shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SAUYIN RAYUWA 61___65

sauyin-rayuwa.jpg

[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 61 na BABY ZAHRA
Yakai kusan 15mnt yana knocking kafin tazo ta bude, tsaya wa tayi abakin kofar tarike kofar tana mai wani irin kallo irin na tsoffin bariki, kusan 5mnt tana haka sannan tace mai antashi lafiya, bata ji ra amsar saba ta juya ciki, yana binta a baya kitchen ta nufa tacigaba da abinda takeyi, cikin tsarguwa da tashin hankali yace mata kaisa don Allah kiyi hakuri da abinda na miki wlhy ba sona bane kuma nasan ban kyauta ba........har ya karaci maganar sa bata ce mai komai ba, indomie take dafawa harta gama ta juyeshi a plate bata amsa masa ba, bata ma juya ba balle tasan meyake fada, tana gamawa fitowa tayi dakinta ta nufa, yazo zai shigo kenan ta bugo kofar tasaka key, ta zauna taci abincin ta cikin kwanciyar hankali, tana gamawa ne, ta kira rukky kobi ta fada mata yanda sukayi, dariya suka sheke da shi rukky kobi tace ki kwantar da hankalin qawata, kar kiyi mai komai a hakan zaki gara shi, kuma karkice zaki ki yimasa magana fa, kina masa amma banda dariya, too qawata karki damu cewar kaisa, bakiga yanda yadamu bama yanzu, rukky kobi tace ae haka ake musu a hukuntasu ta cikin kasa, sake shekewa sukayi da dariya, sannan sukayi sallama, suka kashe wayar
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 62 na BABY ZAHRA
Misalin karfe 12:00pm na rana ne tafito ta daura abincin rana, tana gamawa sai gashi nan yashigo, dakko mai tayi tazo ta ajiye mai agaban sa ta zuzzuba mai, har yana murna ya dauka ta sakko ne, fuskar ta dai ba yabo ba fallasa har tagama mai, tana zaune agurin yana cii yana yimata magana, in magar ehh tace ehh in kuma na a'a tace a'a, shidai har yagama bai gane mata ba, yana gamawa takwashe ta kai kitchen, zata wuce daki yace mata kaisa zonan inason magana da ke, dawowa tayi batare da tace komai ba, ta dawo ta zauna, a kasa, don wannan al'adar kaisa ce, in har yana kujera to ita tana kasa, yace mata a'a tashi ki hau kujera tace mai a'a inajinka daga nan ma ba sai nahau ba, daga kafada yayi alamar bai damu ba, saboda yasaba da irin wa ennan halayen kaisa, yace mata kaisa, shiru tayi bata amsa ba, yasake cewa kaisa, nan ma shirun tayi, sai da yafadi baki uku sannan tace na am ya muktar, ajiyan zuciya yayi sannan yace mata kaisa nasan inna fada miki abinda ke zuciya ta ba zaki yarda ba ko.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 63 na BABY ZAHRA
Shiru ne yaratsa falon na dan wani lokaci sannan yace da farko dai nasan namiki laifi kaisa, amma don Allah ina mai baki hakuri akan abinda namiki, nan ma shirun tayi sannan yace mata kinyi shiru kuma kaisa, yarrr tayi da manyar idanun ta tawani kadasu sama, sannan tace ni babu abinda kamin balle kabani hakuri, shiru yayi yana kallon ta, sannan yace kikace ba abinda na miki, daga mai kai tayi alamar ehh, sannan tace ni bansan akan me kake bani hakuri ba, cikin jin kunya yace ina baki hakuri ne akan daukar kwanan ki danayi nakaiwa er uwarki, kallon shi tayi cikin mamaki, sannan tace to ai ba laifin ka bane, kasan abinda zuciya bata so koma maye zata iya aikatawa akai, cikin hanzari ya sakko kasa inda take zaune yakamo hannuwar ta yarike su gam acikin nasa, sannan yace wallahi tallahi INA SONKI KAISA, ina SON KI har cikin ZUCIYATA, bantaba sanin me ake kira so ba sai akan ki, sai yanzu na lura ashe shirme mukeyi da nasreen ba soyayya ba, sai akan ki nasan me masoyi yake ji aransa akan masoyoyar sa, kaisa don Allah ki taimaka KI SONI koda kwatan kwacin wanda nake miki ne.......kamar saukar ARADU kaisa taji kalaman muktar, nan da nan zuciyarta ta karyata mata abinda yake fada.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 64 na BABY ZAHRA
Cikin hanzari tace ya muktar indai don abinda kamin ne kake so kamin karyar kana sona, ni nayafe maka, amma bana son kana karya donni banna ganin mutuncin mutum mai karya, kaga kuma ni ina ganin girman ka, bai kamata ace kamin karya don in yafe maka abinda kamin ba, kum.....hannu yasaka yatoshe bakinta cikin hanzari, yace kaisa me zan miki don kigane ina tsananin sonki, kaisa ke kalli cikin kwayan idona zaki gane da gske nake, kaisa ko sai na dakko al Qur'ani na rantse miki kafin zaki yarda, mikewa yayi cikin hanzari zai dakko Qur'ani, rike hannun shi tayi cikin hanzari tace ya muktar ba sai ka dafa Qur'ani ba na yarda da kai baka karya ya muktar kakan fadi abinda ke ranka ne, kuka ne ya kwubce mata mai tsuma ran masoya tace daman ashe akwai ranan da zaka budi baki kace kana sona, dawowa yayi ya fuskanceta yasaka hannu yashare mata hawayen ta, sannan ya rungume ta yace kiyi shiru matata, na dade da sonki a raina, amma ban yarda ba, saboda inaganin kamar zuciya ta karya take min, sae da naga sonki zai kasheni kafin na yarda ashe da gske sonki nake, yace kitaimaka kice kina sona don Allah, cikin kwanciyar hankali tace ina sonka yayana! yayana ina sonka!! wani dadine yarufe muktar yadada matseta ajikin sa.........ji sukayi ana cewa to maci amana namiji kudan Zuma inbai kasheka ba zai saka ka jinya, ashe akwai randa zakaci amanata muktar ashe duk irin alkawarin da ka dade kana dauka min na karya ne......
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 65 na BABY ZAHRA
Sake junan su sukayi cikin razana, mikewa yayi a fusace yace ke wai wata irin mahaukaciyace, ko kin mance yanda kike matata itama haka take, kuma in daa na dau miki alkawari to yanzu na karya, kuma ki wuce kifita ke ban guri, kuka nasreen tasaka sosae kamar wacce akama rasuwa, tafadi tanata shure shure, a hankali kaisa ta matso inda take takama hannun ta tace haba aunty nasreen don Allah kisakawa zuciyar ki ruwan sanyi, ni ba abokiyar gaban ki bace, kiyi addu'ar Allah yarabaki da mugun kishi, bashi da amfani, ki tsaya kiyi tunani muhada kai mu zauna lafiya....fisge hannun ta tayi tace dalla cen sakeni makira, in banda makirci ba abinda kika iyayi, tsaki taja sannan ta juya takalli muktar tace mai kai kuma ina jiran takardata, don yau zankoma garin mu, sannan ta wuce tatafi gida, tana fita ya dauki waya yakira numbern baba waziri, bayan sun gaisa ne cikin girmamawa sannan yakaranto masa abinda ke tafiya a gidan sa, baba waziri yaji haushin maganar bana kadan ba, sannan daga bisani yabawa muktar in hakuri, akan zai kira nasreen in

Fada sosae baba waziri yayi wa nasreen sannan daga bisani yayi mata wa'azi mai ratsa jiki, bai kyaleta ba har sai da ya fahimci jikinta yayi sanyi, sannan daga karshe ya umurce ta dataje tabawa mijin ta da abokiyar zamanta hakuri...bai kashe wayar ba har saida ta masa alkawarin zataje tabada hakuri sannan kuma tayi alkawarin irin haka bazai kuma faruwa ba, albarka yayi ta sakamata sannan ya yakashe wayar, kukane ya kwubce mata tayi kuka iya isarta, sannan ta yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi, tashiga toilet ta wanke fuskarta sannan tafito tashafa mai tadan murza powder har da wetleaps sannan ta yafa gyalenta tafito.
BABY ZAHRA DAN ALLAH IN AN KARAN TA ANA AJIYE COMMMENT
Share:

8 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).