WACE CE ITA..?? 14
Na abba gana
Kiyi haquri tanada matsalar gwagwalwane, ta
wani zare ido kana nufin mahaukaciya kake
rayuwa,?? Haba Hoooney wannan ai gangancine
ta fada da qarfi, har saida iffat tajiyota, ta waigo
ta zare ido gasu masha Allah idonta, ido cikin
ido tace; waye mahaukaciya?? Rufee ta rungume
farhaan da qarfi kiyi haquri badake nakeba, rufee
dai taji tsoro, hankalinta ya tashi qarshe taqi
zama gidan tace sai dai ya kaita hotel Dan
bazata zauna da mahaukaciyaba ta hallakata.!
Haka dai rufee ta hana farhaan zama gida duk
gajiyar daya kwaso saida yakaita hotol, kuma ta
hanashi dawowa kar mahaukaciya tamai illa sai
gobe da dare ya lallabata ya dawo gida, iffaaat
dai fruits dinta takeci dare da rana amma taji jiki
ba kadan ba har ta chanxa kala, kullum tana
hanyar bayi tana gudawa.
Dan ma Allah yasa ba irin zainb khalifa bace mai
shegen ci da ba haka ba..
******
Yana isowa ta fashe mai da kuka wallahi saika
maidani gida!! angayamaka banida gata zata
ijiyeni ba abinci wallahi saika maidani gidanmu
ta riqe mai gefen riga tana kuka, anyi arziki
bataci kwalarshibama. sai yanxu ya kula da ta
Dan chanza kamar ta tame ta qara duhu ya tuna
da cewa ya hana abata abinci.! Girjinsane ya
buga to me takeci tsawon kwana 9?? Ya kalleta
sai kuka take sai ta bashi dariya kuma, Ashe
kawai abinda zaisaa wannan shu'umar kuka, yaji
dadi aransa ko banxa ya rage baqin cikin ta
kuma dama Dan ya bata wahala ya mata
hakan..
Sorry iffaaahh, na manta dana hana abaki
abinci, to mi kikeci kullum,?? bansaniba ta fada
a yatsine wato kai ka yahana a bani abinci,
wallahi Dana sani da ban mai kukaba duk a zuci
take maganar.!!
Kiyi haquri kinji, tana kallo ya kira kukunsa yace
a riqa girki da ita,tace bazanciba gida zaka
maidani, bai kulataba ya wuce abinsa.
Bayan kwana biyar farhaan ya sallami rufee,
Kwana na shida yazo da wata matar,
Itama yar gayuce irin rufee saidai wannan tafi
kyau, koda suka shigo iffat na goge Palo,
yarinyar ta kalleta ke kawo min ruwa mai sanyi.!
Ta fada a gajiye tafada kan kujera ta zauna iffat
ko kamar batajitaba, aranta tace dama matansa
biyu yaro dashi sai mata, baijira amsar iffat ba
Dan yasan halinta sarai batada kirki, yanda ya
gaji bazai iya fita nemawa ramsy hotel ba, ya
dauko mata ruwan ya kawo mata kixo mushiga
daga ciki kinga ana aiki anan ka shiga idan na
huta zan shigo ta fada alalace,
Ya wuce yabarta tana danna waya amma ranshi
baiso barintaba, kee mai aiki idan kin gama kizo
ki matsamin qafafuwana....
WACE CE ITA? 14
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Akarasa Mana Don Allah
ReplyDeleteThanks
ReplyDelete