciyata ina
murna tare da gdy ga ALLAH da addu'a
gamahaifina, na kar6i takardu na mi'kawa mama
ta kar6a ta ajiyesu awula'kance, hk dai aka
gama rabon gadon kowa yasamu abinda shari'a
ta tanadar masa, mama ta tattara komai ta ri'ke
ko 'yan uwan Abba maza bata yiwa kara ba
amatsayinsu na waliyyanmu. Saida nayi da na
sanin zuwana duniya ballantana har Abba yaban
takardu na hana Mama, babu irin zagi da cin
mutuncin da mama bataimin ba tare da ALLAH
wadai da MUGUN HALINA!.......


www.abbagana.pun.bz
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive