Ki zama mai godiya ga Allah daya kawoki lokacin aurenki domin byyaiwa ce yayi miki wasu suna nan basu samu ba.
Karki sabawa Allah a wajen sha'anin biki, abinda ya kyautu Shine kiyi godiya gareshi.
Kiyi taka tsantsan da shawarar qawaye, kar su baki shawarar da za su burmaki domin da yawa akwai makiya wanda basu samu wannan ni'imar da kika samu ba.
Ki zama maiyin hanzari akan abinda mijinki yake so. Ki kula da lokacin da yake farinciki, kar kuma ki zama mai bakin ciki lokacin da yake farin ciki ko bakin ciki.
Duk lokacin da yazo miki cikin bacin rai ko fada to ki zama ruwan sanyi don yayyafa masa wajen kwantar masa da hankali Ki yi kokari ki zauna da 'ya'yan kishiryaki lafiya ba tare da kin tsangwame suba.
Ki yi nazarin halayen uwar gidanki hakan zai taimaka miki wajen kyautatuwar zamanku, Ki guji taba alfarar iyayensa da yan uwansa da kuwa abokansa.
Karki zama mai yawan kai karar kishiyarki ko talanta gurin mijinku, ki koyi hakuri da kawaici.
Ki zama mai hakuri da juriya, kar wani tsanani yasa ki sauka daga kan abubuwan da aka dora ki akai na kyautatawa da biyayya ga mijinki.
Idan kikai hakan sai ki zama daga cikin mata nagari wanda zasu samu tsira ranar gobe kiyama.
0 comments:
Post a Comment
pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.