shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 5

CHI GABA.... WACE CE ITA..?? 5 Na Abba gana ****************** Yauma kamar kullum yan matan uku dije ippatu da rukayya suna tafe suna labari suna shewa da dariya da gani dai kasan basu da kamun kai bare uwa uba tarbiya, laaaaaaaa dije kalli malan garba da ya dakemu ranar.! suka waiga gaba dayansu suka kalleshi, ippatu tayi tsaki share shi mugun banza, dijee ta kalli ippatu bazamu share shi ba,yakamata mu rama, mi zamu masa mu rama kalli fa har yanxu tabon bulalanshi, ta nuna hannunta, kawai mu ramako ? Eh mu rama, Suka fara shawara sharrin da zasuyiwa Dan saurayin malamin makarantar allonsu, yayo wankansa na juma'a zashi masallaci sallar juma'a baima kula dasuba. har sun hada sharrin da zasuyi tunda nanne hanyar sa kamin ya dawo daga masallaci, sun nemi toka ta murhu sukaje Gidan da ake daka taba gari irin wannan da tsofafi suke sakawa a qasan lebonsu, suka siyo ta ashirin suka siyo garin barkono na goma suka hada guri daya suka ijiye suka samo bokoti daya suka debo ruwan kwata mai shegen wari suka je suka samo kashin shahu sabo suka kwaba da kwatar nan suka labe gefen hanya, ippatu ta dane bishiya kamar biranya, da bokitin kwatar ta da suka dama da ruwan kashi, malam garba na bullowa shida dije ta watso mai garin tokar daidai fuskarshi, da suka yiwa hadi ita, ita kuma ippatu ta watsomai ruwan kwatar daga saman bishiya, daga kansa har qasa ta diro gasa suka waske, idon malami sun cika da yaji ya sai ihu yake yana Neman dauki,yana murxawa ga ruwan wari a saman kanshi kamin mutane suji ihunsa tuni sun gudu gidajensu. Kuma ba Wanda ya gansu Amma sabida hatsabibancinsu duk Wanda ya sami labari sai yace hatman aikinsu ne sun koma gida duk ranar ba Wanda ya fita cikinsu, wayanda tun safe idan sun fita gantali basa dawowa sai guraren yamma shima Dan sunsan idan sunyi dare akwai samarin da zasu hallakasune shiyasa duk la'anarsu da dibar albarkarsu basa fita gida da dare. Ina ippatu? tana daki, Malam lafiya kashigo a hargitse?? Inafa lafiya yarinya tana son tasa xaman qauye nan ya gagareni.. Ke ippatu.!! Na'am baba, zonan mara kunya yarinya, ku ne kuka jiqe Malam garba da ruwan kwata kuma kuka zuba masa barkono a Ido ko?? LA ilaha illallahu Muhammad rasullullahi wallahi tana taba hannu tana salati kaman gaske, wallahi baba ka tambayi gwagwo yau duk ban fita koda zaureba, Dan banida lafiya, ko goggo,?? to ubanwa zai masa wannan ta'addancin idan bakuba gashichan ido sai Allah, kuma yace bazai barwa Allah ba. Salamu alaikum. Daga waje sukaji sallama koda baba ya fito saiga yan sanda biyu an kamo dije da rukayya akazo a tafi dani, ina kuka ina kiran baba, amma saida yan sanda suka tafi damu police station.. ********** Kun Dade kuna addabar mutane a garinnan, ba makhluqin da bai kawo qararkuba a qauyennan, kun zama annoba jaraba a gari to zamu kulleku har sai likita ya tabbatar mana da samun idon malam garba, DPO yake wannan bayani wasu ippatu, iyayensu sunyi sunyi abasu belin su amma sunqi badasu aka kullesu suna kuka suna basu bane! DPO yasa an musu Dan karen duka tunda ba wata sheida da take tabbatar da cewa su suka aikata wannan laifin, kawai sanin hali yasa aka tsaresu, sunji wuya matuqa, amma dukda haka sunqi fada gaskiyane, rukayya ta gaji ta tona asiri tace sune dije da ippatu duk wahalar da suka sha sun qi aminta hasalima sun qaryata rukayya ne, Dpo dayaga ba nasara kuma likita yace malam garba ya samu sauqin idon sai aka sakesu, aka musu kashedi mai tsanani, sunyi wujiga wujiga dasu, tun suna police station suka fara shirya sharrin da zasu yiwa dpo insun fito kaji hatsabibai dpo ne next target dinsu.......
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive