shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 15 January 2016

NA DAINA SO!! 41 & 42

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO! 41
Muhd-Abba~Ganaamma zata ji dadi kuwa idan aka ce yusuf mayaudarine? shin yusuf zai dawo? wata rana zai tuna da ita ya dawo? idan ya dawo zai nemi gafararta? idan ya nemi gafararta zata iya yafe masa kuwa? babban abin da yafi ci mata kawo a kwarya har yanzu tana son yusuf kuma tana ji a jikinta kamar ba zata iya daina son shi ba lalle so babbar cuta! kiyi hakuri mairamu na san cewa nayi laifi babba don Allah ki yafe min yusuf ne ya durkusa a gabana yana bata hakuri nima wannan al,amarin ba,a son raina ya faru ba har da hawaye a fuskarsa na yafe maka.........na yafe maka....tana mai kuka ta fadi hakan a daidai lokacin ta farka daga barci cikin talatainin dare sharkaf! jikinta ya jike da gumi takaici ya lillibeta bayan data tuna da mafarkin da tayi tana sa ran wata rana mafarkinta zai zama gaske tana sa ran kwananta ya kusa karewa WASHE GARI DA SAFE tana cikin wanka taji an kwala mata kira tsayawa tayi cak! muryar irin tasa ce.......a,a ba irin muryarsa bace
... muryarsa ce mana kiranta a ka kuma yi a karo na biyu daga can daki ake kiranta hakika muryar yusuf taji.


Muhd-Abb~Gana

www.abbagana.pun.bz

NA DAINA SO!42Muhd-Abba~Gana


yusuf ya dawo! ya dawo bata hakuri bata damu da wanke kumfar da ke jikinta ba zani ta daura ta fito a guje daga bandaki ta nufi daki arba tayi da kabir tsaye a kofar falo lafiya ya tambaye ta a razane ya...ya..da..wo?? ta tambaye shi a rude sannan kafin yace wani abu taci gaba da magana yayin da numfashinta ke neman dukshewa daga jikinta kamar mai fama da ciwon asima na....na...na jiyo muryarsa ba muryarsa bace muryata ce inji kabir a guje mairamu ta karasa cikin daki don ta tabbatar ba kowa a dakin karo na farko da kabir yaji tsoron kada mairamu ta haukace a sanadiyyar cin amanar kauna a ranar bayan da mairamu ta idar da sallar la,asar lekawa tayi kofar gida a in da ta hangi yusuf tsaye yana yi mata murmushi na san dama zaka dawo kusan da karfi ta fadi hakan yayin da ta nufe shi a guje rungume shi tayi tana kuka ture ta yayi cira kai tayi ta kurawa fuskarsa ido sai a lokacin ta kula mutumin da ta rungume ba mijinta bane kuma ba mijin surayya bane sunansa kallamu kusan duk sa,ilin da mairamu ta kwanta bacci sai tayi mafarkin yusuf a wasu lokuta yana bata hakuri yayin da a wani sa'in yake yi mata wulakanci iri daban-daban jefi-jefi surayya a mafarkin sau da yawa tana kyalkyala mata dariya.Muhd-Abba~Ganawww.abbagana.pun.bz
Share:

1 comment:

  1. Sulaiman dutsenreme29 March 2016 at 09:35

    Gaskiya kana kokari mallam abba allah ya kara basira

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).