shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SIRRIN ZAMA DA MIJI 9

sirrin-zama-da-miji.jpg

SIRRIN ZAMA DA MIJI

{KASHINA 9}

(IYA MAGANA)


BY

MUHD*ABBA*GANA
09039016969

yana daga cikin ladubban zamantakewa wadanda yake amta mace ta kiyaye shine ta iya magana a lokacin da take hira da mijinta ma'ana ya kamata tun farkon ta sani cewa ita fa macece kuma Allah madaukakin sarki ya san ya nutsuwarta a wajen mijinta don haka yana da kyau maganarta ta zama mai farantawa maigidanta. yana da kyau mace ta zama mai tausasa muryarta a lokacin da take hira da mijinta wato ta zama kamar wata karamar yarinya mai nuna shagwaba wannan shi zai dada sa mijinta ya yarda da ita kuma harta kallo idan zaki kalli mijinki to ya kasance kallone na girmamawa da mutuntawa kuma ya zama kallone da zai tabbatarwa mijin cewa kina kaunarsa kuma kin yarda dashi har a cikin zuciyarki, kuma yana da kyau ko a fagen tafiya kada mace ta zama kamar namiji musamman idan tana a gaban mijinta don haka ya kamata tafiyarta ta zama a bisa tsari da kuma nutsuwa amma idan tafiyarta ta zama ta hauka wato irin ta masu jin karfi to wannan zai iya rage kimarta a cikin zuciyar mijinta. haka kuma yana da kyau a musulunce mace tayi shagwaba a gurin mijinta domin nana aisha (RTA) ta kasance yar lelen manzon Allah (SAW) hasalima an samu lokacin data cewa manzon Allah (SAW) sai ya dauketa haka kuma yazo a cikin wani hadisi cewa manzon Allah (SAW) yana yin tseren gudu shida matarsa wato sayyidatu Aysha (RTA) don haka wannan yana nuna mana muhimmancin kyautata mu'amalla a tsakanin mace da mijinta domin a samu jin dadi nutsuwa da kwanciyar hankali sabanin yanda harkar aure take gudana a tsakanin al'ummar wannan zamani wanda zaka mafi akasarin jama'a wato ma'auratan sun saki ka'idojin zamantakewa shi yasa ake ta fuskantar matsaloli a tsakaninsu wannan yasa saika ga hartakai suga rabuwa wanda shine mafi zama abin ki a gurin Allah (SWT) a cikin harkar aure.mafi akasarin abinda ya sa ma aurata suke samun matsaloli a cikin harkar aure shine son zuciya da suke sa a gabansu wato ya zama an daina binciken abinda Allah yace ko abinda manzon Allah (SAW) yace sai ya zama su kuma mata sun maida aure kamar wata hanyar neman wadata da kuma arziki wato kamar kasuwanci tun a farkon neman auren ba a tausassawa mai neman sai a dinga dora masa abubuwa daban daban tun yana ganin kimar matar har ma ya daina ganin girmanta dana iyayenta, kuma sai a zo ayi auren shi kuma idan ya kalli wahalar daya sha kafin ayi auren shi yasa ba zai ji tausayin matar ba. kuma a karshe dai ita ma sai tace mijin ba zai juyata ba to haka dai lamarin zai ci gaba da kasancewa a tsakaninsu a karshe sai kaga an rabu domin kuma tun daga farkon auren an sabawa koyarwan manzon Allah. zan cigaba gobe insha Allah.
Share:

4 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).