shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 6

WACE CE ITA..??6 Na abba gana ******* Bayan sun fito da sati biyu sundan yi lafiya dan iyayensu sun manna musu mari a qafafu basa zuwa ko ina hatta makarantar allo, gari ya samu lafiya two days, bayan sati biyu kamar sun shiryu sun zama na kirki, aka kwance musu marinda aka saka musu, ranar da suka hadu da juna suka fara dariya suna bada labarin yanda iyayensu suka musu, bayan sun qare labari suka fara shirrin yanda zasu yiwa Dpo su dau fansar dukanda yasa aka musu da marinda ya riqa tsinka musu lokacin, bayan iyayen su ba Wanda ya taba marinsu saishi.!! Sun shirya zuwa har gidanshi su fasa mai glss din akwalar motarsa. Amma basusan yanda zasuyiba, sun gargadi rukayya akan idan ta kuskura ta qara tona musu asiri basu ba ita ta amince, matsalar su daya kada a ganesu, sun yanke shawarar fita da dare Amma suna tsoron samarin garin. Yauwaaaaaa ina yan matannan da muke tsokana masu saka baqiin Abu da hijabi su kulle fuskarsu?? Eh nagane inji dijee naji ana ce musu wani Abu namanta sunan, yauwa mu samo irin wannan abin da suke sakawa mu rufe fuskar mu sai a dauka sune zasu makaranta sai muje mu fashe mu dawo, kaji hatsabibai marasa tsoro.!! Suka saka dariya sun sami wani tuggu da zasu qulla, Matsalar su daya basu da niqab din nan dijee akwai gyallen tatan gasara na Maman su zata dauko sai su yagashi suyi niqab tunda gyallen baqine haka kuwa akayi, suka tare yar makaranta ita ta dauka dukanta zasuyi, sai taga kawai sun karbi niqab dinta suna kalloyanda yake, suka sa allura suka hada irinsa, kaji shegun yara... da dare suka fita sai unguwar su dpo suka shiga har chikin gidansa batareda shakkun komaiba, da qarafunansu da suka samo gun kanikawa, suka ma glss din motar tamas tamas, da yake dpo yana gurin aiki, matarshi tana islamiyya yarane kawai suke Gidan wataqil suna bacci sukayi operation din ranar har suka gudu ba Wanda ya gansu,har suka iso gida!! Labari ya chika qari, ya yadu a kowa yace da dai da rana ne da sai muce su ihhatu da dijee ne, Amma yanzu duk qauyen an yarda basu bane barayine kawai suka masa wannan karen aikin... uku bala'e kenan!! suna nasara aduk aikinda sukasa gaba koda zasusha wahalane.. ***************** Yauda gobe ba wuya a gurin Allah abubuwa da yawa sun faru a dan qaramin qauyen nan ciki kuwa harda rasuwar mahaifin ippatu sanadiyar hatsarin mota, yajee birni siyo kayan shagonsa anan babbar mota ta bi saman motar su Allah yayi mai cikawa.! Su ippatu an Dan natsu kadan an rasa mahaifi, mahaifiya kuma dama batasan duniyar da takeba coz ba rabuwar allah sukayi da babantaba duk sharrin goggone, tunda tayi wayo bayan babanta ya kwatota a hannun mahaifiyarta bata qara saka mahaifiyarta a idoba haka ma yayyenta.. Tun farko farko zaman haquri goggo takeyi da ippatu, bare yanxu da ba mahaifin ippatu, sabida haka ta yanke shawarar miqata birni wanke wanke ko ta moreta....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive