shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 15

WACE CE ITA.?? 15.
by abba gana
Nan ma Tayi banxa da ita har ta qare aikinta,
tana neman ficewa palon, ta kalli iffat kizo ki
danna min hadda bayana kiyi min a hankali Na
gaji sosai, tana magana a wahalce irin ta gaji
dinnan, iffat nan ma ko ta mata banza ta fara
waqar ta badi ba rai soyayyar jigon rayuwa da
amana...... kusan kullum sai iffaat ta yi wannan
waqar Dan tana bala'en Sonta kuma baiti biyu
ta iya tun aqauyensu, ramcy taji shiru, ke kodai
kurmace ke? Kurmane kuma zaiyi waqa,! Kee
Ana magana kinyi banza da mutane, iffaat
Tamata kallon wulaqanci, shi mijin naki yace
miki aikina kenan danne dannen matansa??
Aikina biyune zuwa uku hajiya batace in ma
matansa tausaba.! ta miqe zaune Ke marar
kunyar yarinya, kina kallon mutane kamar kina
kallon kashi, wai ma Waye matar tasa? Zan miki
display a gidannan kuwa, iffat kam bata ko
kalletaba taja tsaki ta wuce dakinta, ramcy a
fusace ta tashi taje dakin farhaan, har ya fara
bacci ihunta ya tayar dashi, ya zaku ijiye mai
aiki Mara kunya a cikin gida yarinya har tana
mini tsaki.! Yadanja tsaki ya rasa abinda zaice,
aransa yace ki godewa Allah data tsaya akan
tsaki, bayason ta fahamci koshi iffat ba ragawa
takeyiba, cool down baby ba girman ki bane kina
fada da mai aiki in kin kula yarinyace, xata qara
magana ya janyota ya rungemeta.... nidai jabo
danaga abin zaifi qarfina sai kawai na bar musu
daki nayo waje.
Guraren maqreeb suka farka daga bacci suka
fito yunwa ta addabesu ya nema musu snack
suci, ramcy tace indomie take so tachi, kuku
kuma bayanan, to miye amfanin wannan
yarinyar? Basai ta girkamin ba, no ki barshi xan
girkamiki farhaan ya fada yana miqewa Dan
yasan iffaat zubar mai da mutunci zatayi, ramcy
dataga dai da gaske zai mata girkinne sai tace
ta fasa amma zuciyarta fall da tunanin miye
amfanin yar aikin, suna zaune suna hiransu suna
dariya iffaat ta taso tazo gabansu ta wuce, wani
warin datti ya daki hancin ramcy tace; kai amma
wannan yatinya na wari! Ta toshe hanci, iffat ta
waigo taceni nake wari? Farhaan yace ke ki
matsa ki baiwa mutane guri,an fada kina wari
qaryane bakya warin? Shima kallon banxa ya
mata yaci gaba da hiranshi, ran iffat ya baci
matuqa, ba'ataba fada mata hakaba wai tana
wari sai yau, ko qauye su dijee da rukayya ne
ake cewa suna wari ba wanda ya taba CE mata
tana wari ta wuce fauuuuuh kamar guguwa ta
tasooo, tana zuwa daki ta fara tunanin abinda
zatama matar farhaan ta rama, cox taji haushin
abinda ta fada mata, itaf ta dauka matarshice,
batasan matan banxa bane, tayi wata dariya
mugunta an samu idea ta miqe tsaye taje
kitchen ta dauko man gyada, tayi zaune duk ta
gogo gurin da ba carpet dashi tayis sai maiqo
yake yaji oil sosai, cox ta taba zubarda man
gyada a kitchen tafadi har sau biyu sai ta gane
cewa yana fadar da mutum, ita kanta da
tsantseni take tafiya har takai wani guri ta
zauna, ba'ajimaba kuwa saiga ramcy an fito da
kayan bacci kamar tsirara, tana fitowa daki tana
yatsine yatsine, sai wayanta tayi qara
juyawanda zatayi ta dauko wayan, kikajita
teeeeem ramcy anfadi qasa ansha qasa, ta fadi
saman hannunta tayi wata qara, iffat ta
gyalgyale da dariya, tazo kanta tana kallonta
tana dariya, ramcy kuwa sai kuka takeyi tace da
bana wari Dana taimakeki Amma ina tsoron in
saka miki warina .......
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive