shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 April 2016

SAUYIN RAYUWA 20___25

sauyin-rayuwa.jpgsauyin-rayuwa.jpg

[9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 20 na BABY ZAHRA Dawowa tayi cikin nutsuwa, tasamu guri ta zauna, yana cin abincin sa yace kaisa tace na am yace kinsan me nake so da ke tace a'a yace inace kina son saurayin ki iron nan ko, cikin sauri tace mai eh, yace to nima ina da wata wanda nake so kuma ita nake son aura, kinsan me nake so da ke, tace a'a kisami abban ki kice masa ke bakya sona kina da wanda kike so, idan yaki ki masa kuka sosae kice masa ke bakya sona, saboda ke kinsan ni ba tsarar auranki bane, idan kikayimin haka to ni namiki alkawarin zan samawa iron kin aiki a jalingo inace kince yayi diploma tace ehh ya ce to zan Samar masa aiki a cen inyaso sai kuje cen ku zauna, tunda yafara maganar sa batace mai komai ba sae da tabari yakaraci zancen sa kafin tace mai, naji abinda kace ya muktar, amma kasani ni ina da tarbiyya kuma ina da biyayya don haka bazan iya samun abbana ba, ae Kaine babba don haka Kai kasami abban ka kagaya masa cewa baka sona, inyaki sai kamasa kuka kadaga masa hankali inyaso sai yace yafasa,da kake zancen soo kuma kai shaida ne ni bana son kamar yanda kaima baka sona, biyayya nayi nakarbe ka amatsayin kaddara, sannan kuma bakayi karya ba da kace ni ba tsarar auren ka bace saboda ni miji mai addini nake nema nagari wanda yasan mutuncin 'ya mace da kimarta, wanda yake biyayya wa iyayen sa,don haka ni ban damu da namiji dan boko ko wayayye ba, da kake zancen zaka samawa iro aiki ce maka akayi baya aiki ko mai, a hakan da ka ganshi yana da arzikin da zai ciyar dani ya tufatar da ni, alhamdulillah a hakan nake son shi kuma inza abarni zan aure shi, amma ni banna son kyalkyal banza, kuma ni inda zaka je kasami su abba da maganar nan da ka taimake ni ba kadan ba, domin nima banna son ka biyayya zanyi, kaga tafiya ta BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 21 na BABY ZAHRA Poster kawai yayi yasake baki yana kallon kaisa, wai wannan yarinyar dama tana da baki ashe har zata iya duban tsabaragen idon sa tace zata gaya mai irin wa ennan magan ganun lalle agaishe da ita, ko da shike ba laifin ta bane laifi nane da nasake mata hartake gayamin irin wa ennan magan ganun, daga yau na daina sake mata fuska, wata kakkaurar ajiyar zuciya yayi yadan kishingide akan gadon, wayar sa ce ta hau ruri da baiso dagawa ba, sai ya duba yagani ashe momy ce da sauri yadaga ,tace mai kai muktar kar kayiwa kaisa maganar nan, ashe abban ka yaji abinda nagaya naka har yayi mummunar fushi da ni, da sauri yace ae nikam harna gaya mata ma ae momy, cikin daga murya momy tace shikenan ka kashe ni, me tace maka yace bata yarda ba tace bazata fada ba, zagina ma tayi, tayi gaba abinta, momy tace to alhamdulillah, gwanda da tamaka hakan, da sauri yace gwanda da tamin haka kuma momy, momy tace iyyi gwanda ta maka hakan, ina ce ba marinka tayi ba, yace ehh tace to ai zagi baya tabo, yace momy nifa ban gane me kike nufi ba, momy tace bazaka gane ba kuwa kabari sai kadawo zamuyi magana, nidai abinda nake son ingaya maka dai yanzu kasan yanda za ayi ka lallaba kaisan kurabu lafiya, yace in lallabata fa kika ce mom, momy tace eh ka lalla bata, muktar yace gsky momy bazan iya ba, cikin fada momy tace sannu muktar wato har kayi girman da ina fada kana fada ko, to bari ingaya maka wata abinda baka sani ba, shine aure na yana shirin mutuwa akan auren ka da kaisa, in anyi in zauna in ba ayi ba inyi garin mu!!! BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 22 na BABY ZAHRA Gaban sane yayi mummunar faduwa yace momy bangane ba, tace eh haka dai ubanka yace, salati yasake yace momy ki kwantar da hankalinki insha Allahu za ayi auren nan, ae wannan ma abu ne mai sauki don dai aure kawai, momy tace to in akayi ka ceci aure na in kuwa ba a yi ba kai kayi sanadiyar aure na, noo momy baza ayi hakabama insha Allahu, kashe wayar ta tayi domin kwana biyun nan hankalinta baya jikin ta, bakaramin tashi hankalin muktar yayi ba da jin wannan maganar, yanzu ashe abin haryakai haka da har abba zai furta irin wannan mummunar kalmar akan momyn su zazzafar ajiyar zuciya yayi, ya mai da kansa kan filo ya kishin gide ya shiga kogin tunani kala kala. Kuka takeyi sharshar da hawayen ta, tadaga manyan idanuwar ta tace fulani gsky ni bazan iya rabuwa da muktar ba yaza ayi don kawai yace zai aure mu mu biyu shikenan kuma sai kice ae baya sona ne, wlhy ni ina da yakinin muktar yana sona yanda bakya zato, shima dai abin yafi karfin shine babu yanda ya iya shiyasa ya karbi yarinyar a matsayin kaddara, dalla rufemin baki! cikin tsawa fulani ta ke maganan daya ke bakisan mutuncin kanki ba shiyasa kike furta irin wanna kalaman daga bakin ki BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 23 na BABAY ZAHRA Kuka nasreen tasake sosae kamar ranta zai fita, fulani ce cikin tsawa tace tashi ki fitamin adaki ko in ci ubanki! da sauri nasreen ta tashi tafita gefen ta ta wuce cikin sauri, kan gado tafada ruf da ciki tana ta kuka mai tsuma rai, kuyan gunta ne suka tsaya tsuru tsuru suna kallon junan su anrasa wanda zai shiga uwar dakin ta ya rarrashe ta, falmata ne tayi karfin halin shiga dakin kasancewar itace amintacciyar kuyangan ta, a hankali ta karaso inda take tare da cewa ranki shidade gimbiya lafiya kuwa, da sauri nasreen ta tashi tace falmata fulani tana son ta rabani da muktar intarabani da shi bansan inda zan saka rayuwa ta ba wai don kawai zai aure mu mubiyu ni kuma nace ehh na yarda amma wai fulani bata yarda ba cikin kuka take maganar, dasauri falmata ta zauna bakin gadon ta tallafo kafadar nasreen tace ranki shidade insha Allahu baza ayi haka ba, ki kwantar da hankalin ki nasan yanda za ayi hajiya ta yarda, da sauri nasreen tace kamar yaya falmata, kasancewar falmata itace mai bawa nasreen shawara kuma bata taba bin shawarar ta taga ba dai dai ba don haka tana gab dajin tabakin falmata, falmata ce tace hadin kanki kawai zaki ban, domin nan da kwana biyu zanje incewa hajiya baki da lafiya, ke kuma sai ki kira Dr adam ku dai dai ta dashi inyaso sae muyi karyar zaki kamu da ciwon zuciya in har ba abaki wanda kike so ba, nasan hajiya najin hakan zata amince BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 24 na BABY ZAHRA Daddadar ajiyar zuciya tayi, ta rungume falmata abinda yasa take son ta kenan saboda akwai ta da bawa mutum shawara nan da nan, tace to yanzu abinda za ayi ko bari inkira Dr adam in yanzu sai in tsara masa yanda za ayi, wayar ta falmata ta miko mata tasaka hannu ta karba ta daddan na numbers in shi ringing biyu yayi ya dauka, bayan sun gama gaisawa ne ta karanto masa abinda ke faruwa da kuma wanda take da bukatar yayi mata, baiyi wata wata ba ya amince kasancewar shine family Dr su kuma sunyi da shi akan duk kudin da akabayar na magani yarike an bashi, bakaramin murna yayiba da jin wannan zancen, don haka sun bar abin zuwa jibi... Acen jajere kuwa muktar duk ya zaku gobe yayi saboda a gobene yake son komawa abuja, daga bakin kogi yake yana tafiya a hankali cikin kasaeta da nuna kamar hanyar na gidan sune, daga cen ya hango ta suna ta hira harda da dariya, da saurin sa ya iso inda take cikin tsawa yace mata ke wai bakya jin magana ne, ke wai mara hankalin inane, jikin kaisa ne ya hau rawa tace wlhy yaya inagaya masa ne kar yasake kulani donni yanzu anmin miji, yace dallah rufemin baki shine naga har da dariya, zaki wuce ki ban gurine ko sai na wanka miki mari, da gudun ta ta wuce tayi hanyar gida, juyawa yayi cikin bacin rai yace kai idan nasake ganinka da yarinyar nan sainayi mugun bata maka rai wlhy, IRO baice mai komai ba yayi gaba kawai abinsa, tsaki muktar yayi tare da cewa kazami kawai, sannan yasaka kansa gaba ya nufi hanyar gida BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 25 na BABY ZAHRA Yana shiga ya tura nana tayi masa kiran ta, da sallamar ta tashigo jiki a sanyaye saboda tasan me ta aikata,tsoronta daya ma shine kar ya gaya wa abban ta, tana shigowa tanemi guri ta zauna tace yaya gani, ko uhumm bai ce mata ba balle har ya kula ta, suna zaune a hakan sai da sukayi kusan 30mnt tun tana zaune akan kafarta harta gaji tanemi guri ta zauna, kaiii cen dai har ranta yafara baci, kuma ba abinda yafi bata mata rai kamar ko ya daga ido ya kalle ta yanata daddana wayar sa, ranta ya kai kololuwa gurin baci, a fusace ta tashi zata fita, da sauri yace inkin fita ki kawomin abinci, kuttt lalle agaishe da ya muktar wato daman bawani abu bane yasa yayi kiranta ya kirata ne don yayi mata rashin mutuncin shi daya saba, shiru tayi ko ta amsa, takama hanya ta fita, ceen dai yaune gobe ne ba kaisa babu dalilin kaisa yana zaune agurin yana zaman jiran dawowar ta amma yaji shiruu, yana zaune agurin tsawon 40mnt kafin sai ga nana takawo masa abincin, ranshi idan yakai million to ya bace, cikin tsawa yace wa nana kee ina kaisan take, da sauri tace tana cikin gida, yace ki mayar mata da abincin kice mata ta kawomin ita da kanta, da sauri nana tajuya ciki, ranshi yagama baci harya kullatawa zuciyarshi cewa tana zuwa sai ya wanka mata mari saboda shi ba sa anta bane, sai kuma wata zuciyar tace kai fa kafara mata hakan inda baka mata ba, da itama bazata maka ba, kan gadon ya buga wai meye yake faruwa da nine nasakewa yarinyar nan dayawa duk wata hanya da zata sa ta rainani nariga da nabi wannan hanyar, kuma ko ya kirata daniyar yi mata fada amma sai ya gagara tana da kwarjini sosae a idon sa..... Sallamar ta ce ya katse mai tunanin sa BABY ZAHRA

Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).