shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 18 July 2015

WACE CE ITA? 7

WACE CE ITA..?? 7 Na abba gana Tashin hankali ni kaina Jabo na tausaya wayanda zasu dauki ippatu aiki gidansu kamin su korota nasan zataci ubansu.! Goggo kullum gori take mata har ta fara girgar dangi a gida, amma ba mashinshini bare a aurar da ita. Wazai kwasar ma kanshi jaraba. ippatu da yar birni ce da sai anyi haddadiyar mace dan komai Allah ya bata sak mamanta ta dauko fulani gaba da baya sai ta hada da da duhun babanta sai tayi Dan duhu farinta mai haske ne da duhu gata qirar kalangu ga gashinan kamar yakasheta amma ba gyara idan akayi kitson sallah qarama sai babbar sallah ake tsefeshi, tayi baqi Dan na tabbatar da tafi zainb khalifa baqi sabida tsabar rashin wanka, qafafu duk sun jeme haqora sunyi tsatsa da wata laka laka a ciki idonnan sunyi ja duk jikinta tabone sabida fadowa saman bishiya da akeyi a jijji ciwo, ko saman Garu da ake dirowa ko a na gudu a fadi a ji ciwo haka dai take masha Allah..... ******* Goggo tayi magana da altine akan tanason a kai ippatu birni aiki amma inaaaaaa altine taqi aminta Dan tasan halin ippatu sama da qasa, gaba da baya, altine taqi yarda har goggo ta gaji da zuwa gidanta neman alfarma ta haqura, ranar goggo taje suna maqotansu taga wata mata daga birni tana maganar a nemo mata yar aiki yarinya qarama mai qoqari da kuzari goggo batace komaiba, Dan tasan idan ma tayi magana anan mutane zasu fadi mugun halin ippatu. Saida aka watse matar na fita goggo ta faki ido ta bi bayanta, tajata gida tace tanada ya amma batason kowa yasan zata kaita aikine zatace takaita gun yar uwartane goggo tace yarinyar marainiyace, tanason ta dan riqa samun abinda zasu chi su rufawa kansu asiri, Amma batason kowa ya sani, hakadai goggo yayita tsara matar, ana haka saiga ippatu an dawo daga kogi tun safe dataje sai yanxu tayi shudi daya, Koda matar taga ippatu taga uban bokitin data dauko saman kanta chike da ruwa ta tabbatar da cewa ippatu Nada kuzari, kamar gaske ippatu ta gaida matar ta wuce abinta matar kuwa ta amince da ganin ippatu kuma tace baxata fadawa kowaba. Matar da yake gidan biki tayi sanarwar anata kawo mata yara yan mata amma Duk wacce aka aiko sai tace musu ai ta samu bata fadawa kowa cewa ippatu CE ta samuba har ta koma birni,.!! Bayan kusa sati uku da magana matar tazo ta tafi da ippatu birni ta mata dinki kala biyu Dan kar taje Gidan daga shigarta a koresu , aka hada da yan kayan sallarta. Ippatu tayi kukan rabuwa da qauyensu Dan batason zuwa aikin da za'akaita sun rabu da dijee da rukayya sunata kuka sai birni......
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive