shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 2

WACE CE ITA..?? 2 Na Abba gana Tana dirowq dijee rukayya kozo nan ta basu umurni. Sukazo ina mangurona da gwaibata ? Taki ko tamu inji dijee, ta wani harereta itama dijee ta harereta ta jajayen idonta gasu qanana itadai rukayya batace dasu komaiba tayi tsaye dama sune hatsabiban dije da ippatu. Ippatu ta rufe ido cikin tsiwa, abani kayana kamin in lissafa uku. Ta fara lissafi daya biyu uku itadai rukayya ta miqaa mata kayanta dijee ko ta sakasu a Dan kwali ta gulle taci damara da Dan kwalin. Bude idon ippatu ta kwashe dije da mari dama sun saba. Suka fara danbe aka tima dije a qasa dama batada qarfi sai rashin kunya, dagyar rukayya ta rabasu Amma duk manguron da gwaibar sun turmuje a qasa sai guda biyu da gwaiba hudu suka rage. Ko wannen su na fitarda numfashi daddaya. Amma fa dije anji ji jiki kusan kullum sai sunyi dambe da dijee Dan dukansu basuda kunya kuma basuda haqurin juna gashi basu iya rabuwa da juna.! Gamon jini da hali ita rukayya batada fada biye take dasu kamar raqumi da akala duk yanda akayi da ita chan takeyi. Ippatu ta baiwa rukayya mangoro daya gwaiba daya ta riqe mangoro daya gwaiba uku kaji adalci irin na ippatu dije kuwa tahau tsini Dan bata bata komaiba. Ta daure fuska muninta ya qara fitowa, Sunkama hanya ana gaba da juna kowacce tabi hanyarta ippatu na tafe tana shan magoro da gwaibarta, Bala'eeeee wallahi ga bello mai kifi chan, inji rukayya, Habawa baima hangosuba Amma tuni sun yanki ticket suka fara gudu ba tsayawa basu tsayaba saida suka daina hangoshi suka fara dariya. Kamar basune sukayi danbeba har sun shirya. Ippatu tana dariya tace dijee kin tuna faduwar da bello mai kifi yayi suka qara kwashewa da dariya suka tafa ai ranar saida ya bani tausayi habadai, wallahi baibani tausayiba kifinsa bala'en tsada sai shegen dadi inji dijee, Dan yaga ana saye yake yiwa mutane yanga. Shegiyarda sukamai saida ya qare suyar kifi ya jera akan tire zaije talla kawai sukayo tsokana aka biyosu suka zo a guje suka barar mai da kifi kuma sukabi takai suka wuce ko waigowa basuyiba shiko bello mai kifi dan jaraba maimakon ya tsaya kwashe Dan kifinsa sai kawai ya biyosu a guje, garin binsu ya fadi a qasa ya huge bakinsa, sukam tuni suka bace mai ko mai lafiya baya iya kamasu idan suna gudu bare bello mai kifi daya tsufa. Dan ko dijee bai mangalar duwawu idan ta saki qafa ba dama bare rukayya mai kamar bulala, Nidai Jabo bantaba ganin gyauyawa kuma Yan iskan yara, marasa kunya ga tsokana da rashin tsoro irin wayannan yaranba dije da ippatu ba, Dan ita rukayya yar kallo ce sai zugasu da takeyi idan sun samo su sammata ko ta musu gadi suyi abinda zasuyi. Suna dariya suna tafawa abinsu har suka iso gida sai lokacin ippatu ta tuna da aikenta akayi sayen daddawa da manja, ko shakka babu ta xubar da kudin, ta kwance Dan kwalinta data daure kudin amma ina tuni sun fadi, zakuwa tashi qaniyarta idan ta koma ba daddawar nan da manja ga uban shiririritan da tayi.. Maimakon ta shiga gida sai kawai ta kama hanya tana tafe tana tunanin yanda zatayi da saqon googo, kicibis taci karo da wasu yara suna fada ta tsaya kallo suma aikensu akayi sai taga sun yarda kidi naira ashirin da biyar ta dauke ta qulle a habar zaninta. Yau wace rana ippatu taga fada bata tsaya sayen fadanba da walakin. Taje ta siyo manjanta na goma daddawan biyar ta siyo kan kifi na biyar tana tafe tanaci har taje ta dawo suna fada fadan yanzu kuma na an sace kudin dayane ta kyalkyale da dariya iron ta mugunta ta wuce abinta.....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive