shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA?3

WACE CE ITA..?? 3 Na Abba gana Ta wuce abinta koda taje gida ta rasa yanda zatayi ta shiga Gidan ta fara labe labe. Ubanme kikeyi anan ??muryar babanta taji ya mata tsawa saida hanjin cikinta suka juya duk duniya babanta kawai take tsoro ta fara kame kame, bakomai baba sannu da zuwa. To wuce gida munafukar banza ya tasa qeyarta suka shiga. Malam ina ka tsintomin ippatu? wallahi tun qarfe biyu na aiketa Dan nasan halinta batadawoba sai yanxu, kaga har na qare tuwo! Dan ubanki ina kikaje? Ta fashe da kuka wallahi baba sai bayan la'asar ta aikeni ko minti uku banyiba na dawo. LA ilaha illallahu Muhammadu rasulillahi... Ihhatu "haka take kiranta Dan bata iya sunan ba" kina nufin qarya zan miki? Kinma saba bani kayana ta qwace manjanta da daddawarta, baba ya juyo ya kalleta ina kika samu kifi sai qarnin kifi kikeyi. Ta fuske kamar gaske gidan su kulu mai daddawa suka sammini.! Na dauka kin qara tsokano bello mai kifine. Aah wallahi baba.!! Idan ta tashi zama ta Allah sai ki rantse da Allah ba ita bace take taqdiranci a hanyaba kamar wata waliyiya har ma dai gaban babanta..... ******************* Ippatu yarinyace yar kimanin shekara 11 duk yanda zan muku bayanin ta idan dai ba ta muku taqdiranci nata kungani da idonkuba ba zaku gane WACE CE ITA ba, Sabida batada kunya, batada tsoro ba tada ladabi ba tada mantuwa ba yafiya haka take wata hargitsatsiyar yarinya da ita. Gata qazama taqin qarawa, batasan tsabtaba ko kadan haka batasan wankaba bare wanki farace Amma yanxu tafi zainb khalifa baqi, haqoranta Dan rashin wankewa har sunyi tsatsa daga sama, daga qasa kuwa kamar an kwaba laka an shafa mata idonta kuwa gasu Manya Manya Amma sunyi jaa kamar na sister khade qafar nan kuwa duk tayi wani iri Allah ne ya tsareta qafar bata Faso da tuni ta farfashe Dan su dijee tuni qafafunsu sun yayyage da Faso, bata yawo da takalmi, a cewarta takalmi basa barinta gudu. Mahaifiyarta sun rabu da mahaifinta tun tanada shekara 6 tanada yayye guda biyu maza duk mamansu daya, suna gurin mamansu, itama babansu yaje gun mamar ne akan dai ta bashi yayanshi, ta hana, dazai dawo ippatu ta maqalemasa ya dauketa ba da son ran mamarba, tana zaune gun kishiyar mamanta gwagwo rabi, gwagwo batason ippatu ko kadan ita kuwa ippatu ba abinda ya dameta harkar gabanta take bata damu da asotaba kuma gwagwo rabi duk abinda zata mata saita rama cox bata mantuwa bata yafiya.! Shiyasa hankalinta kwance bata tsoron kowa duk qauyensu sai babanta kuma bata ragawa kowa duk qauyen nan. An sakata makarantar boko har uku ana korota sabida uban yara da takeci, a makarantar allo ma Dan yana maqocinsune da tini ya korota ippatu kenan....
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive