shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SAUYIN RAYUWA 46___50

sauyin-rayuwa.jpg

[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 46 na BABY ZAHRA
Misalin karfe 11:00am dai dai aka daura auren MUKTAR USMAN SHEHU JAJERE, da amaryar sa NASREEN MUHAMMAD LAMIDO, ran asabar wanda yakama 03/01/2051 akan sadaki naira #500k, yau dai burin nasreen dai ya cika,tanata rawar kai a cikin gidan yau za akaita gidan angonta,masoyin ta,abin alfaharin ta,rungumar filo tayi da sauri ta kwanta rigin gine ,idon ta yana kallon silin, muktar shi da kanshi ya koma jajere don dakko kaisa, tunda suka dakko hanya ba wanda yacewa kowa ci kanka, sai tsula gudu kawai yakeyi akan hanya, ceeen dai yadan saci kallon ta ta gefen ido, tasha kwalliya tayi kyau kuwa sosai sai wasa takeyi da en yatsunta da suka sha kunshi mai kyau, tayi kyau fa yafadi hakan a ransa, suka cigaba da gudu har suka iso, wani gida suka dosa sai da suka iso yace mata fito, a hankali ta fito tabi bayan sa knocking yayi abakin kofar dakin, wata mata ce ta bude kofar suka shiga, tace a'a muktar kar dai wannan ce dayan amaryar tamu, murmushi yayi yace eh itace, ta kamoni tace sannun ki da zuwa fa, murmushi nayi bance mata komai ba sannan na nemi guri na zauna, daki ta shiga sai gata da mijin ta, yace ya abokina har kun iso, ehh kawai muktar yace masa, sannan yace bari in dakko nasreen ko ina zuwa, yace masa too,
Ceen kamar bayan 30mnt saiga shi ya dawo ce min yayi tashi muje, cikin nutsuwa na tashi, nabi bayan sa,har kofar gidan matar ta rakomu, bayan na bude nashiga, sannan itama ta tashi daga gaban ta dawo baya, muktar ne ya shiga gurin zaman ta while abokin sa kuma ya shiga mazaunin direba, yaja muka tafi, a hankali nace mata ina wuni, sai da ta kalleni sosae sannan ta iya budan baki cikin yatsina tace min kalau
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 47 na BABY ZAHRA
Har muka isa airport ba wanda yakuma ma wani magana, kaina yana kan waya ta ina game in candy crush, muna zaune muna jira a kira mu, a tsakiya muka saka shi sai tadin su sukeyi shi da nasreen, tana kwance a kan kafadar sa, ni kuwa sai game ina nake tayi, duk a tsarge ma nake sakamakon kallon da wani a ake ta mun gsky na tsargu da yawa,duk na bi na matsu ma muyi mu tashi, ceen kuwa sai aka fara kiran mu... Munjeru cikin layi muna shiga jirgin, kowa kan numbern site insa ya nufa, nasreen da muktar tare suka zauna while ni kuma site ina yana ta gefen nasu muna facing in juna, ji nayi ana cemin barka dai hajiya, najuya gefena wa zan gani wannan matashin ne da ya isheni da kallon nan, bance masa komai ba yanata min magana amma nayi shiru, hankalia duk yabi yatashi duk da A/C da ke cikin jirgin amma ni zufa nake hadawa sakamakon wani mugun kallon danaga muktar yana min, magana nasreen ta ke masa amma ina hankalin sa yayi nisa gurin kallon mu nida mutumin nan, shiru nayi tayi har Allah yasa jirgin mu tasauka lafiya, nan da nan jikina yakama bari sakamakon bina danaga mutumin nayi, sae da muka isa dai dai gurin motar dazamu shiga ne, muktar yatare mutumin da cewa malam lafiya kam ko, murmushi matashin yayi ya mika masa hannu da sunan suyi musabaha amma ina kememe muktar yaki yabada hannun sa, sae ma ce masa da yayi cikin tsawa kai tambayar ka fa nake lafiya, cikin nutsuwa yace wlhy lafiya kalau sai alkhairi, wlhy naga kanwar kace kuma ina so, wlhy in za aban ita ina so kuma da aure, amma tun dazu nake mata magana taki kulani, wani mummunar harara muktar yasake masa, sannan yace ce maka akayi tallar ta akeyi ne ko meye, to mata nane ita ko da magana ne, cikin sauri saurayin nan yace a'a ba magana, amma in kana son ka hanani ita ba sai ka dangan ta ta da matar ka bama in kace min baka sona ba shikenan ba.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 48 na BABY ZAHRA
Ya wuce yayi tafiyar sa abinsa, ran muktar in yayi millions to duk ya bace, da karfi yabude gabar motar ya buga ta da karfi, drivern sune yace Allah ya huci zuciyar ka yallabai ko uhumm baice masa ba, haka zalika ran nasreen ma ya baci sosae akan meye muktar zai gwada kishin sa akan yarinyar da yace baya so, kodai muktar karya yayi min dai, dukka motar kowa ranshi a bace haka suka iso gidan, hannu bibbiyu aka tarbesu nasreen tayi dakin momy kaisa kuma tayi dakin aunty rukky, sai misalin karfe 4:30 kafin sauran suka iso a gajiye, en uwan nasreen aka sauke su a masaukin su, en uwan kaisa ma aka sauke su anasu masaukin
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 49 na BABY ZAHRA
Misalin karfe 8:00pm kowa ya shirya don zuwa gurin DEENA, har an fara tafiya da wasu ma gurin, masu kwalliya aka dibowa amaren, muktar ne ya kawo kayan da zasu saka, kasancewar shi ya hada dinar, fess sukayi kamar basu ba, sai da kowa yagama tafiya kafin aka umurci amaren da su fito su tafi, amota suka hadu, shine a tsakiyar su, suka tafi, suna isa bakin hall in motar ta tsaya, suka fito daya bayan daya, nasreen bata tashi ankaran ashe kaya iri daya suka saka da kaisa ba sai da hasken wutan filin ya haska su, tana gani taji kamar tayi hauka don kishi mai muktar yake nufi dayakama yayi musu kaya iri daya da wannan bakauyiyar yarinyar, haushi ne ya rufe ta, amma ba yanda ta iya haka nan dai suka jera zuwa ciki, kujeru uku aka saka musu shi yasha kayan ado, a tsaki ya suka sakashi, bakaramin kyau sukayi ba, anci ansha sannan aka cashe, misalin karfe 1:00am sannan suka gama aka kwashi kowa aka mai da shi gida, sannan amare da angon su suma suka tafi, suna isa kaisa ce tafara bude motar don ganin yanda nasreen take shishshi gewa jikin muktar duk sai kunya takama kaisa shiyasa ma tayi ta Allah Allah su samu su iso gida don ita bata taba ganin irin wannan al'amarin ba.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 50 na BABY ZAHRA
Agajiye ta shige dakin su saboda tagaji ba kadan ba, kwanciya tayi da niyar yin bacci amma sai mee?, abinda yafaru tsakanin nasreen da muktar ne yafado mata nan da nan taji bacin rai yakamata tarasa meyeke mata dadi a wannan daren, ceen kuma sai wata zuciyar tace mata to ke bacin ranki akan me, bayan ba sonshi kikeyi ba, in ma sunyi ba masoya bane su ke kuma naki a wanne, tsaki tayi da karfi wanda har sai dayajawo hankalin mutanen dakin kowa yajuyo yana kallanta, rakiya ce tace kawata lafiya kuwa, kada manyan idanuwarta tayi, tayi wani yarrr da su, tadan yatsina fuska tace wlhy kaina ke ciwo, daya daga cikin en dakin ne tace bari in baki panadol, cewa tayi a'a kibarshi kawai ban son shan magani bacci kawai nake bukata, tadan gyara kwanciyar ta, amma ina bacci yaki zuwa mata tunanin muktar ne kawai yake zuwa mata, sai tsaki takeyi acikin ranta

Juyi yakeyi kawai agado amma bacci yaki zuwa masa, yarasa meyasa yanzu daga zaran yasaka kansa akan filo da sunan bacci amma sai ya gagara, in banda tunanin kaisa ba abinda yakeyi, yarasa dalilin wannan abu ga wacce yakamata yayi tunanin ta amma bayayi saina kaisa, tsaki yayi yadan gyara kwanciya, ko zai dan samu bacci yazo masa amma sai mee? tunanin ta yacigaba tun bayajin dadin tunanin har yafara ji, nan da nan yaji ransa tana son ganin ta, wayar sa ya dakko ya dialing numbern ta, ceen kuma kome ya tuna sai kuma ya fasa yayi tsaki yayi cilli da wayar gefe.......haka dai tsakanin kaisa da muktar bawanda ya rintsa har saida akayi kiran sallar farko kafin shaidan yazo yarufe su da babbar bargo, bacci mai dadi ya dauke su.
BABY ZAHRA
Share:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).