shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 8

WACE CE ITA..?? 8
Na muhd abba Gana
*****************
Bayan sun isa birni matar da nikaina Jabo
bansan sunantaba takaita gidanta, tasa tayi
wanka ta saka kayan da ta dinka mata, suka
kwashi hanya takaita gidan da zatayi aiki, ippatu
tunda ta shigo birnin sokoto take qauyanci ganin
sabuwar duniya ya hanata kula da fadan da
matar take mata bare ta mata rashin kunya,
data shigo gidan Alhaji Habib nan kallo ya koma
sama, gidane da idan na tsaya muku bayaninsa
zan bata lokacine, duk unguwar ba gidan da
yakaishi girma, ga lambu a gidan shuke shuke
manyan itatuwa swimming pool ne, gurin ijiye
motoci ga abubuwa nan kala kala, ataqaice dai
Gidan dai ya hadu, ippatu tana shiga palon
santsin tayis ya kwasheta ta xube qasa tiiiiim..!!
Wata Yar budurwa da matar gidan suka saka
dariya, taji haushin dariyar da aka mata ta daure
fuska abinta, badan yau tazoba da sai ta tsula
musu rashin mutunci su har sun isa su mata
dariya.!!?
Matar data kawota ta riqa hannunta suka
qarasa palon suka zauna, sanyin ac tuni ya fara
shigarta ta fara rawar dari sai qarar haqoranta
kikeji kakaf. kakaf, alhaji yace a kashe ac din
baquwarsu tanajin sanyi.! haba Abba wallahi
zafi akeyifa wani Dan saurayi ya fada yana
yatsina fuska alamar zafi! Alhajin dakanshi
yatashi ya kashe ac ya dawo ya xauna. Wacce
ta kawoni ta fara musu bayanina kamar yanda
goggo ta mata bayani, taji qaryarda goggo ta
zuba tayi yawa ta kasa haquri Dan ita ba'aqarya
gabanta, tayi charb ta chabke ta fara zuba,
goggo ba itace mahaifiyataba mahaifiyata sun
rabu da mahaifina tun ina qarama mahaifina ya
rasu shekara kusan biyu da suka wuce kum.....
Keeee, keep quiet mana ya fada yana mata
kallon wulaqanci, chikin tsawa ya fadi maganar
ta gane keep quiet dan lokacinda tana boko
kamin a korota Malaminsu yana yawan fadar
haka idan ana surutu kuma daya fada sai kowa
yayi shiru, shima malaminsu da qarfi yake fada
kamar yanda wannan ya fada, ta dallamai
harara hadi da yimai kallon banxa ta zubar.
Kaiiiii abba u see? Kaga yanda take kallona
kuwa,?
Farhaan yakamata ka riqa haquri mana, da
zuwan baquwa zaka tsaneta haka, kada ka
manta da ita zaka zauna.. farhaan ya juyar da
kai gefe gaskiya dady bana tunanin xan iya
zama da wannan, kalletafa!! wata kyakyawar
dattijuwa ta kalleshi wallahi kayi kadan wannan
itace ta qarshe ba chanji. Duk maganar. da
suke da englsh suke yinta, Ya bata fuska ya
tashi yabar musu guri yar qanwarshima ta bi
bayanshi suna gunagunai da turanci,
Matar data kawoni ta basu haquri tace kuma
kada in qara magana, ganin maganata kamar
itace ta haifarda rigima sai nayi shiru bawai dan
raina yasoba, taci gaba da musu bayani inajin
tana qarya amma ba halin magana......
Mujeee zuwa muji yanda iffat za'azauna a gidan
aiki, da wannan hali nata...
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive