shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday, 5 January 2016

NA DAINA SO!! 21 & 22

na-daina-so.jpgna-daina-so.jpg NA DAINA SO 21 Muh'd-Abba~Gana 09039016969 NASAN kina tunanin kamar zan ga kina yi min rashin mutunci to ina mai tabbatar miki da cewa bana daga cikin samari masu karamar kwakwalwa na dauki alkawarin zan ke yi miki addu'a a kan Allah ya tabbatar da alkhairi tsakaninki da wanda kikeso yasa ya zama miji na gari wanda zai ke kula da hakkokikin ki ki cire damuwa daga zuciyarki ki kwanta kiyi bacci sai da safe har ya isa wajen kofa da zummar ficewa daga dakin ya tsaya sakamakon kiran sunansa da tayi yaya kabir na'am to...ka kana da wata budurwar ne? murmushi yayi ba tare da ya bata amsa ba ya fice daga dakin sai dai kafin ya fita sai da mairamu taci nasarar ganin hawaye a fuskarsa. kwanaki biyu da faruwar al'amarin kabir ya bayyana wani labari a gida labarin da ya girgiza kusan kowa domin mahaifiyarsa ya fada wa cewa ya janye maganar son mairamu a yayin data nemi dalilinsa na daukar wannan matakin kawai ji nayi na fasa.....kuma na tuna akwai wata da muka taba yin alkawarin aure a birni ya kawo wannan uzirin ne don gannin bai dorawa mairamu laifin komai ba itama ta fuskanci haka a zahiri ya hakura amma a badini ba zai iya ba babu irin kokarin da kabir bai yi ba don ganni ya cire son mairamu daga zuciyarsa amma abu ya faskara kusan ko yaushe kuma a duk inda yake akwai tunanin mairamu a tare dashi har kokarin yin wata budurwar yayi don ganin ya shafe babin rayuwar mairamu daga zuciyarsa da rayuwarsa gaba daya to amma daga bisani ya gano cewa babu gurbin da wata zata iya samun mafaka ko da ta siyasa ce a zuciyarsa saboda yadda mairamu ta yi mamaya yana ji a jikinsa idan har ba mairamu ba to ba zai iya yin aure a rayuwarsa ba zai mutu tuzuru NA DAINA SO 22 Muhd-Abba~Gana har bayyan sallar magariba ba wani labari shin ko fitowar yamma yayi? mairamu ta tambayi kanta bayan da ta idar da sallar magariba tun la'asar cikita ke gugi saboda azababbiyar tunwar dake addabarta amma ta ki yarda taci komai don ta tsara cewar da mijinta zasu ci tare duk da cewar tana sa ran murnar ganinsa ma kadai zai iya hana ta cin abinci mai yasa har yanzu bai iso ba? karfe takwas na dare agogon dake manne a jikin bangon dakin ya nuna mijinta bai dawo ba to ko fitowar dare yayi? ko motace ta lalace musu a hanya? ko hatsari suka yi? ko yan fashine suka tsare su? bata yi aune ba sai taji hawaye na barazanar fitowa daga idanunta sannan al'amari ne cewar hanyar shigowa kauyen bata da kyau ana yawan yin hadarirrika baya ga yan fashi dake tare mutane daga lokaci zuwa lokaci hadari? yan fashi? tana faran ba daya daga cikin wadannan al'amuran ne......rashin fitowa da wuri? amma mai yasa bai fito da wuri ba? kuma ma...........tunanin dake kwakwalwarta ya datse kusan a lokaci guda numfashinta ya nemi daukewa sakamakon kwankwasa da taji an soma yi. www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).