shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 11 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 46

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA

46

MUHD-ABBA~GANA DA AMRAH

A daren ranar haka na kwana jiki babu qwarie, ko baccin kirki ban samu nayi ba, da zarar bacci ya daukeni sai in tuno da abnda idona ya gane min, dakuma abnda kunne na yajiye min. Tabbas na cuci rayuwata, na yaudari kaina, idan masoya sukaji labarina na tabbatar da zasu shekara dubu suna tsine mun. Washe garie tunda safe na shirya cikin riga da skirt na atamfa mai manyan flowers red, hijab na dauko shima red madaidaici na saka, na jawo flat shoes suma red ina qoqarin sakawa mom ta shigo dakin mu tace "Wahida wai me kike ne da har yanxu baki fito break fast ba?" Nace "mom am ok fa" "Kamarya kin qoshi? Me kika ci tunda safen nan", "Mom banci komai ba, kawai dai bana jin yunwa ne", Karki 6oye mn komai Wahida, nasan dole akwai abnda yasa kika qoshi", Neman wuri tayi ta zauna tukuna tace dani "Wahida! Ya kamata ki fada mn damuwarki, kinga dai ni mamanku ce, baki da wacce tafini idan kuma akwai sai inji", Kai kawai na gyda mata alamar "a'a", Batace komau ba ta fice daga dakin nabita a baya ina fadin "mom na tafi skul", A parlour na samesu da Dad yana braekfast yace "auta har anyi shirin skul din kenan?", "Ehh dad na fito ken...", ban gama maganar ba naji sallamah, na dago kaina ina shirin ansa sallamar, wa zan gani? Bom boy ne tafe bayanshi da wannan mummunar matar rashi mai zubin kilaki, da qyar na iya ansa sallamar, dad fuskarshi da annuri yace "aahhh mutane lagosi sannu sannu, yaushe a garin?", Bom boy yace "wlh dad yau kwanan mu uku kenan", Mom ta 6ata rai tace "au yau har kwananku uku amma sau yau zakazo mana? Munyi fushi a koma", "A'ah mim ayi mana afuwa, wlh mun dawi a gajiye ne, jiya kuma munje gidan Mahida ne daga can muka wuce gidan farouk, daman dan mu kankare laifin mu ne yasa nace mata muyi sammakin zuwa yau, sai dare mu tafi", Dad yace "tou sannunku da hanya, amaryarmu an same mu lafiya?", Cikin kisisina tace "lafiya qalay dad" har qasa ta duwa tace "Gud morning ma'am", "Morning too dear, ya mutanen gida ya baqunta?", "Alhamdulillah mom", Sai a lokacin Bomboy ya kalle ni yace "sister Waheeda ina kwana?" Mom tace "yanzu ke wahida bakiji kunya ba? Ace yayanki shine zai gaishe ki?", Nace "mom banfa ganshi bane", fita nayI ko bankwana ban masu ba, zuciyata cike da qunci da nadama, a raina ina fadin "ashe sama su dad sun san Shahid zayyi aure shine suka qi su fada mun?" Dan guntun tsaki nayi nace "tou kuma ai bai zama dole su fada mn ba, tinda sun san BANA KAUNARSHI, da wanann tunanin naja mota ta na kama hanyar skul.

ABBA GANA

AND

PRINCESS AMRAH

Share:

11 comments:

  1. IMAM IBNKATHEER ZULQARNAYN11 April 2016 at 08:09

    Super brozs......muje xuwa,muna biye da kai

    ReplyDelete
  2. IMAM IBNKATHEER ZULQARNAYN11 April 2016 at 08:13

    Super brozs.........muje xuwa

    ReplyDelete
  3. IMAM IBNKATHEER ZULQARNAYN11 April 2016 at 08:13

    Super brozs......muje xuwa,muna biye da kai

    ReplyDelete
  4. gaskiya hoton nan nake so

    ReplyDelete
  5. ayya plss abba a dan kara yawan posting nan in da hali. tnx

    ReplyDelete
  6. abbagana (admin)12 April 2016 at 12:53

    hoton gaskiya sai ta whatsapp

    ReplyDelete
  7. abbagana(admin)12 April 2016 at 12:53

    insha Allahu za,a kara

    ReplyDelete
  8. Allah bar mana kai

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).