shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday 12 February 2022

NASIHA GA MATAN DA ZA’A YIWA KISHIYA - SIFFOFIN UWA TAGARI 13

NASIHA GA MATAN DA ZA’A YIWA KISHIYA - SIFFOFIN UWA TAGARI 13


Ki zama mai maida al'amuranki ga sarki Allah, shine ya zama gatanki majubincin al'amuranki, in kikai haka kin tsira daga zuwa wajen bokaye da yan duba dan kulla makirci. Ki kasance mai yadda da qaddara domin kuwa tuntuni Allah ya hukunta zaku zauna karkashin miji daya. 

Ki sanya wa ranki cewar mijinki yayi riko ne da sunnar Annabi SAW. Ki zama mai hakuri saboda Allah, ba mai hakurin tilas ba. Karki takurawa mijinki akan abubuwan al'ada kamar kayan fadar kishiya da kayan gyaran daki. 

Karki kuskura ki yarda da zugar kawaye, yan uwa ko kuma iyaye Wadanda zasu umarceki da ki tada hayaniya ga mijinki ko kuma kishiyartaki, ki sani cewa mutuncinki da kimarki zasu zube a idanunsu. 

Ki dauka kishiyarki yar uwarki ce abokiyar zamanki ce wajen taimakawa maigidanku yadda zai tafida rayuwa da harkokinsa baki daya. Ki kasance mai bata shawara ta gari wajen sha'anin zamantakewar aure, ku zama masu biyayya ga mijinku matuqar bai sabawa umarnin ubangijiba. 

Idan kika aikata haka yake yar uwata zaki shiga cikin sahun mata nagari wadanda sakamakonsu shine aljanna.

Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).