shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Saturday, 16 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 48

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA

48

MUHD-ABBA~GANA Da Amrah

Ganin banda niyyar fada mata ne yasa tace "Wahida talk mana", A hankali na share hawaye nace "Mahida tabbas idan nace bana son Bomboy nayi qarya, tun dama can da nake ce maku BANA KAUNARSHI wlh qarya nake, kawai dan ina tsantsar son yin karatu ne, ina ga kamar idan na yarda na auri Bomboy zai hana ni karatu na, sai yanxu nake ta faman da na sani, ina zagin kaina, yanzu da nasan banda mafita, saboda ya riga da yayi aurenshi"... Sosai nake kuka dan ba qaramin tausaya mn Mahida tayi ba, ta rasa abnda zata fadi sai runguma ta da tayi tana share min hawaye.

A hankali muke jin qarar taku kamar ana tafiya, ban dai daga kai na kalli masu tafiyan ba, saboda qarar tafiyar tafi karfin ta mutun daya, muryar dad mukaji yace "Assalamu Alaikum", "Wa Alaikumus salam" Mahida ta fada. Tuni na gama kidimewa dan a tunani na dad ya gama jin zancen da mukeyi. Ban gama kidimewa ba sai dana dago kaina naga jerin mutane sun qura mn ido cikin tausayi suna kallo na. Cikin dattako dad ya qaraso ya zauna kusa dani ya rungume ni, tsam nima na rungume shi hawaye na na sauka a jikin shi, yace "Wahida ina so ki sani qaddara ta riga fata, duk abnda kika ga ya faru to daman can Allah ya gama tsara shi. Ni nasan kina son Shahid ko dama, kawai dai rudin zamani ne yake dibarki da kuma son karatu da kikeyi. Zainab da kike gani yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, ina so ki sani zata dauke ki tamkar kanwarki ta jini, bazata taba yin kishi dake ba domin kuwa ni nasan halinta sosai saboda ni na hada aurensu da Shahid".

Zumbur na miqe tsaye cikin rashin fahimtar furucin dad, naji yana maganar Zainab bazata iya kishi dani ba, tunda niba matar Bomboy bace ba dama ya za'ayi tayi kishi dani? Ya akayi dad ya aurawa Ya Shahid mata ba tare da na sani ba?", Ban gama tunani ba naji dad yace "zauna duka zan baki ansar tambayoyinki", Ashe maganar zucin da nakeyi ta fito waje, zama nayi cikin son jin labarin na fuskanci Dad.

"Labari ne mai tsawo Wahida, tun kafin Shahid ya tafi Lagos ranar da yake shirin tafiyar, Small yake fada mn wai Shahid yana shirin tafiya kuma wai bazai dawo ba sai da mata, nayi baqin ciki sosai a lokacin da naje gidan har ya tafi, numbern wayarshi a kashe, sau uku ina neman wayarshi bai kunna ba, ganin haka yasa na rubuta mashi text kamar haka:

Assalamu Alaikum Son, Naji labarin tafiyarka a bakin Small, amma lokacin danazo gida har ka tafi, ina ta kiran numbernka kuma shiru, kuma kace bazaka dawo nan ba sai kayi aure, to ni kuma gaskiya kusan duk ban yarda da matan Lagos ba musamman na bariki, akwai wani abokina dake zaune Lagos da iyalinshi, yana da 'ya'ya duka 'yan mata, zan mashi magana sai ka zabi guda daya a ciki saboda yaranshI suna da tarbiyya, amma bazan mashi magana ba sai ka kirani dan in tabbatar da kaga text dina. BISSALAM.

Bayan kamar sati biyu naga kira da wata sabuwar number, na dauka nayi sallamh najI muryar Shahid, munyi magana sosai kuma ya amince da za6i na, yaje gidan amini na wato baban Zainab, ya za6i zainab saboda tafi duk sauran yaran hankali, ba'a dauki lokaci ba aka daura aure".

ABBA GANA AND

PRINCESS AMRAH

Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).