shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 April 2016

SAUYIN RAYUWA 16__20

sauyin-rayuwa.jpg

[9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 16 na BABY ZAHRA Hakince suke a dakin baki,muktar da nasreen bansan wayafi wani iya mulki da sarauta ba, suna zaune sai zubawa junan su mulki sukeyi,kuma ahakan soyayya sukeyi sosae don har wani shagwaba nasreen ke wa muktar, cikin faduwar gaba muktar yace wa nasreen sweet kinsan kuwa da yaya abbana ya yarda yazo yamin tambayar ki, tadan gyara zama tace a'a sai kafada yace in gaya miki da kyar yazo , ko kinsan meyasa tace a'a saboda wai ya bani mata er kanin sa anan jajere, subhanallah cewar nasreen yabaka matafa kace cikin kasaita yace mata eh!!! Nasreen tace yanzu ya akayi kenan yahakura, yace mata waaa ae ba hakura yayi ba, sharadi ya gindaya min kafin yazo, tashi tayi sosae ta zauna daga kishingiden da tayi tace sharadin me kenan, cikin isa da mulki muktar yace cewa yayi sai dai in hadaku ku biyu dukka in aura arana daya!!! Zumburr tamike tsaye tace bangane ba muktar kana nufin tunkafin inshiga gidan ka harkamin kishiya, to kuwa bazai yuyu ba gsky ba zata taba sabuwa ba, er ni innan ace wai har anmin kishiya gsky inaaa, cikin nutsuwa muktar ya mike tsaye yace ashe daman bakya sona nasreen, saboda irin son da nake mikine fa yasa na karbi auren wancen yarinyar da bata dace dani ba, saboda abbana yace in har ban yarda da auren ta ba, to kema insakawa raina munrabu kenan, ko ance miki ni ina son ta ne, kenake so nasreen, nasreen ke nake so, jikin nasreen ne yayi sanyi tajuya ta kalli masoyin ta, tace nima ina sonka muktar amma bazan iya jurar ganin wata tana taraiya da kai ba, cikin muryar kuka ta furta maganar, nan da nan tasaki kukan da ke makoshinta, da sauri muktar yazo ya riketa yace ki kwantar da hankalinki nasreen ni nakine ke kadai, ko an aura min kaisa kisakawa ranki cewa ke kadai ce agurina, namiki alkawarin babu abinda zai shiga tsakanina da ita na aurataiya, wani daddadan sanyi ne ya ziyarci zuciyarta wanda har yasa bata san sanda ta rungumeshi kam ajikinta ba, kusan 15mnt suna haka, muktar ne yayi kokarin janyeta daga jikinsa, gudun karya shiga wani hali BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUW page 17 na BABY ZAHRA Dakyar suka rabu da juna, sun rabu akan zai sake dawowa, shi da kanshi ya koma da motar akan sai randa zai koma abuja zai dawo da ita, a hanya ne wayar momy ta shigo, a hankali ya dauka sallama yayi mata amma ko amsawa batayi ba ta haushi da fada, gefen titi yasamu yafaka motar don sauraren abinda mahaifiyarshi ke kunshe da shi....... Kana jina ko muktar yanzu ashe mani zaka watsawa kasa a ido karasa wacce zaka aura wai sai kaisa, kuma yaushe kafara neman kaisa a gidan nan ni ban sani ba, da har zakace wai zaka aure su su biyu kana hauka ne, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, sai da tamasa tatass yana shiru baice mata komai ba, sai da takai aya sannan yace to ni momy ninace miki ina neman kaisa, abba ne fa yace saina aure ta na dole nima naso inbijire masa shine yace to sai dai incire rai da auren ko wacce mace indai bazan auri kaisa ba, nima fa hakuri nayi na karbi ta, kuma yanzu haka ma daga gidan su nasreen in nafitoni kuma nagaya mata yanda abin yakasance kuma ta yarda za ayi auren haka, salati momy ta sake, atakaice dai kace min kayarda ka karbi auren kaisan kenan, to wlhy baka isa ba, muktar cikin tashin hankali yace to momy in banyar da ba yazanyi kenan kinga yanda ran abba yabaci ne sosae, tsawa momy yasake mai to ni ina ruwa na yabaci mana nidai yanzu kaji abinda zan gaya maka kasami kaisan kace mata tasami abban ta tace masa itafa bata son auren nan tadagawa abban ta hankali in yaso sai yagayawa abban ku sae susan yanda zasuyi, too kawai yace mata, kaaa sai kuma yaji wayar ta katse, yakira yakira bata daga ba, sai kawai ya hau hanya, acen kuwa momy na cikin kitsawa muktar abinda zaiyi sai kawai taga abba akanta harde da hannu da alamu yaji me take kitsawa...... BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 18 na BABY ZAHRA Dan sose sose ta fara na rashin gsky, sae da yakai 5mnt baice mata komai ba sannan daga bisani yace mata bazan hanaki abinda kika kin tsawa danki ba amma sai dai ina son kisani , duk randa akace an fasa auren kaisa da muktar to kisakawa ranki cewa kema zaman ki yakare agidan nan!!! Kamar saukar aradu taji saukar maganar, da sauri ta mike tsaye tace a'a alhj abin bai kai harga haka ba, indai zancen aure ne ko yauma a daura, bai tsaya sauraron ta ba yayi ficewar sa abin sa, zama tayi abakin gadon ta, wata zazzafar ajiyar zuciya momy ta sake, tace cab in alhj ya sakeni ina zan fara zuwa ae sai dai in koma kauyen mu, da sauri ta dakko wayar ta ta danna lambar muktar amma ina tayi tayi ya shiga yaki, tsaki taja tadan kwanta tafada kogin tunani Acen kuwa bayan ya isa yadan kwanta yana tunanin maganar momy shi, saiga nana er autar su kaisa tazo shigewa tagun dakin shi, ya kwalla mata kira ta shigo cikin sallama tace yaya gani yace yauwa goggona auntyn ki tana gida kuwa, ehh tace mai yace to tashi kije ki kiramin ita ko maza kice mata tazo ina neman ta, cikin sauri nana ta mike tana mai cewa too, adakin inna tasame tasuna hira da innar ta tashigo aunty wai kizo inji yaya muktar cewar nana, cikin faduwar gaba tace ni kuma yadawo ne ya muktar in tace mata eh yana dakin sa, inna ce tace tashi kije mana tunda kikaji ance miki kije inji shi kam ai kema kinsan yadawo kenan BABY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 19 na BABY ZAHRA Da sallama tashiga dakin a hankali ya amsa don itakam bataji mai yace ba ta dai ga bakinsa yayi motsi, tana zama yace ke waike bakisan yakamata bane nadawo tun dazu amma shine baki kawo min abinci ba balle ruwa, a hankali tace laaa ai yaya bansan ka dawo bane amma kayi hakuri bari in dakko maka, da sauri ta mike tashige cikin gida, al halin fa cikin sa a koshe yake kawai dai baya wuce abincin kaisa ne don koba komai yarinyar ta iya girki, yasan dadin dandanon abincin kaisane tun lokacin da take zuwa musu hutu abuja, idan har kaisa na gidan to bayacin abincin kowa inba nata ba, ya zame mata jiki itake mai girki kullum nashi daban ne bayacin na masu aiki, kuma yayi missing in girkinta sosae yayin da ta daina zuwa gidan su, saboda irin musguna mata da sukeyi agidan da shi da kanwar sa zahra da uwarsu momy, agurin hjy rukkaya kawai take hutawa kasan cewar tana mata matsayin goggo ne ita, sallamar tane ya katsemai tunanin da yake yi foodflacks ne na abinci da plat da spoon da ruwa a gora mai sanyi ta kawo masa ta jiye a gaban sa, ta bude jalof in shinkafa ne yaji kifi banda, nan da nan kamshin abincin ya mamaye dakin, har yawun muktar ya kada, tadan zuba mai ta kalleshi tace ya yi haka, kai kawai ya daga mata, Allah Allah yake tagama yasamu yafara cii ta rufe kular tasaka mai cokali ta ajiye mai,ta siyaya mai ruwa a cup ta mika mai domin tasan al'adar sace baya cin abinci sai yadan sha ruwa, yasaka hannu yakarba, yace ashe dai wannan yarinyar haryanzu bata manta halaiyata ba,yafadi hakar azuciyar sa, tana gamawa ta tashi ta juya zata fita, yace zonan ki zauna BABAY ZAHRA [9:10PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 20 na BABY ZAHRA Dawowa tayi cikin nutsuwa, tasamu guri ta zauna, yana cin abincin sa yace kaisa tace na am yace kinsan me nake so da ke tace a'a yace inace kina son saurayin ki iron nan ko, cikin sauri tace mai eh, yace to nima ina da wata wanda nake so kuma ita nake son aura, kinsan me nake so da ke, tace a'a kisami abban ki kice masa ke bakya sona kina da wanda kike so, idan yaki ki masa kuka sosae kice masa ke bakya sona, saboda ke kinsan ni ba tsarar auranki bane, idan kikayimin haka to ni namiki alkawarin zan samawa iron kin aiki a jalingo inace kince yayi diploma tace ehh ya ce to zan Samar masa aiki a cen inyaso sai kuje cen ku zauna, tunda yafara maganar sa batace mai komai ba sae da tabari yakaraci zancen sa kafin tace mai, naji abinda kace ya muktar, amma kasani ni ina da tarbiyya kuma ina da biyayya don haka bazan iya samun abbana ba, ae Kaine babba don haka Kai kasami abban ka kagaya masa cewa baka sona, inyaki sai kamasa kuka kadaga masa hankali inyaso sai yace yafasa,da kake zancen soo kuma kai shaida ne ni bana son kamar yanda kaima baka sona, biyayya nayi nakarbe ka amatsayin kaddara, sannan kuma bakayi karya ba da kace ni ba tsarar auren ka bace saboda ni miji mai addini nake nema nagari wanda yasan mutuncin 'ya mace da kimarta, wanda yake biyayya wa iyayen sa,don haka ni ban damu da namiji dan boko ko wayayye ba, da kake zancen zaka samawa iro aiki ce maka akayi baya aiki ko mai, a hakan da ka ganshi yana da arzikin da zai ciyar dani ya tufatar da ni, alhamdulillah a hakan nake son shi kuma inza abarni zan aure shi, amma ni banna son kyalkyal banza, kuma ni inda zaka je kasami su abba da maganar nan da ka taimake ni ba kadan ba, domin nima banna son ka biyayya zanyi, kaga tafiya ta BABY ZAHRA

Share:

1 comment:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).