shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 12

WACE CE ITA..?? 12
*******by abba gana
Ta samu guri ta rakube nesa dashi, ya daure
fuska ki karba umma zatayi magana dake, ina
ummar? Magana take kuka kuka Ya zanyi
magana da ita? Ki karba nace jiki na rawa duk
ta rude ta karbi waya, ki daura a kunne takuwa
danna waya a kunne,tayi mutuwar tsaye, Tana
tsoron kar ta jata, wayar ma a juye ta daurata
sai ya shareta, to kiyi magana, kamin tayi
magana sai taji an sake kiran sunanta har zata
wurgar da wayar sai kawai ta daure ta amsa, jiki
na rawa, sundan gaisa, nan dai umma ta mata
magana akan ta daina yiwa yayanta rashin
kunya duk abinda yakeso ta mishi, ta amsa da
to zata daina, amma hajiya kice ya daina
dukana,!! gaban abokansa yake dukana kamar
jakar gidansu, duka.!? Eh, kuma kullum saiya
zagi margayi babana bayan na fada mishi
babana ya rasu yadaina, amma kullum saiya
zageni, kwallata ta cika mata ido batason a zagi
babant ko kadan. umma taji haushi sosai ta bata
haquri tace zatamai magana,daganan tadan
bata labari har tana dariya, tama manta da
tsoronda takeji,, haushi ya kama farhaan ya kira
amata fada, ta bige dakai qaranshi, har tanata
dariya, tana dariya shiko ya qura mata I do yana
kallon haqoranta da sukayi wani tsatsa, ta qare
ta kawo mai tana dariya ya kalleta ke wai laka
kikeci hala,kinga yanda haqoranki sukayi tsatsa
kuwa? Ta harareshi, ba laka naciba kashi
nakecii, tayi tsaki ta wuce dakinta, ya bita da ido
cike da takaicinta to waima miye amfanin kiran
umma da nayi? Gashi ba abinda ya chanza! Kalli
ko second goma ba'ayiba ta qara yimin rashin
kunya, shima yayi tsaki lallai an hadashi da
qaddara kuma umma tace sai ta dawo
za'achanzamai ita, nanda shekara daya kenan
lallai zaici uban yarinyar nan kuwa, dole ya nuna
mata WACE CE ITA, a duniya ya rasa horon da
zaimata taji haushi ko zata Dan natsu, ya kira
kukunsu yace daga yau kada ya qara yin girki da
ita, okay sir,
****
Da yamma mutuniyar taku ta tashi daga bacci
ta nufi kitchen taga wayam ba abinci da Rana
ma batachi komaiba yanxuma bataci komaiba,
tana tsaye saiga farhaan ya shigo, abincin sa a
shirye kamar yanda aka saba hadamai amma ba
nata ta kalleshi fuska a yatsine, Ina abincina?
Nine mai miki girki? Ko ni nasaba girka miki?
Karki manta kema yar aikinace so ki kula kisan
abinda kikeyi a gidannan ya bone. Ta kalleshi
rai a bace to dan ina Yar aikinka sai akayi mine?
Sai kada in nemi abincinda zanci? Ta kalleshi Ni
yanxu mixanchi ? Yana kai spoon a baki ya
tauna ba tare daya kalletaba Kici halinki ko ki
girka da kanki idan kin matsu,.! Tofa yau
za'aqure iffaaat yan mata......
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive