shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 22 April 2016

SIRRIN ZAMA DA MIJI 8

sirrin-zama-da-miji.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 8}

(KIYAYE SIRRIN MAI-GIDA)

BY

MUHD*ABBA*GANA 09039016969

Dukkan mace ta gari bazata so ta yada sirrin maigidanta ba ko kuma ta fadawa wasu sirrin maigidanta musamman a cikin sha'anin abin daya shafi harkar kwanciyarsa aikata wannan laifi ne mai girma a gurin Allah domin manzon Allah (SAW) ya tsawatar da kada miji ya bawa mutane labarin abin da yake aikatawa da matarsa haka itama matar kada ta bada labarin abinda yake faruwa a tsakaninta da mijinta a cikin sha'anin kwanciya. haka kuma baya halarta a gurin mace ta hana kanta a gurin mijinta wato idan ya nemeta domin kwanciyar aure yin haka sabawa Allah ne da kuma manzon Allah (SAW) hasalima jinkiri a lokacin da miji ya bukaci saduwa da matarsa shima laifine domin manzon Allah (SAW) yace Allah ya tsinewa matan da suke cewa mazajensu sai an jima har barci ya rinjayi idanun mijin. wato su kuma wadannan in matan baza su cewa mazajensu su ba sa son jima'i ba to amma sai su dinga jan aji har sai mijin yayi barci to yin haka laifine babba don haka sai a kiyaye domin samun zaman lafiya da kuma cikar samun ladan zamantakewa a gurin Allah madaukakin sarki. abinda ya sawwaka kenan sai mun hadu a babi na gaba

Share:

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).