shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 4

WACE CE ITA..?? 4
Na abba gana
**********
Ta dauki allo na tafi makaranta, gwaggo ko
kallonta batayiba Dan tasan ba makaranta
zatajeba wacce batason makaranta zata fita tun
qarfe biyu, za'a gurin jarabadai, allonta har
rubutun ya goge dan tsabar rashin zuwa
makaranta da takeyi tana fita taje bayan qyaure
ta boye allon ta sa mai bata tsayaba sai gidan
su dijee da yake dijee da rukayya gida daya suke
dagyar suka samu suka sulalo suka fito. Suna
tafe suna tadi duk yaran garin har Manya
tsoronsu suke dan basu bar kowaba, idan
babbane ya daki daya taron dangi sukemai ko
suyita jifarsa da duwatsu, basu tsaya ko inaba
sai rafi suna zuwa suka tube dagasu sai qajeren
wando rukayya dai ta fara girgar dangi dija ma
ya kunmo kai Amma basu kunyar kowa suka
fada ruwa sukayi iyo sosai kaman kifaye sun iya
ruwa kaman me suna ruwa suka hango baba
shehu mai gadi shima ya hangosu sunsan kamin
su fito ya iso sai dijee tace kar mu gudu idan
yashigo kamamu mu bashi ruwa mu danneshi a
ruwa.! Sun haqamai gadan zare, Baba shehu
dayazo sai yaqi shiga kaman yasan abinda suka
fada, ya kame guri daya kamar bai gansuba,
sukayi jira har suka gaji Amma yaqi tafiya sai
kawai suka yi shawara akan su nutse su tafi
chan nesa dashi su fito. Suka nutse a ruwa,
baka ganin tafiyarsu, saida sukayi tafiya mai
nisa sannan suka fito suka lallabo suka zagayo
suka saka tufafin su suka nufi gona satar
mangoro shiko baba shehu yanachan yana jiran
fitowarsu daga nutsewar da sukayi yaji shiru sai
abin ya bashi tsoro kardai ya kashe yayan
mutane!!! Tuni ya fada ruwan ya shiga lalube
Amma basu ba labarin su chan ya hangosu suna
gudu sun ciko zaninsu da mangoro da gwaiba
yau hadda lemu da basu cika diva ba sun debo.
Tsoro ya kama baba maigadi daganan baba
shehu mai gadi ya sallama cewa ba mutane
bane aljanun dajine ko Yan ruwa suke
addabarshi, dole ya nemo tsari karsu hallakashi.
Da sauri ya fito ruwan saida sukaxo Dan kusa
dashi suka kwashe da dariya sannan suka mai
gwalo suka gudu. Kaji hatsabibai....
***
Tun daga ranar baba maigadi bai qara binsuba,
hasali ko kallonsu baiyayi idan suna abinsu, da
suka gane ya saka musu Idone sai suka maida
abin Sana'a kullum zasuje su debo sai suje su
wanke suje talla da sukaga basa ciniki sabida
baqin halinsu sai suka riqa daurawa rukayya
tallar rukayya kuwa akwai farin jinin talla, talla
ta karbeta nan danan suke saidawa gurin rabon
kudi suyita bala'e da danbe. Ba ranar da basa
fada kuma aranar suke shiryawa,.....mu hadu a kashi na gaba
by
abba gana
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive