shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 15 January 2016

NA DAINA SO!! 39 & 40

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 39Muhd-Abba~Gana


take tattara tufafinsa wadanda suka yi datti ta wanke masa ta tuna irin yadda take tarairayar mijinta irin yadda take ji da shi kamar tsoka daya a miya amma kuma......... sauri tayi ta dafe gefen kanta sakamakon ciwon da ya soma yi to amma ba yadda zata yi ta hana tunane-tunane kutsawa cikin kwakwalwarta tun bayan yin bikinsu da watanni shida yusuf ya hadu da wata irin rashin lafiya mai zafin gaske kusan duk wani abu da mairamu ta mallaka sai da ya kare a hanyar nema wa yusuf magani akwai wata gona da ta gada daga wajen mahaifinta mutumin da bata taba gani ba saboda ya rasu ne kafin a haifeta har gonar sai da ta sayar don ganin mjinta yusuf ya samu lafiya sannan kusan komai ita take yi masa sakamakon tsamarin da rashin lafiyar tayi sai dai a kwantar a tayar daga karshe dai ya warke daga cikin kashi uku na kudin gonar kashi daya ya tafi a kudin magunguna kashi daya kuma ya salwanta a kudin abinci da kayan cefene yayin da kuma taba shi kashi daya ya ja jari mairamu bani da kalmomin da zan iya amfani da su wadanda zasu iya biyyana hakikanin irin farin cikin da nake yi da Allah ya bani ke a matsayin mata abin da kawai na sani shine ina daya daga cikin wadanda sukayi dacen samun mace ta gari kuma ina yi miki godiya a bisa kokarin da kikeyi min Allah ya saka miki da alkairi shin mai kike so a waje nΓ’?


Muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz

NA DAINA SO 40


Muhd-Abba~Gana

kayi min alkawarin cewa har abada zaka rike amanata wannan ne kawai burinki? kwarai kuwa na sha yi miki alkawari kuma ina mai kara jaddada miki cewa you are the one and only one' i love you more (kalmar wani i love u karyane injini) shi duk ire iren wadannan kalam da yusuf ya sha fada mata kanzon kurege ne? mai yasa zai yi mata haka ? kudin da ta bashi da shi yayi kasuwanci har kasuwancin nasa ya bunkasa ya yanke shawarar zai je birni ya nemi wani aiki sannan ya ci gaba da bunkasa jarinsa watakila da yaje jarin nasa ya bunkasa watakila a cikin jarinne har ya samu ya auri surayya daga bisani sai data nemi wannan mujallar ta karanta a boye duk da ta san cewa yin hakan ba karamin karin takaici da bakin ciki ba ne a gare ta abin dayafi dugunzuma tunaninta lokacin da dan jarida ya tambayi yusuf cewa shin ya taba yin aure? ban taba yin aure ba!! kuma ba zan kara yi ba! surayyace kadai matata ta haddace maganar daya fada furuci mafi tayar da hankali a shekara shin hakan na nufin yusuf ya manta dani? mairamu ta tambayi kanta a karo na barkatai bata tsammani hawaye a idanunta sai dai hawayen jini..... wanda yace namiji uba ne to tabbas zai mutu maraya.............namiji ba dan goyo bane .........maza kwandon zawo........maza tabarmar kashi.......maza mayaudara .......maza maha'inta!!! ( wallahhi bandan)

Muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).