shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 13

WACE CE ITA..?? 13
Na muhd abba gana
Ta kalli kitchen din ko za'akasheta ba abinda
zata iyayi a bayan buda fridge ba abinda ta iya,
kuma ga wasu abubuwa kamar fridge akai taga
ana girki. Za'ayi shegiya kuwa.ta kalleshi taga
yana kai loma hankalinsa kwance., tayi tunanin
ko ta barar mai da abincin da yake ci a jikinsa
sai kuma ya bata tausayi, kawai saita rakube
saida ya kammala Wanda ya rage shi tacinye....
**
Tafiya ta kama farhaan zuwa Lagos, ya tafi
satinsa daya baidawoba. tun ranar da ya tafi
batachin abinci saidai tabuda fridge duk abinda
taga nacine ta dauko ta chinye, cikenta ya
lallace kullum tana hanyar bayi, to anachin
abinda ba'asaba Chiba wasu kuma ba bisa
Qa'ida ake cinsuba duk wani abu da tagani mai
Dan gishiri gishiri da zaqi zaqi ta gama dashi.
Kaihar saida ta qare chiye chiyen takai batada
abincin da zatachi yau.
kwananta biyu bataci komaiba yunwa na
Neman ta hallakata.. tunda tazo gidan bata
taba koda fita wajen Palonba daga daki sai Palo
sai kitchen, batamasan qofar da ake fitaba...
Aranta taji ta fita haka ta biyo hanya tabi nan ta
leqa chan har tayi karo da qofar fita, ta baya ta
fita, Habawa, tayi murmushi taga S pool aranta
tace wato gidan nan hadda qaramin kogi sukeda,
ta waiga ta hango lanbu komai yaji fruit duk sun
nuna wasu sun fado a qasa Habawa tayi ciki da
sauri taci ayaba son ranta saida ta qoshi,
sannan ta kwance Dan kwalinta tayo guxuri ta
fito har zata wuce taga yanda ruwan nan sukayi
sky colour sai suka bata sha'a ta tu6e ta fada
tayi wanka sosai gata gwanar iya ruwa, gashi,an
Dade ba'ahaduba ta Dade a ruwan sannan ta
fito, dama tunda umman su farhaan ta tafi
batayi wankaba kwana goma kenan, ta fito cike
da nishadi an samu banxa, dagyar ta gane
hangar komawa daki taje ta chanxa tufafi tunda
wayannan sun jiqe, tana zaune Palo a qasa ta
miqe qafafu ta saka fruits dinta tsakiyar qafafu,
tanashan mangoro abin sai Wanda ya gani,taji
qamshin turare hadi da dariya koda ta duba
farhaan da wata mata yar gayu da qananan jaya
a jikinta tasha attach fuskannan tasha fenti
bakinnan yaji janbaki, ta rurungumo farhaan,
tana mai shagwaba suna ta dariya, sun bata
haushi haka kawai, ta miqe da dariyanta
tagaishesu a tunaninta matarsace, matar ta
mata kallon tsana da gyama ta kalleta a
wulaqance ta zubar, hooney miya kawo almajirai
a gidannan bayan kace min ba kowa dagakai sai
masu aiki biyu. Wai itama mai aikinace, .matar
ta wani jaa da baya honey wannan din?? Aiko
hanyar databi bana son nabi tana magana
ayangace tana wani rungumoshi, ran iffaaat ya
bace tuni tasha magani aranta tace Dan an
samu an gaishesu suke yiwa mutane wulaqanci
ba matar shi bace ko uwarshice tamin iskanci
zanci zan rama, taja wani dogon tsaki,ta
murguda baki ta wucesu, hooney kana kallo mai
aikin gidanku abinda ta mini...??
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive