shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 7 October 2015

Wannan labari akwai wa'azi mai tsoratarwa a cikinsa.

kujera.jpg

WANNAN LABARI AKWAI WA'AZI MAI
TSORATARWA ACIKINSA.
Wani mutum ne mai imani da yawan aiyukan
addini, dayake zaune anesa da garinsu domin
kuwa garin mamaye yake da alfasha.
A cikin wannan garin akwai wasu mazaje su 3
‘yan uwan juna da suke kula da kanwarsu wadda
itama babu ruwanta.
Wata rana sai sukayi shawara su dauketa su
kaita can wajen gari inda wancan bawan-Allah
yake zaune kota kubuta daga munanan dabi’un
da suka mamaye garin.
Da farko wannan bawan-Allah yaki yarda don
kuwa yasan hadarin kadaita da budurwar daba
matarsa ba.
Amma sai nan danan shaidan yarada masa
“kaga, kaine mutumin da yafi kowa tsoron Allah a
wannan waje.
Idan kaki karbar wannan yarinya har ta koma
wancan garin, lallai da sannu zata lalace.
Saboda haka sai ya karbe ta.
Da fari yana bar mata abinci a bakin kofar
dakinta yatafi abinsa, sai shaidan yadawo ya
kuma rada masa cewa:
Ta yaya kasan cewa hakika tana samun abincin ?
Zaifi kyau ka rinka dakatawa kadan kana
tabbatar da cewa tana samun abincin ba wata
dabbar bace take cinyewa.
”Saboda haka sai ya rinka tsayawa.
Bayan wani dan lokaci sai shaidan yarada masa
cewa:
“kaga ga yarinya mai hazaka a kulle a gidan nan
kai kuma gaka da irin wannan tarin ilimi.
Ba zaifi ba ace kafara koyar da ita in yaso
zamanta anan baya zama hasara ba gaba
daya?”.
To daga nan fa sai yafara koyar da ita darussa.
Da farko yana barin wani abu a tsakaninsu
saboda gudun fitina, amma sai shaidan ya bashi
shawara a zuci cewa:
Ya kamata yarinka kallon idanunta yayin karatun
domin ya tabbatar da cewa tana koyon karatun,
ba barci kawai take yiba.
Daga nanfa shaidan yasan cewa tarkon nasa ya
danu.
A hankali a hankali harsai da mutumin nan
yayiwa yarinya ciki.
Bayan hakan ya auku sai yadawo ya rada masa
cewa:
”Tofa kaine mafi imani a garinnan.
Yanzu ko mutuncin ka yagama yawo (inhar aka
gano wannan katobara kowa zai gujeka).
Abin da yafi shene ka kasheta ka binne, in yaso
sai kacewa ‘yan uwanta ‘rashin lafiya tayi, kuma
duk da kokarin kana neman magani saida cutar ta
kasheta.
Wannan tabbas zaifi wancan abin kunyar.
Haka kuwa ya yi.
Da ‘yan uwanta sukazo dubata, mutumin harda
hawaye, yana basu labarin yadda cuta ta kamata,
da irin kokarin da yayi na magani har tamutu.
Babu wata jayayya suka yarda, don kuwa kowa
yasan shi mutumin kirkine.
A ranar da daddare duk su ukun sukayi mafarki
cewa:
Wannan mutumin ne yakashe musu ‘yar uwa ya
binne a wani wuri.
Da safe sukayi ta mamaki da ta’ajabi ga yadda
duk su ukun sukayi mafarki iri daya.
Sai sukayi shawara zasuje wannan wuri da suka
gani a mafarki su tone.
Ai kuwa suna tonewa sai sukaga gawar yarinya
har da juna biyu.
Suka kamo wannan mutum suka tafi dashi cikin
gari gaban jama’a.
Mutane suna can suna shawarwarin yadda za’a yi
dashi sai shaidan yazo masa yanemi mutumin da
yayi masa sujjada inyaso shi kuma zai fitar dashi
daga wannan bala’i.
Da mutumin yaga bamafita saiya yarda kuma ya
aikata hakan.
(WA IYAZU BILLAHI ).
Daga nan shaidan yabace yarabu dashi, ya barshi
acikin masifa da halin da nasani.
Dan uwa 'Yar uwa kunji fa irin makircin da Iblis
la'anannen Ubangiji yake kullawa dan adam,
harya halakar dashi.
Ya Allah ka tseratar damu daga kowanne irin
makirci na Shaitan.
Allah ya kubutar damu daga aikata aikin da
nasani.
Allah ya sanya Katangar da bazata taba
rushewaba tsakaninmu dashi.
'Yan uwa ku kasance damu a wannan shafi
akoda yaushe.
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive