shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 1 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 43&44

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNAR KA!!!

43&44

MUHD-ABBA~GANA 09039016969

--------------------------------------------

wallahi ina muku kallon sani sannan ina ji a jikina duk daga inda kuke ku jininmune amma meke tafe daku ya roki ya amin yace nanne gidan malam abdulkadir? tsohuwa tace nanne nanne gidan tsamiya? nanne ke kuma sunanki inna furera? ta amsa ya ce yayanku nawa ko baku taba haihuwa bane? tsohuwa tace a to mun taba haihuwa shekara talatin da biyar kenan tai shiru tana matsar hawaye,ya amin ya ce ina dan da kuka haifa koya mutu? ai ba namiji bane mace ce sunanta maryam amma kasancewar yar farice muna kiranta inna wuro,gaba dayanmu muka lalli juna tsohuwa ta bamu labari kamar yadda yadda mon ta shaida mana na sanadiyar barin gidan mahida tace inna ki bar kuka domin maryam tana nan da ranta tsohuwa ta rike kai da gaske kin san maryam kin san inna wuro? nan ya amin ya bata labarin ita da dan tsoho kuka suka dinga yi gaskiya mun ga gata gun wadannan bayin Allah washe garri tun safe muka tarkato tsofaffinnan zuwa kano ta dabo. a gida kuwa hankalinsu abba in yai dubu ya tashi har katsina anje bama nan wannan ya kara daga hankalin iyayenmu har gidan rediyo talabijin kafafan yada labarai ansa cigiyarmu misalin karfe biyar muka iso tun kan muyi fakin aka baibaye mu kowa ka gani fuskarsa akwai alamar tambaya,kai tsaye dakin mom muka nufa Allah sarki mominmu hankalinta a tashe ta mike ta nufo mu Allah mom har ta rame daga ina kuke na nuna mata tsohuwa mom ta zubawa matar ido sai kuma ta fada jikinta kukan farin ciki suka dinga yi ni kuma dakin abba na shiga duk da ya samu labarin dawowarmu nan na shaida masa gaskiya su abba sun taya mom farin ciki ganin iyayenta,mom farin ciki kamar ta goya mu tayi ta sa mana albarka.zaune nake anmin kunshi su ya amin anci uwar kwalliya shida abokansu sai faman shige da fice suke yi kasancewar yau ne daurin aure,ya shiga ya tsugunnna gabana yana kallona nai dariya yaya kamar kaine angon? yace wahida kamar kece amaryar na taba baki kawai na yi shiru yace wai me dame dame kuka shirya nace ai komai ma yaya mun shirya,yanzu so nake a gama samin rani inje in anso mana dinkinmu,munyi da telan zai aiko min amma shiru yace ki bari zan anso miki amma kiyi zamanki.dan kar wahida ta san me ake ciki yasa aka daura auran a babban masallacin juma'a sai dai ita ko a jikinta,fati sun sha shi kalala sun rakashe sun case duk inda zaka ga mahida tana manne da mijinta yayinda wahida ta manne wa yayanta gwauro al'amin mamy ma tana jikin angonta faruq a ranar aka kai amare wahida sunyi kukan rabuwa ita da mahida an kai amare dakunansu sai dai ban da wahida domin baba rabiu yace a barta sai bomboy ya dawo.yau watan mahida uku a gidan miji yaune kuma na kai mata ziyara muka rungume juna hadda kukan farin ciki tare muka shiga kicin muka shirya komai bayan mun gama cin abinci muna zaune muna hira muka ji takun takalmi kwas kwas alamar za,a shigo aka turo kofar wata budurwace tai sallama ta shigo muka amsa ya shigo daga yanayin shigarsa dressing dinsa ko ba a fada ba kasan ko waye sanye yake da kayan sojoji ya turo kofar muka zubawa juna ido wani annuri ke fita a fuskarsa yayi kyau ainun,inalillahi ji nai sam bazan iya daina kallon kyakkyawar fuskar ba.

Abba gana hausa novels @ facebook.

www.abbagana.pun.bz

Share:

11 comments:

 1. acigaba mana

  ReplyDelete
 2. dan allah acigaba

  ReplyDelete
 3. IMAM IBNKATHEER ZULQARNAYN1 April 2016 at 14:58

  Dan Allah aci gava mana brosss!we really enjoy this story

  ReplyDelete
 4. Dan Allah Akarasa Mana Sireenah Kashi Na Uku Mana, Wallahi Littafin Yayi

  ReplyDelete
 5. Sannu Da Kokari Allah Ya Taimaka Acigaba

  ReplyDelete
 6. dan Allah aci gaba

  ReplyDelete
 7. Aisha abubakar7 April 2016 at 06:25

  sannu da kokari mun gode amma dan allah ka rikaturowa dayawa


  ReplyDelete
 8. pls acigaba

  ReplyDelete
 9. Ko dan roqon nan da ake tayi ai ya ci ace a qarasa lbrn. Ko dai mu haqura ne. Shirun yayi yawa Allah Ya sa dai lfy. Pls a aiko mana da ansa a comment. Mungode

  ReplyDelete
 10. abubuwanne sai a hankali ana karawa da hakuri

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).