shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 April 2016

SAUYIN RAYUWA 9 & 10

sauyin-rayuwa.jpg

SAUYIN RAYUWA 9

Gaban muktar ne yayi mummunar fadi ALKAWARI? Yafadi azuciyar sa, dai dai lokacin da abban jajere yakatse mai tunani da cewa eh nasani ae yaya amma ae namiji mijin mata hudu ne kuma ae kaisa zabin mune don haka shima sae mubarsa yayi zabinsa! KAISA dasauri yafadi sunan acikin ransa nan da nan yaji gaban sa yana fadi zufane ya hau karyo masa babu kama hannun yaro, abban abuja ne yace to ohon masa donni kam bazan je wani gidan sarauta ba, abban jajere ne ya umurci muktar da yaje cikin gida, jiki sanyaye yatashi yafice waje yabarsu acikin zaure, cikin mota yakoma yadan kwanta, KAISA KAISA sunan da yaketa nanatawa kenan acikin ransa yanzu daman ashe abinda yasa abban shi baya son yake kawo masa maganan budurwa kenan kullum yace mai ba yanzu ba, daman ashe da wannan jakar yarinyar yake son hadani, to gsky bazai yuyu ba zanyi iya bakin kokari na don ganin an rushe wannan auren, kamar niii ace yanda nake in nan ne za a aura min wata bakauyiyar yarinya buga kan starring motar yayi da karfi yace kai gsky bazai yuyu ba..., acen kuwa abban abuja ne ke cewa abban jajere kasan Allah kwanan nan zan bijiro da zancen auran nan don naga wannan yaron zai iya yimana shashan ci, abban jajere ne yace mai haba yaya adai bi abin a hankali yaya, yanzu abinda za ayi goben sai mu shirya muje jalingo sai muji zancen ita wancen in! Wa inje ina cewar abban abuja ba inda zani, abban jajere ne yace yaya kar ayi haka yakamata muje dai muji..... Ahakan Abban jajere yayi ta lallashin yayan sa harya yarda akan eh zasuje amma da sharadin za akira muktar in ya yarda zai aure su su biyu rana daya in kuma bai yarda ba to sai ya san wanda zaije mai neman auren kuma kai ma ban yarda kaje ba, a hankali abban jajere yace to shi kenan anai mo shi, abban jajere ne ya leka ya kwalla mai kira yafito da sauri har yana tun tube, zaunawa yayi kusa da abban jajere yace abba gani, abban abuja ne yace to na yarda za aje ayi maka tambayar ita yarinyar amma da sharadin zaka hada su ita da KAISA ka aura, gabansa ne yayi mummunar faduwa BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 10 na

BABY ZAHRA Gaban sane yayi mummunar faduwa, cikin sauri yace in hada su kuma abba cikin tsawa yace masa ehhh in kuwa baza ka hada su ba to kahakura da su dukka sannan kuma ka hakura da yin aure gaba daya, zufane tacigaba da kyetowa muktar ba kakkautawa, jikinshi har rawa takeyi, yanzu dawata kallama zan samu nasreen ingaya mata cewa su biyu zan aura, kai ina nasan bazata yarda ba, to yanzu in bata yarda ba yazanyi da abba, abba ne ya katse mai tunani da cewa kaiii kaifa muke jira ka tsaya kayi shiru sae zuru zuru kake da ido, abban jajere ne yatari numfashin shi da cewa yaron abba ko dai abaka lokacine, cikin sauri yace eh abba, abban abuja ne yace a'a babu lokacin da za a bashi kawai inya ga bazai iya ba to ya hakura da su dukka, cikin sauri muktar yace a'a abba to...to....to... Ita kaisan tana sona ne, abba ne yatare numfashin shi dacewa ina ruwan ka intana son ka kobata son ka, kai dai ka ammince mana ae zaku fahimci juna kafin ayi auren, muktar yace to shikenan abba na amince daddadar murmushi abban shi yasake wanda har sai da hakoran sa suka baiyana, lalle Abba nason auren nan, nan da nan har fushin shi ya sauya dariya, gsky nikam na amunce da auren nan ne ba don ina so ba sai don ina matukar tsoron abba na don bashi da dadi tagurin abinda ya kwallafa rai akai don zai iya bata min sosae akan wannan ganar amma ba komae bari mukoma gida zan samu momy na in gaya mata za asan yanda za ayi a wargaza zancen auren nan,( cewar muktar acikin zuciyar shi) abba ne ya katse mai tunani da cewa to tashi maza kashiga cikin gida ka kwanta kayi bacci dare yafarayi ko, too kawai iya ce mai, yatashi cikin nutsuwa yashige ciki

Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).