shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 9 January 2016

NA DAINA SO!! 29-30-31-32-33-34-35

na-daina-so.jpg

[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 34


Muhd-Abba~Gana

daga cikin bayanan da yusuf yayi kwata-kwata bai nuna cewa ya taba yin aure ba balle yace ya baro mata a kauye kawai dai yace shi dan asalin kauyen kantafarfara ne wani irin bakin ciki ya kai farmaki zuciyar kabir yayin da ya tuna da irin so da kaunar da mairamu ke yiwa yusuf ya tuna da irin dagewar da tayi don ganin yusuf ya zama mijinta to so shi a lokacin da bashi da komai ya tuna da irin yadda mairamu taki yarda a raba aurenta da yusuf bayan daya koma birni da zama ya barta a kauye,ya tuna da irin shekarun da mairamu ta shafe tana jiran dawowar mijinta amma daga karshe abin da zai yi mata kenan? mene ne dalili? kabir bai yi aure ba sai tsintar kansa yayi yana zubar da hawaye hawayen bakin ciki da takaici hawayen tausayin rayuwar mairamu hawayen bakin ciki shekarun da mairamu ta salwantar tana jiran dawowar wanda ba zai dawo ba hawayen nadamar goyon baya da yayi tun a farko har aka yi wannan aure hawayen rashin sanin ta hanyar da zai bi don ganin ya kankarewa mairamu bakin ciki da bacin rai na shekara da shekaru hawaye abin da ya faru hawayen abin da ke faruwa,by muhd abba gana,hawayen abin da zai faru lamari irin na kauye.

Muh'd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 29


MUH'D-ABBA~GANA


HABA yaya ka...kabir kamar yadda ka ka boye sona a cikin zuciyarka haka zaka boye abin da nake gani a zahiri dukkaninsu shiru suka yi na tsawon wasu tsirarin sakanni yaya kabir don Allah ka daure kaima kayi aure baice komai ba babu kalmomin da zan iya amfani dasu wajen yi maka godiya game da irin dawainiyar daka yi min a rayuwa,amma abin da zan ce kawai shine Allah ya saka maka da alhairi ya saka mana gaba daya ina yi miki fatan alkairi Allah ya baku zaman lafiya ke da mijinki......
ba karamin farin ciki kabir yayi ba yayin da ha ga ma'auratan sun zauna lafiya sai dai shi ya kasa yin koda soyayya balle a je ga batun yin aure ba karamin kaduwa yayi ba sa'ilin da ya samu labarin cewa yusuf zai je birni yana tsoron zuwansa birni saboda..............a'a ai ya shiryu.Allah ya shirye shi ya daina lokacin da aka debi tsawon watanni takwas zuwa tara ba tare da yusuf ya dawo gida ba kabir ya tsinci kansa cikin matsanancin damuwa saboda tunani daya yi na cewar mai yiwuwa yusuf ya koma gidan jiya. karo na farko da kabir ya gane cewar yayi kuskure daya goyi bayan mairamu har ta zama matar yusuf.
MUHD-ABBA~GANA

www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 33


Muhd-Abba~Gana

WATA firgitacciyar kara ta kwalla kafin ta dafe kokon kanta da hannu biyu bayan addu'o'in da aka yi ta tofa mata sai da aka kira wani likita yazo yayi mata allura kafin bacci ya ci nasarar sace ta ganin irin yadda jikin nata ke ci gaba da daukar zafi kamar kwanon tuyar da aka dora a kan wuta ya sa da sassafe a ka dauke ta zuwa asibiti asibiti daya ne a kauyen har ruwa aka kara mata kwanakinta uku a asibitin kafin a sallame ta da magunguna baya ga allurai lokacin da mairamu ke kwance a gadon asibiti kusan duk sa'ilin da ta bude ido sai tayi tsammanin ko zata ga mijinta yusuf a kusa da ita ya dawo daga birni bata ganshi ba kabir ya yi matukar girgiza daya samu labarin sanadin wannan rashin lafiyar shima da ya nemi mujallar ya karanta labarin ya bashi tsoro matuka saboda tunanin halin da mairamu zata tsinci kanta a ciki,by muhd abba gana, tabbas yusuf ne! mijin mairamu ya auri jarumar fina-finan hausa! bayan tafiya dayayi ya bar matarsa tsawon shekaru ba tare da ta ji duriyarsa ko da sau daya ba karo na farko da aka samu cikakken labarinsa shine yayi aure a birni har hira da akayi da yusuf a mujallar,sai da kabir ya karanta.

Muh'd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 30


Muhd-Abba~Gana


BAYAN da mairamu ta bude kofar ne ta tsaya turus!! kamar wacce tayi mugun gamo ba mininta bane ya dawo wata gajeriyar mata ce tsaye a kusa da kofar ba yau ta fara ganinta ba kuma jiya ba karewa ma makota ne babarbariyace ce ana kiranta da hajja gana shi ya sa ta tambaye ta a kidime hajja gana lafiya?? shiru ta dan yi kafin ta soma magana kin tuna kanina mas'ud da ya tafi birni satin da ya wuce? eh na tuna to dazu ya dawo daga birni? ehhhhh shin ya hadu da yusuf ne? hajja gana batace eh koh a'a ba wanda wannan ya taimaka wajen karasa tayarwa da mairamu hankali tabbas hajja gana tafe take da wani mugun labari mairamu ta raya a ranta kuma ga dukkan alamu labarin ya shafi yusuf wani abune ya same shi? hatsarin mota ne ya ritsa da shi? yan fashine suka tare shi? rashin lafiya ce ke damun sa? mene ne wai kam?


Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 32


Muh'd-Abba~Gana

TABBAS jarumar film ce sunanta surayya to mene ne hadin wannan fisararriyar buduwar da mijina? cikin daga murya mairamu ta fadi hakan bayanin ba shi da dadi" fada min ko mene ne aure suka yi da yusuf ta soma ja da baya kamar wacce ake nunawa mutuwa yau satin su biyu da aure inji hajja gana karyane!! karyane!! karyane!! wallahi karyane! yusuf ba zai min haka ba babban burinta a wannan lokacin shine kawai kasa ta dare ta fada ko kuma rufin gidan ya ruguzo mata a kwanya to amma ko ba komai tayi farin ciki sa'ilin da wani matsannancin duhu ya soma lilliba bargo a kwakwalwarta lokaci guda numfashinta ya soma dakushewa daga jikinta har ta kai ta kawo ta gaza ci gaba daja da bays abu na karshe da zata iya tunawa shine hajja gana ta nufo ta da hanzari da zummar ta ringumeta don hana ta faduwa amma ta makara

* * ** **


cikin talatainin dare mairamu ta bude ido farfadowa tayi daga dogon suma?ko kuma farkawa tayi daga bacci mai dauke da mugun mafarki? kwance take a kan gado mutane kewaye da ita ga dukkan alamu addu'oi ake karanta mata yayin da mahaifiyarta ke karanta Al-KUR'ANI.hakika abin da ya faru ba mafarki bane babban takaicinta a cikin jama'ar dake wajen bata ga mijinta yusuf ba yayinda ta tuna da hoton bangon mujallar nan take kanta ya soma yin wani irin ciwo yayin da a sa'i guda matsanancin zazzabi ya lillibe ta maganganun hajja gana ne suka soma sintiri suna barazanar wargaza mata kwakwalwa a cikin mujallar nan aka yi bayani tun sati biyu da suka wuce aka daura auren wannan shahararriyar jarumar......ya aure ta ya ma riga ya aure ta ya aure ta!! ya aureta!! ya aureta!!!


Muhd-Abba~Gana

www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO 31


Muh'd-Abba~Gana


fada min mai ya faru? ya hadu da yusuf ne? a'a bai badu da shi ba amma....... amma me? kiyi min bayani mana wata mujjaa ya siyo......mujalla? shi mas'udun? eh a daidai lokacin hajja gana ta mikawa mairamu wata mujjalla cikin rashin fahimta mairamu ta karbi n
mujallar ta duba bangon hoton data gani a jikin bangon ne yasa saura kiris mujallar ta subuce daga hannunta hoton mijinta ne!!!!! dogo mai doguwar fuska fari mai fararen idanu siririn saje da dan madaidaicin gashin baki daya bari ne ya nemi ya mayar da shi jami'in tsaro yayi matukar kara kyau fiye da yadda ta san shi idan har akwai abin da bai sauya ba a tare da shi to bai wuce irin murmushinsa ba hoton da ta gani a kusa da yusuf ne ys sata ji kamar an doka mata tabarya a kirji domin hoton wata kyakkyawan budurwace mai siffa irin ta larabawa itama budurwar murmushi takeyi kamar yadda yusuf dinke murmushi sai daga bisani ta lura da cewa yusuf din rike yake da hannun wannan budurwar......shin a ina ta taba ganin fuskar wannan budurwar? rudewar da tayi ba zai iya barinta tayi wani kyakkyawan aiki da kwakwalwan ba hajja ga.....gana.me....mene wannan? kin gane wannan budurwar ? ba....ban gane ta bs wa cece???????


Muh'd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
[5:47PM, 1/9/2016] Bana: NA DAINA SO!35


Muhd-Abba~Gana

cikin kankanin labari ya karade mutane da dama sun girgiza da samun wannan labari wasu ma har da zubar da hawaye saboda tausayawa ga mairamu yayin da kuma wasu ke korafin cewa laifintane data riki namiji uba , tuntuni an bata shawara taki yarda inji wata mata a taron biki, yanzu ai ta gane cewa namiji ba dan goyo bane inji wata tsohuwa,to yanzu ya zatayi?,wani mai sayar da itace ya tambayi abokinsa amma har yanzu fa bata tsufa ba, cewar wani saurayi a majalisar yan zaman kashe wando,amma gaskiya yaci amanar yarinyar nan wani dattijo ke fadawa abokinsa a kan hanyar su ta zuwa masallaci idan yar uwata ce har birni zan tafi naje na yi masa mugun duka inji wani mafarauci nida za ta amince ma ai da sai na aure ta inji wani mafi talauci a kauyen haka dai labarin mairamu yazo kanun labarai kusan ko'ina tun daga cikin masallaci zuwa kan hanya majalisun samari da dattawa balle kuma taron dake hada mata ko kuma yan mata tun ina budurwa mijin nata ya gudu ya barta watar mata mai yaya hudu take bawa wasu yan mata labari amma ga dukkan alamu ya zama mai kudi inji wata daga cikin wadanda ake bawa labarin mai yasa kika fadi haka? mai magana ta farko ta tambaya, saboda jarumar film din ya aura ni abin ma daya fi bakanta min rai kenan karo na farko da wata daga cikin wadanda ake bawa labarin tayi magana aduk fadin birnin ya rasa wacce zai aura sai mai yin wasan kwaikwayo" kusan duk inda mairamu ta tafi ana zundenta wasu ma har dayi mata jaje kamar wacce aka yiwa gobara a kan haka ta yanke shawarar daina fita ko'ina sai in da wani kwakkwaran dalili.


Muhd-Abba~Gana


www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).