shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 18 July 2015

WACE CE ITA? 16

WACE CE ITA..?? 16
Na ABBA GANA
Maimakon ta dagata din amma ina sai dariya
takeyi, ramcy sai kuka take tana ki taimakeni
iffaat taci gaba da wa qarta ta badi barai, tayi
sauri ta goge duk gunda ta saka mai,ramcy nata
kiranta ta taimakamata amma iffaat kamar ma
batajiba, hankalinta kwance, ramcy ta rarrafa
taja jiki ta dauko wayanta ta kira farhaan ta
gayamai faduwan da tayi da dariyar da house
girl dinsa tamata ba'ajimaba saiga farhaan da
Dr. Sunzo Dr. ya duba ramcy akace hannunta da
qafarta sun targade, farhaan yaje dakin iffaat
batanan yaje ko ina batanan kamar daga sama
ya ganta ta chiko dan kwali da fruit lambu taje
kenan, tana qarasowa ya wanketa da mari.!saida
abinda ta debo ya watse, Ke dan ubanki Mara
tarbiyar inace ke?? Mace ta fadi Dan bakida
tausayi idan baki taimaketa kin dagataba ai
bakya mata dariyaba, Dan Kinga ina gyaleki a
gidannan kike abinda kikaga dama, karfa ki
manta ke ba kowa bace illa yar aiki, kuma
wallahi zan riqa chin ubankine, wawuya Mara
tarbiya.!! Ya fada a hasale ya wuce daki gun
ramcy, ranshi a bace yaci gaba da rarrashinta...
ran mata ya bace ga duka ga zagin chin
mutunci, ta fashe da kuka, ta fito harabar gida
ta rakube wani guri tasa kanta a cikin chinya ta
fara kuka, kuka take sosai cox ranta ya bala'en
baci ba'ataba samun nasara akantaba irin
wannan wato duk dabarar da zatayi dan ta rama
abin da ya mata ta sai taji yana bata tausayi
bazata iyaba, shegiyar matar ya kamata ta qara
yiwa wani sharrin, haka taci gaba da kuka har
farhaan ya fito zaikai ramcy asibiti ya sameta
anan ya zabga mata harara ya wuce abinshi, har
sukaje suka dawo tana kuka sai ta bashi tausayi
yaje ya ijiye ramcy ya dawo, kewai mi kikeyi
anan,? ki tashi ki shiga ciki kinzo kina ma
mutane kuka, tayi banza dashi yayi yayi tun
yana fada fada har ya dawo rarrashinta, har ya
gaji taqi daina kuka kuma taqi tashi, ya gaji ya
koma chikin gida, iffat dai ta gaji da kuka tayi
bacci anan, har gari ya waye guraren 9 farhaan
zaije skull yaganta anan kwance ya rasa yanda
zaiyi da ita sai kawai ya dauketa a hankali
yakaita Palo saman kujera ya shinfidar, ita kuma
ramcy tana Palo zaune saman keken guragun
da aka bata, tamai kallon tuhuma waye ka
dauko, sheeeeeeee, ya dora yatsansa akan
lebensa yace kada tashi, banganeba yar aikice
kake dauka, yace batada lafiya, jiya sabida
abinda na mata akan ki waje ta kwana. Ramcy
tace then so what Dan ta kwana a waje, ya bata
amsa da then so keep quiet kada ta tashi nace!
Tamai kallon tuhuma farhaan ka gaya min WACE
CE ITA??
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive