shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Monday, 18 April 2016

BANA KAUNARKA!!! 49

bana-kaunarkajpg.jpg

BANA KAUNARKA!!! 49

MUHD-ABBA Da Amrah

Cikin damuwa na miqe tsaye saboda wani irin ZAFIN SO (A novel by Amrah) da naji na Ya shahid, ya kishin shi da nake ji. Dad yace "koma ki zauna mana, ai ban gama ba".

Komawa nayi na zauna jiki babu qwarieh na fuskanci Dad, yaci gaba da "tunda aka daura auren Shahid kullun sai munyi waya dashi, ganin ya kasa daurewa da rashinki yasa na yanke hukuncin a hada aurenku dana mahida, ba tare da kin sani ba, yanxu haka maganar da nake miki ke matar Shahid ce".

Ido bud'e nace "what? Dady me kake fada ne? Yaushe na auri Bomboy?", Dad yace "ki kwantae da hankalinki zaki fahimci komai", Kai kawai na daga sannan yace "har mahaifiyar ki ta san da maganar auren, kuma kema inda kin kula a lokacin da ake maganar auren kusan komai sai an ambace ki, duk dangi sun sani ke dai ce baki sani ba, sannan kuma tunda aka daura aurenku na hanaki fita mara muhimmanci, ko a skul na hana ki hulda da maza baki daya sai dai mata, matan ma wanda na yarda dasu kawao".

Sai a lokacin na tuna da duk maganganun Dad, na tabbatar da ni matar shahid ce, tou ni yanzu murna zanyi ko baqin ciki? Na ma rasa abnda ya kamata nayi, gashi fai ina son Bomboy amma bazan iya zama da kishiya ba.

Note: gareku mata masu qin kishiya. Ehh tabbas kishiya abar qi ce, amma kuma sai musan kalar qiyayyar da zamu nunawa kishiyarmu. Allah da kanshi ya bada ixinin auren mata hudu indai namijin zai iya adalci a tsakaninsu. Tambaya anan itace ; shin zamu haramta abnda Allah ya halalta ne ko kuwa?, yana daya daha cikin abnda ya halakar da mutanen da sukazo kafin mu, haramta abnda Allah ya halalta, da kuma haramta wanda ya halalta. Tabbas Qur'ani shine babban abn koyi, domin kuwa a cikin shi yake dauke da duk wani abu da muka sani da wanda bamu sani ba, haka zalika Qur'ani yana kawar da duk wani baqin ciki ko damuwa, a duk lokacin da mijinki ya fada miki zai qara aure dan Allah 'yar uwa kar kiyi hauka ko nuna rashin class, dauko Qur'an kiyi karatu insha Allahu zakiji komai yazo miki da sauqi, zakiji duk wata damuwarki babu ita, zakiji kishin yayi sauki fiye da kafin kiyi karatun. Ya Allah ka qara tsarkake mana zukatan mu, ka raba mu da jahilin kishi.

ABBA GANA

DA

PRINCESS AMRAH

www.abbagana.pun.bz www.abbagana.tk

Share:

7 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).