shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday 26 October 2015

RAYUWAR***FAUZIYYA-10

rayuwar-fauziya.jpg

10RAYUWAR (FAUZIYYA) Part (10) Cigaba 10.
Kwana 4 da Auren Fa'iza Nuraddeen ango
yakoma khairo wai akwai abinda zaiyi yadawo
bazai dadeba. Tunda akayi auren tsahon wata 2
banta6a zuwa gidanba sbd Mama tacemin
batason zirga-zirga sbd karna kashe mata aure
amma fa su suna zuwa musamman da sukaga
mijin baya gari, yadda Fa'izan naga tanamin
waya akan yaushe zanzo yasa nafad'awa Mama
duk ranar da zasu ina neman izinin binsu ta
amince, munje tanata murna da ganinmu
musamman ma ni gsky nayi Mamakin Fa'iza
azuciyata nace dama Fa'iza zata iya nutsuwa
haka? Lallai aure yafi 'karfin komai. Gidanta
yayimin kyau sosai na yaba 'kwarai har santin
nawa yafito fili, mun ci mun sha harda guzuri
muka taho gida. Nura ya shafe kusan wata 3
akhairo kafin yadawo gida, nadad'e ina mamakin
Tuzuru kamar Nura amma aure kwana 4 kabar
amarya, idan yazama dole tafiyar meya hana su
tafi tare? Nasan yana da kud'in dazai iya yiwa
mutum 20 visa lkc d'aya, kuma bayan
dawowarsa zaman gida be dameshi ba kllm yana
waje 11-12amyake dawowa gida tun 8am, idan
yazauna agida to yana tare da abokai inzasu tafi
ya bisu, narasa meye ma'anar hakan gaba d'aya
abin yafara damuna, magana bata 6uya wata
'kawata tashaidamin wai wata 'yar uwar su Nura
taji tana maganar cewa "Yayi mamakin Fa'iza
don ya tabbatar da tayi harka da maza awaje"
abin yad'auremin kai nace ko dalilin da yasa
yake wnnn yawace yawacen kenan, nidai nabar
magana ban fad'eta ga kowa ba nasan wata'kila
sharrine towama zan fad'awa. Babban abin
tashin hankali da mamaki ba afi wata 5 da
Aurenba Fa'iza tayomin wani txt kamar haka:
"Fauziyya kitaimakamin aduniya bani da 'yar uwa
kamarki, ko mama akwai sirrina da zaki sani
bata sani ba, mijina yana mu'amala dani ta inda
ALLAH ya haramta, na amince masa don gudun
6acin ransa wllh yanzu wajen ya kumbura sosai
jini da ruwa yake fitarwa bansan yazanyiba, 'yar
uwa kitaimakamin karki bari kowa yaji hatta
Mama ma wllh ina cikin mawuyacin hali
Nagode."
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive