shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 18 July 2015

WACE CE ITA? 9

.: WAYE ITA..?? 9
Na abba gana
Wacce ta kawoni Ta qare bayananta na qarya
dana gaskiya da goggo ta kitsa mata....
Kyakyawar matar tace Allah ya bamu ikon riqeta
yar marainiya da ita, dama yaron mune muka
nemowa mai aiki, duk wacce aka kawo sai su
sami sabani dashi kusan mai aiki 13 ana
kawowa suna samun sabani, shine yanxu yace
asamo mai qaramar yarinya tunda aikin nashi
bashida yawa yace bayason Yar cikin qari sabida
sauran daga qazamai sai barayi sai yan iska sai
marasa kunya da sauransu, shi kuma baya iya
zama dasu amma wannan yarinyar ni tamini
sosai, ammafa sai ta zama mai haquri Dan
farhaan akwai fadin rai da fushin bala'e sai kina
haquri kinji yan mata? Ta amsa da to kamar da
gaske, ya sunanki da sauri nace ippatu. Matar ta
maimaita iffaah suna mai dadi! Sai naji tafi kowa
iya sunana yanda ta fada ta wani juya baki,
"kunsan bahaushe baya banbanta "P""F" duk
daya yake kiransu" Maman farhan ta mini nasiha
ta kira yarta farahnax amma shiru bataxob,
dakanta tace muje in nuna mini dakinki da zaki
zauna, tashin hankali koni Jabo dakin ya burgeni
bare wata yar qauye irin iffaaah...
An gaya mata aikin da zatanayi, zata gyaramai
dakinsa tattara mai kaya takai ma mai wanki ya
wanke, ta wanke bayi, ita zata riqa tashinsa da
safe yaje skull. Hummm iffaat kam sarkin bacci
wa zata iya tayarwa daga bacci, Naji matar
gidan ta burgeni cox batada gyama kuma ba
wulaqanci haka mai gidan amma su hatsabiban
yayan yan wulaqanci ne tasan ma korarta zaiyi
Dan bazai iya zama da itaba.
******
Kwanan hajiya Fati hudu da iffaaat anyi sa'a ba
wanda ya tsokaneta bare ta rama, yau zasu bar
naija su koma UK da yarsu farahnax, akabar
farhan da iffaaat a gidan. Da gani jininsu ko
kadan bai haduba amma ba yanda ya iya
mamarshi harda rantsuwa akan cewa bazai
chanza taba, dole yayi haquri koda na shekara
dayane, ya fahimchi yarinyar batada kunya dole
ya saitata.!!
Bayan tafiyar su hajiya ya dawo daga rakiyansu
da yayi a airport ya shigo gidan,
Keeee come here, taxo gabanshi tamai qiqam
kamar ice ta tsaya, Oyaaaa get seat tazauna
bawai ta gane mi ya fada bane kawai a
makarantar boko kamin a korota taji maliminsu
na cewa seat down ta gane cewa acikin biyun
daya na nufin zamame tunda yana fada kowa
yake xaunawa, haka yana cewa come here sai
taga anje gun malami. sai itama tayi hakan,
akayi Sa'a ta gane farhaan ya dauka tanajin
English ganin ya mata Dan biyu ta gane sai ya
fara bayani Hausa da turanci saida yayi yayi
yace have u get me.? Yaga ko motsi batayiba,
ya qara tambaya shiru kakeji yagane aikin banxa
yayi, keee ya daka mata tsawa. Kina jina?? eh
inaji. to mi nace?? Ta harareshi mi kace kuwa?
Duk maganar da nayi bakiji abinda naceba. Ta
tabe baki ai ban dauka dani kakeba to da uban
wa nake, zanci ubanki fa.! ta miqe zunbur ta
nunashi da yatsa kada ka qara zagar min baba
sabida ya rasu idan ka qara zagin babana zan
rama masa kaji na fada maka. Ta murguda baki
ta maka mai harara... Farhaan kam gaskiya
tamai yawa ya tsaya yana kallon baqauya tazo
tanamai rashin kunya har gida wai kuma Yar
aikinsa, anya kuwa tasan WACE CE ITA anan
gidan? ba shakka batasan WACE CE ITA ba nine
xan Sanar da ita WACE CE ITA a gidannan, baice
mata komaiba yaci gaba da kallonsa.....
Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive