shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 11

.: WACE CE ITA..?? 11

******by abba gana
Ranar farko da farhaan yayi baqo wani abokinsa
da sukayi karatu a UK. Tare sunyi missing din
juna, farhaan yanata addu'a kada wannan
kucakar ta fito ta kwafsa mishi Dan ya lura
kanta rawa yakeyi ba kadanba, suna tsaka da
gaisawa sai gata ta fito. Kamar an korota daga
daki, Ku tashi zan goge nan gurin! Ta fada ba
tareda ta kallesuba, Tafara share palon, meene
kebakiga inada baqo bane,? maza ki bacemin da
gani har ta fara shara tajiyo tsawan da ya daka
mata ta miqe tsaye, tana yatsina fuska kai
bakasan lokacin aiki na bane da zaka kwaso
tarkacen abokanka kazo dasu Ku hanani aiki..!
Habawa Ya wanke ta da mari tashin hankali..!
ta dauki bokitinta na ruwan dattin data goge
sauran guraren dasu, ta watsawa abokinsaA
fuska, tunda shine silar adaketa, ta matsa daga
nesa tana jiran hukuncin da za'amata da Wanda
itama zatayi Dan bata yafiya, dukansu sun rasa
abinyi abokinsa ya fara bala'e ya zaka zauna da
mahaukaciya farhaaah, bakasan hadarin
hakabane? Wannan wata rana zata iya kasheka
wallahi, tana shigowa palon nagane batada
hankali, Kaine Mara hankali baniba tana zazzare
ido kamar lecturer ya titsiye jabo a clss bata iya
karatuba, farhaan zaije gunta abokinsa yariqe
hannunsa, cool down my man. Akwai banbanci
tsakanin mai hankali da mahaukaci nasan da
tanada hankali bazata taba yimin hakaba, muje
daga ciki inyi wanka in chanja kaya kawai.
Baqin ciki ya hana farhaan magana ya rasa
yanda zaiyi, Dole ya nuna mata WACE CE ITA a
gidannan. Abokinsa yaja hannunsa suka wuce
daki ita kuwa hajiyar tachi gaba da aikinta.
((Allah ya tsaremu da aikin jahili da baqauye.))
ta gyara gunda ta jiqe da ruwa kamar bata
zubarba, aikin ma fa yinsa kawai takeyi amma
ba abinda ta iya bayi ruwa kawai take sakawa
ta dauraye duk da cewa umma ta nuna mata
wasu abunuwan, gadonsa kuwa sai Wanda ya
gani da yake shima gwanine gun shiririta haka
yake kwanciya akan gadonsa shi warine kawai
bayaso.
Bayan abokinsa ya tafi ya kwala mata kira ta
fito ya nunata da yatsa wallahi yau sai kin bar
gidannan Dan ba gidan ubanki bane, ko in
hallakaki matsayaciya kawai, tofaaa ran ta ya
baci ta tsani a zagi babanta ta kebe baki, ai bani
nakawo kaina gidan na ubankaba, ubanka ya
kawoni sai ka bari idan ubanka ya dawo sai ya
maidani gidan ubana kamar yanda ya daukoni,
ta fada cike da gadara da rashin tsoro. Sai ya
saki baki yana kallonta ta juya ta koma dakinta
ya bita da kallo,
Ita kanta tasan zata iya gayawa farhaaah ko
wace irin magana amma bata taba kawo ta kulla
masa sharri ko daya a zuciyantaba, haka kawai
yake bata tausayi kajifa..
Maamanshi ya kira, umma wallahi yau sai na
babbala wannan qazamar yarinyar batada
amfanin komai, umma dai nata bashi haquri dan
tasan zai rina, nan ya kwashe duk abinda ya
faru ya gayawa umma ita kanta umma ta jinjina
wa wannan yarinyar da Karen aikinta. amma
bata nunawa dantaba ta bashi haquri da kuma
yimai kashedin ya fita hanyarta Kuma kada ya
qara sa mata hannu, tace yakaiwa iffaaat waya,
waye iffaaat umma?? Itayarinyar mana,
baimasan sunantaba sai yau, kullum da yake
kullum da keee yake kiranta ya kwala mata kira
ta fito ya bata waya yaga dai batasan wayaba
bata Masan yanda ake amfani da wayarba sai
kawai ya sa speaker, taji ana kiran sunanta a
ciki, farko ta dauka radio ne yake magana sai
taji ana kiran sunanta habawa.... Ta wugar da
wayar Da gudu ta koma daki jikinta na rawa abin
ya bashi dariya sosai, sai ya bita dakin yana
shiga wani qarni da wari ya tarbeshi ya kasa
numfashi ya dawo Palo ya qara kiranta dagyar
tafito, ni kaina Jabo abin ya bani mamaki Dan
kuwa iffaaat ko lokacinda aka kaisu police
station bataji tsoronda taji yanxuba Ashe Akwai
abinda take tsoro.......
Mujeee zuwa muji ta'addancin da zatamai kamin
tafara........
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive