shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 2 January 2016

NA DAINA SO!! 13 & 14

na-daina-so.jpg NA DAINA SO 13 Muhd-Abba~Gana tun yana karami ba shi da abokin fada ko musu baya yi balle a kai ga tankiya ko yaushe yana zaune shiru-shiru kamar baya magana yana daga cikin tsiraran samari kauyen da iyayensu suka biya musu kudi suka je suka yi karatun boko a birni tun yana karamin mutum ne shi mai matukar jin tausayi don ko da babbar sallah ba ya iya tsayawa a wajen da ake yanka raguna don yanzu sai ya fara hawaye ba wai dabbobi kadai da tsintsaye yake tausaya wa ba har ma da mutane musamman mata yana daga cikin mazajen daba son ganin ana wulakanta mata,musammam ma ta fuskar tauye musu hakki a mu'amala ta auratayya ya jima yana takaici da tananin ta hanyar da zai bi don gannin an daina dannewa mata yanci a kauyen kantafara amma har yanzu hakarsa bai kai ga cimma ruwa ba daga cikin wadanda yafi tausayi a duniya akwai mairamu mairamu: kanwa a zahiri masoyiya a badini tun kabir na karamin yaro yake matukar kaunar mairamu wacce kusan kanwa ce a gare shi tun da mahaifiyarsa kanwa ce ga mahaifiyar mairamu tun suna yara sun shaku da juna mairamu tana daukan kabiru a matsayin dan'uwanta kuma yayanta domin tana kiranaa da irin sunan da sauran kannensa ke kiransa da shi wato yaya kabir yana daukanta a matsayin kanwa kuma masoyiya domin ya jima da yanke hukunci a kotun koli na zuciyarsa kan cewa mairamu ce zata zama matarsa idan lokacin yin aurensa yayi to amma a yadda ya tsaya ba zai sanar da mairamu sirrin dake zuciyarsa ba har sai lokaci yayi (KUSKURENE!!!) yana sa ran itama tana sonshi (GANGANCINE!!!) ko da bata sonshi to yana da tabbacin zata so shi idan ya nemi hakan ya kasance (HASASHE!!) lokacin da kabir ya kammala karatunsa a birni bayan da ya dawo gida ya ga irin tashen da mairamu take yi da irin yadda samari ke yawan yin hirarta wasu ma a cewarsu a tarihin kauyen kantafarfara ba a taba ganin budurwa da ta kai mairamu farin jini ba a kokarin sa na yiwa tufkar hanci kabir yana ganin yanxu ne lokacin da ya dace ya bayyana wa mairamu sirri da ya jima yana boyewa a zuciyarsa don ayi musu baiko musamman ma da yayi la'akari da abin da mahaifinsa yace na ya fito da wacce yake so kafin karshen shekara yayi aure tabbas yaba da zabi sunanta mairamu sai da ya fara sanar da mahaifiyarsa tayi matukar farin ciki da jin labarin da dan nata ya bata murna kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha tabbas kayi dace da mace ta gari abin da mahaifiyar tasa tace masa kafin taje ta sanar da mahaifinsa hannu biyu mahaifin nasa ya karbi abin don a cewarsa ya jima bai ji labarin farin ciki irin wannan ba nan da nan magana ta bazu a cikin gida na cewa yaya kabir yana son mairamu to amma sa'ilin da kabir ya tunkari mairamu da maganar al'amura suka rikice masa akwai wanda take so!!!! NA DAINA SO 14 Muhd-Abba~Gana HAR BAYAN AZAHAR BAI ZO BA shin ko bai fito da wuri bane? miramu ta tambayi kanta to mene ne ya hana shi fitowa da wuri? aiki ne yayi masa yawa? to wanne irin aiki? tsawon shekara shida bata sa shi a kwayar idonta ba kuma yau din ma da zai dawo gida shin ba zai zo da wuribane? da matsala miramu idan ina tare da ke komai na duniya kan zame min abu kyakkyawa babu wani aiki a duniya nan da zai iya shagaltar dani daga barin tunanin ki kece madubin zuciyata idan ban ganki ba bana jin dadi dadadan kalaman mijin nata yi ta tunawa wadanda a halin yanzu ta kasa gane matsayin su tsakanin zancen mafarki wakokin wasan kwaikwayo da kuma ire iren tatsunkyoyin mutanen farko sai dai har yanxu tana ganin ya dace taci gaba da ba shi uzurin na watsi da yayi da rayuwarta a'a ba watsi yayi da rayuwarta ba kawai dai mantawa yayi da ita a'a ba mantawa yayi da ita ba hasali ma ba zai iya mantawa da ita ba kawai dai rabuwa yayi da ita to shin rabuwa kawai ne? kuma har tsawon shekara shida duk yadda ta kai da son boye laifin mijin nata tana ganin wannan karon baza ta iya kare shi a babbar kotun da ke zuciyanta ba mai yasa yayi min haka? shi kadai ya san amsa har bayan sallar la'asar babu wani labari kusan sau shida a cikin awannni daban daban tana jin kwankwasa a guje take zuwa ta bude kofar gida amma ga karin takaici sai taga babu kowa daga karshe dai ta gano cewa kunnuwanta ne ke zolayanta a halin yanzu babu kuzari a tare da ita bayan gajiya data yi da kaiwa da komowa a tsakar gidan zama tayi a kan tabarma ganin da hada kai da gwiwa tunani ta soma yi na musanman a kokarinta na gano daga inda matsalar ta samo asali a can gefen kauyen nasu a bakin wani wani karamin rafi miramu ce da kabir ke fuskantar juna amma ita mairamu tafi sunkuyar da kai da kallon fuskar dogon saurayinta a lokacin kwananta biyu da samun labari a gida labarin da yayi matukar girgixa tunaninta labarin cewa kabir YANA SONTA!!! Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz
Share:

0 comments:

Post a comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).