shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 11 January 2016

NA DAINA SO! 36

na-daina-so.jpg

NA DAINA SO 36






Muhd-Abba~Gana






makwanni hudu da faruwar al'amarin har yanzu ganin abin take yi kamar wani mugun mafarki mai tsayi wanda har yanzu ta kasa farkawa ta wani bangaren kuma abin yafi kama da mummunan tunanin al'amarin da ba zai taba faruwa a gaske ba sai dai ko a cikin ire-iren tatsuniyoyin mutane masu ikirarin kare hakkin mata ta wani bangaren kuma labarin na kama da ire-iren labaran da ake nunawa a cikin wasannin kwaikwayo na zunzurutun cin amanar mata da mazaje keyi a wannan zamanin abin da har yanzu take yawan tambayar kanta game da wannan al'amarin shin gaske ne mafarki ne, tunanine,tatsuniya ce ko kuma al'mara? sanye take cikin wata doguwar riga har kasa mai launin sararin samaniya kanta babu kallabi zaune take a kan kujera tayi jugum! kamar wacce aka sanar da ita adadin kwanakin da suka rage mata a duniya ta rame sosai saboda rashin cin abinci yadda ya kamata kuma ga tunanin wannan al'amarin kusan ko yaushe na barazanar wargaza mata kwakwalwa kusan tun ranar da wannan mummunan al'amarin ya faru na samu labarin yusuf yayi aure a birni gidan baya rabo da mutane don likita ya bar da shawarar cewa a daina barinta ita kadai ko yaushe gidan cike da jama'a a nata faman raha da barkwanci kamar yadda likita ya bayar da umarni sai dai ita kwata-kwata bata son yin magana balle a je ga batun yin raha duk kuwa da irin kokarin da mahaifiyar da kuma yan uwata suka dinga yi don ganin hankalinta ya kwanta don ganin ta manta da rayuwar yusuf kwata-kwata.






Muh'd-Abba~Gana






vwww.abbagana.pun.bz
Share:

3 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).