DAN******ALHAJI-5
DAN ALHAJI 5
muhd-Abba~Gana
tace mutunci ki nake taya ki karewa tace to ummi afwan tace a wuce a kiyaye gaba tashi kije kiyi abinda zakiyi wanka ta fada bangaren safuwan kuma ko yinin wannan ranar tunanin rufaida ne ya zamo masa abincinsa ya kasa sakat!! bacci ma kasawa yayi sai juye juye yake yi.daga ya rufe idonsa sai ya ganta lokacin da iska ta yaye mata hijab shi komai nata burgeshi yake a haka sulainman amininsa yazo ya same shi suka fita ya akayi yau ban ganka a majalisa ba? yace labari ne dani yace to bani na sha yace wallahi wata tsintuwa nayi akan hanya yace tame? yace wata zukekiyar yarinya nayi arba da ita yace wannan ba irin wadan can bace ina ganin ma auranta zanyi yaja da baya yace aure fa kace? yace kwarai kuwa.
muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.