shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 10

WAYE ITA..?? 10
Na Abba gana
Ta kalleshi in tafi?? Yayi banza da ita, ta qara
tambayar sa yayi mata banxa, ta kama hanya
zata tafi ya daka mata tsawa, ki dawo ki tsaya
nan, taja ta tsaya kusan 30mnt tana tsaye, ta
gaji zata zauna ya hanata Idan kika zauna sai
na kakkaryaki, tayi tsaki, ta kauda kai, ya qare
abinda yakeyi ina miki magana zakice baki dauka
dake nakeba ko?? To waye a dakin da zanyi
magana dashi? Ta kalleshi a wulaqance da chan
dakake maganar dawa kakeyi?? sau nawa ina
ganinka kana daura hannu a kunne kanata
magana ko kuma kayi yare kana dariya, wani
lokaci ai wata waya kake sakawa a kunnenka
kayita magana kai kadai duk da uban wa kake
magana?
Kaga yanzuma na dauka da ubanda kake
magana farko dashi kakeyi yanxu .
Zunbur ya miqe yayi niyyar mammaketa sai ya
tuna da abinda ummanshi ta fada mai "ban
amince ka daki yar mutaneba marainiyace duk
abin da ta maka kamin waya zan mata magana"
sai ya koma ya zauna ya dun qule hannu itako
tana tsaye ta riqe kunkuminta kamar mai jiran
danbe, ya kalleta wata mummuna qazama da
ita, ya rasa abinda zai fada mata ta gane WACE
CE ITA. ya harareta yaja dogon tsaki, to ki
zauna, ta zauna ya maimata bayanin da ya mata
da dazu, shima dai iskancine yazai ijiye baqauya
kamar wannan yana mata English to amma ai da
yayi na farko ta gane, ya akayi ta gane? Koma
yane ya rage nata..
Yace Inada abokai mata da maxa, kuma ko
wanne yana zuwa nan gidan suna kwana wasu
suna wata daya wasu suna sati biyu idan sunzo
suma duk abinda kike min suma zaki musu
hadda girki idan suna buqata zaki musu. Ni ban
iya girkibafa Malam.! Gidanku basu koya miki
girkiba ? Eh basu koyamin ba, ta fada cike da
tsiwa,sai yayi banxa da ita ya fahimci yarinta na
damunta amma zai gyarata a hankali, ya nuna
mata WACE CE ITA a gidannan, OK ya rage naki,
haka zaki girka musu in sun buqata, tayi banza
dashi Dan tunda take bata taba yiwa goggo
girkiba cox batama zauna gidaba bare tasan
yanda ake girka abinci. Ko girkin murhu bata
iyaba bare na gas, ya qara jaddada mata abinda
umma tace bata ba fita waje, ba wasa da masu
gadi, ba ruwanta da kowa aikinta kawai. za'ayi
shegiya kuwa.!
Yaqare fada mata abinda zai fada mata ta tashi
ta shige dakinta.
Tunda tazo gidan a Leda take kashi sai ta saka
bola idan yayi yawa ta fitar dashi sabida duk
dube dubenta bataga masai a gidan ba, shi yasa
dakinta yake wari Dan bata damu da gyara
komaiba, gurinda kawai akace ta gyara dakin
farhaan take gyarawa....
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive