shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 1

WAC CE ITA..?? 1

Kiyi sauri ki sauko maigadi ya kusa zuwafa,
Daga saman icen wata siriyiyar yarinya kamar
bulala da qarfi tace mangoro nawa na tsinko?
Daga gefen wata yar lukutar yarinya tace guda 8
ne Amma uku basu nunaba. Yarinyar da take
saman ice tace yauwa.. haka naga ta diro
kaman biri daga saman iccen ni jabo da naje
gano muke WACE CE ITA? saida na firgita mace
haka ba tsoro na kalli bishiyar naga tsawonta
abinda yafi bani mamaki ya akayi ta hau bishiyar
ba tsani.? Kamin in waigo sai kawai na hangota
saman dayan bishiyar har ta Dane bishiyar, ta
fara tsunko gwaiba tana wurgowa qasa
qawayenta suna cabewa, da gani wayannan
yaran taqdiraine waima ya take hawan bishiyar
ba tsani?? Yau sai na kakkaryaku Dan
ubanninku! Matsiyata..!! Muryar wani dan tsoho
naji da alama shine mai gadin wurin Iffatu sauko
baba shehu.!! baba Shehu!! Haka suke fada
suna ihu, Timmm naji Abu siririyar yarinyar ta
fado na tsorata Dan na dauka ta karye Amma
inaaaa tana fadowa qasa ta dauki dayar gwaibar
ta basu daukaba ta filfila har ta wucesu koda ta
iso bakin qofar gonar taga baba Shehu ya kulle
qofa tashin hankali..... Kunsan baba Shehu ya
kulle qofa dole zamu tsallaka ne kamin yazo,
tana fada jikinsu na rawa, ke dijee kulllum ke
kike bamu matsala wallahi bazaki qara biyomuba
gashi ke baki iya gudu sabida shegun duwawun
nan naki. Mtswwww... Kuzo mubi ta chan ginin
yafi gajarta. Suka kwasa a guje suka samu suka
tsallakar da dije da yake ita rukayya irin ippatu
CE ba auki da kanta ta tsallaka duk da haka sai
da iffatu ta taimakamata. Juyowan da ippatu
zatayo ta hango baba shehu da gudunsa ya
kusa kawowa gurinta, ya wurgo mata sandarshi
amma bai sametaba, da yake gurgune sai ta
yanka a guje kamar fanka fil fil da ita, gurin ginin
yafi tsawo dama, na yanda ta iya baba Shehu
zai iya kamata, tana nisa dashi,taja baya sosai
tazo a guje sai kawai ta dane ginin saida ta hau
ta waigo tayiwa baba shehu gwalooo sannan ta
dira a qasa......
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive