[9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 41 na BABY ZAHRA Cikin sauri goggo indo tace to wawiya wannan kudin ne yayi yawa, bari in kirga inga nawa ne, kirgawa goggo indo tayi tsaff 300k ne cif cif , cikin sauri kaisa tace 300k goggo indo ae yayi yawa, harara goggo indo tasake mata tace wai kin mance ne bamu bayar fa da kudin dilkan ki bafa gasu kudin gyaran ma duk ba akarasa bayarwa ba, kuma ae jiya kina ji hajja fatee takirani tace an kawo turarukan wutan ki, too kawai kaisa tace, sannan goggo indo tace kuma ina son zakiyi kamu ma, tace ammafa nace masa walima kawai zanyi, goggo indo tace banni da shi zan gaya masa tace mata too ta tashi taje ta jona wayar ta a charge... Washe gari har gurin motar suka raka shi sannan yatafi su kuma suka juya gida, gidan su nasreen ya nufa, bayan sun gaisa ne take tambayar sa yasu abban jajere, kasancewar bata san yana cikin gari ba tun tuni, amsa mata yayi da suna nan cikin koshin lafiya, cen bayan sun dan taba hira ne, ya mike yace zai wuce saboda jirgin su ya kusan tashi, cikin shagwaba tace sweet baka kara min kudin ba, yace gsky nasreen kiyi hakuri saboda yanzu banda kudi, kinsan kaisa ma zatayi event so itama naje nabata nata kudin, cikin fushi tace ohhh wato kaje ka kwashe kudin ka bata kenan ni kuma ko oho ko, cikin mulki yace mata yanda na baki haka itama nabata so bana son mita pls, yayi gaba yabarta agun har ya isa mota baiganta ba, yacewa drivern ya jaa kawai sutafi, wato saboda ya hanata kudi shine yau baisami rakiyar da tasaba masa ba, kai nasreen kenan Allah dai ya shirya BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 42 na BABY ZAHRA Acen abuja kuwa komai ya kan kama na zancen biki, abba shi da kansa ya raba amaren ko wacce in aka kawota ga gun wanda zata sauka, kasancewar abba yasan momy bawai tana son kaisa bane yasa yabata nasreen, yace in aka kawo nasreen komai na hidimar ta ita da kawayenta da en uwanta suna kan momy, ita kuma kaisa yabada ta wa er uwar ta aunty rukkaya, komai na hidimar ta yana hannun aunty rukkaya ne, so komai na bikin yana tafiya dai dai ba tare da ansami wata matsala ba...., za a daura auren kaisa ran Friday while ita kuma nasreen ran Saturday, don haka komai ke tafiya dai dai
Tun ranan talata ne akafara event in nasreen, mothers day sukayi anci ansha sannan kuma an chashe, sai dai ango bai sami hallartar event in ba cewa yayi shi sai ran alhamis zaizo,washe gari ranan laraba ne akayi family nd frnds day, shima dai kamar na jiya anci ansha kuma ancashe, amarya tayi rawa sosae, Ranan alhamis ne kaisa zatayi kamun ta wanda tayi shi a cikin garin jalingo, kamu yayi kyau amarya tafito sasoe gashi kuma ango ma da abokanan sa sun hallaci bikin,bai wani zauna sosae ba a filin yatashi yayi gaba. sakamakon kiran da nasreen take ta mai saboda itama ranan take kamun ta BABY ZAHRA [9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 43 na BABY ZAHRA Bayan antashi daga kamun ne, suka koma gida dakin su suka shiga suka kwakwkwanta suna hutawa saboda gajiyar da sukayi....rukkaya kobi kawar kaisa ce da sukayi makaranta anan jalingo ita er Bauchi ce amma itama tana aure ne a abuja, ta zauna ne a gurin yayar ta anan jalingon kuma unguwar su daya dasu goggo indo, don haka mijin ta yasan su tare shiyasa ma bai hanata zuwa bikin kaisa ba, juyowa tayi tace qawata gsky kinyi sa an miji fa, wannan san talelen saurayi haka, gsky naji miki haushi da akace ku biyu zai aura naso ace ke kadai ce wlhy, amma duk da hakan dai ba wata matsala zan daura ki akan network ae, gashi ma Allah yasa gari daya zamu zauna, wacce unguwa ce ma zaki zauna, murmushi kaisa taya tace kai ke kam qawa Allah ya shirye ki wato haryanzu dai bakin nan tana nan ko, na so ace ae kamal yayi min maganin bakin nan, dariya suka yi dukkan su, rakiya ce tace ae sai an dan taimaka an dauraki akan network saboda ke innan da sauran ki anbarki a baya ae, sake shekewa da dariya sukayi, rukky kobi tace ke da Allah nikam gaya min a wacce unguwa zaki zauna, kaisa tace inaga a saraha estate ne, ihu rukky kobi tayi tace qawata ke dai kawai sai mun hadu, bari intashi inshiga gidan maman shazia kafin tafara nemana, tashi nayi narakata har kofar gida, najuyo kenan zan shige karo muka ci da shi sosae har sai da kirjina ya hadu da jikin sa, kasancewar ban kaishi tsayi ba, da sauri nace yi hakuri ya muktar wlhy bansan kana gurin ba, poster yayi don ko iya motsi baiyi ba, na ja jikina a hankali na barshi a tsaye a gurin, daki na shige nafada kan gado ruf da ciki kakkaurar ajiyar zuciya nayi, ni kaina naji awani abu, balle kuma shi, ae dolene ma yayi poster agun, tafadi hakan a ranta, bansan me ta tuna ba kuma sai naga tayi murmushi ta tashi ta zauna, rakiya ce tace mata ke kuma amarya lafiya nagan ki kina murmushi, ko dai kin tuna gobe yiwar haka kina gidan angon kine, gaban kaisa ne yayi mummunar faduwa, kuma hakane fa a she, innalillahi wa inna alaihirraji un ta furta shi a ranta ta dafa kirjin ta yana bugawa da karfi da karfi, ihu su rakiya suka sake, sai a lokacin ta tuna metayi, nan kuwa basu san mai yake damun taba tsaki tasake sannan tace lalle kukam baku da matsala wlhy, mameey yahya ce tace kema ae matsalar ki ta kare tunda gobe za akaiki gidan angon ki, tashi kaisa tayi tabar musu dakin abinta. BABY ZAHRA [9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 44 na BABY ZAHRA Washe gari da sassafe ne muktar ya turo mota aka dauki su kaisa aka wuce da su jajere dukkan su, harda goggo indo da tawagar ta duk aka dunguma zuwa jajere,
Karfe 3:00pm dai dai na ranar jumma'a ranar da takama 02/01/2015, ne aka daura auren MUKTAR USMAN SHEHU JAJERE, da amaryar sa KAISA AHEAD MALAMI SHEHU JAJERE, akan sadaki naira #100k dubu dari, tunda aka daura auren ne ango da abokanan sa suke ta daukar hotuna, shi dai muktar baisan me yakeyi ba murna yakeyi ko bakin ciki shidai yasan ya tsinci kanshi cikin annashuwa, abokan sa sai tsokanar sa suke wai mai mata biyu, dariya kawai yake musu Misalin karfe 4:30pm amare suka shirya don zuwa gurin walimar da suka hada shi anan jajere, anci ansha sannan kuma an wa'azantu sosae domin kuwa malama juwairiyya ce tazo tun daga Bauchi domin bikin kasancewar ta kawar goggo indo ce, so tayi wa'azi mai ratsa jikin kowacce mace, bayan amare sun dawo ne sukayi sallah suka ci abinci, wayar ta ce ta hau ringing, ya muktar tagani baro baro akan screen in gaban tane yafadi tunda yabata wayar nan bai taba kiranta ba sai yau, a hankali ta danna received sallama tamasa ceen kusan 5sec kafin ya amsa yace ya gida tace lfyklw, yace to daman ba wani abu bane BABY ZAHRA [9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 45 na BABY ZAHRA Daman kice wa duk wacce zataje abuja to gobe zasu wuce da sassafe misalin karfe 6:00am saboda su samu su isa da wuri don akwai DINA partyn da za ayi goben acen, amma banda ke,ke zamubi jirgin karfe 2:00pm insha Allahu, su dai ki gaya musu saboda su fara gaba, too kawai tace masa, bai kara ko 1sec ba ya kashe wayar sa bata tsamma nin ma ko yaji too inda tace in, cikin gida ta shige, gurin goggo indo taje tasanar mata da sakon ya muktar in, too fa goggo indo tace za ayi ta kenan saboda kowa zatace zataje amma bari inje in sami innarki sai muyi shawarar wa enda zasu, too nace mata sannan na koma dakin da muke nida kawaye na, sanar musu nayi da zancen tafiyar nan da nan suka fara shiri ba wasa, Washe gari kuwa Kamar yanda ya fadi 6 nayi sai ga motoci sun bai yana, ta window naji shi shida goggo indo suna magana, akan suyi sauri tafiyar basu kadai bane harda en gidan su nasreen ma, tun tuni ya tura musu mota don haka mu suke jira zasu tafi tare, amma banda kaisan don na yanka mana ticket uku ne ni da ita da nasreen, guda goggo indo tasake har sai da tasashi jin kunya tace wato mune 'ya'ya baabaa shine aka turamu amota zaka dauki matan ka kasaka su ajirgi kuyi gaba ko, sosa keya yayi yabar gun da sauri sai da ya isa bakin zaure sannan yace goggo don Allah muna jiran ku yanzu. Bakwai saura motar su ta tashi suka tafi ni daya ta aka bari a gidan, dakin inna ta na wuce nasame ta da sauran en uwa wa enda basu watse ba anan na zauna suka sakani a gaba da nasiya.. BABY ZAHRA
tnxs
ReplyDeletetnxs
ReplyDeletemunajin dadin nishadantar damu da kake da wadannan novels din, ubangiji yasaka da alkhairi. pls acigaba
ReplyDeletemunajin dadin nishadantar damu da kake da
ReplyDeletewadannan novels din, ubangiji yasaka da
alkhairi. pls acigaba
tnxs mallam abba
ReplyDeletemun gode muna jiran karashi
ReplyDeletetnxss
ReplyDeletetnxsss
ReplyDeleteameen
ReplyDeletemuna godiya
ReplyDeletetank u
ReplyDeletemun gode allah yakara basira amin.pls acigaba
ReplyDeleteTnx
ReplyDeleteMuna godiya don Allah aci gaba
ReplyDeleteAci gaba muna ta jira admin
ReplyDeleteMungde don Allah acigaba
ReplyDeleteThanks acigaba
ReplyDeleteMina godia
ReplyDeleteMUNA GODIA DON ALLAH ACI GABA
ReplyDeleteHAHAHA!!! MUNA GODIA GABADAI GABADAI PRINCE.
ReplyDelete