[9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 26 na BABY ZAHRA Sallamar ta ne ya katse mai tunanin sa, a hankali ta ajiye mai kular abincin a gaban sa, har ta juya zata fita yace mata zonan cikin nutsuwa ta dawo ta zauna, ya ce mata kaisa ni sa'an ki ne? A'a kawai tace masa, yace to amma meyasa kika rai nani ko don kinji ance miki ni zan aure ki shiyasa kika bi kika raina ni, cikin nutsuwa da fahimtar juna yake mata maganar, bata ce masa komai ba har sai da tabari yagama maganarsa sannan tace haba ya muktar yanzu don kawai ance min kai zaka aure ni sai kawai in raina ka ae yanzu ne ma yakamata in girma maka ta yanda baka zato, indon ban kawo maka abinci da kaina bane yabata maka rai to don Allah kayi hakuri, insha Allahu irin haka bazai kuma faruwa ba, shiru kawai yayi yana mata wani mugun kallo wannan yarinyar ko duk yanda ka kai da bacin rai tasan ta yanda zata shawo kanka da kalamai masu dadi nan da nan kaji zuciyar ka ta kariya, sai yace mata to ina son kimin wata alkawari guda daya, cikin sauri tace ya muktar inajinka indai har baisabawa addini ba ni kuma namaka alkawarin koma meyene zan maka shi matukar zai faranta maka rai, yaji dadin kalaman ta ba na wasa ba, sannan yace ina son kimin alkawarin baza ki sake tsayuwa da wannan saurayin naki ba, saboda kinga abban ki baya son kina tsayuwa da shi don haka sai ki kiyaye bacin ran abban ki, BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 27 na BABY ZAHRA Ni kinga gobe in Allah ya kaimu zan koma abuja kuma jirgin karfe 9:00am zan bi, don haka zan bar nan da safe, cikin nutsuwa tace insha Allahu na maka alkawarin bazan kuma tsayuwa da shi ba amatsayin saurayi da budurwa, sannan kuma Allah ya kiyaye maka hanya, inka isa ka gaidamin da su zahra, yace to zasuji, tashi kije.... A hankali ta tashi tayi fucewar ta, binta kawai yayi da kallo yace a ransa wannan yarinyar inda namiji ce ita bakaramin yaudara zatayi ba saboda kalaman bakinta masu dadi, gsky kalaman ta sunyi gashi kuma.........yayi sauri ya kawar da tunanin ta daga ransa... Washe gari da sanyin safiya yatashi ya kammala komansa yashiga cikin gidan yasamu abba ya sallame shi ya sallami inna ya dakko kudi mai yawa yabawa inna taki karba shi kuma ya ajiye mata akasa adakinta yayi fucewar sa waje, kicibuss sukayi da kaisa a dai dai zauren gidan, ina kuma kikaje da safen nan ta sunkuyar da kanta kasa sannan tace mai naje sayo kosai ne, yace meyasa baki aiki su nana ba bana son yawan yawo fa, ooh su muktar akwai son iko da mutum, a hankali tace mai lokacin basu tashi a bacci bane, kuma nayi saurin zuwa ne saboda in kawo maka kasamu kaci kafin kafita ashe ma har ka fito, yaji dadi sosae saboda kaisa tana bala'in kula da cikin sa ta yanda baya zato ko shi bai kula da cikin sa Kamar yanda ita take kulamasa da cikin sa, dan murmushi yayi yashafa gen fuskarta yace karki damu inna je gidan su nasreen zanyi breakfast, wani yarrrr taji tundaga kanta har zuwa tafin kafanta, sakamakon shafa fuskarta da muktar yayi BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 28 na BABY ZAHRA Wucewar sa yayi baima san yayi ba, tana tsaye a inda yabar ta har saida abban ta yazo wucewa ne kafin hankalin ta yadawo jikin ta, da sauri ta fice kofar gida tasamu harya saka kayansa a bayan both suka iso inda motar yake ita da su abba suka mai sallama ya shiga motar suka dagawa juna hannu yayi kwana da kan motar yatafi sannan suka shige cikin gida... Zaune yake akan kujera 2 setars nasreen ce kwance akan kafadar sa sai zuba masa shagwaba takeyi yana ta faman lallashin ta, da kyar ya kwaci jikinsa anata saboda karyayi missing flight ganin har 8:30am ya wuce, da kyar suka rabu sai a hakan ma sai da yayi mata alkawarin next month zai zo, harda ita a en rakiya har airport suka rakashi sai da sukaga tashin jirgin su kafin suka koma gida... * A cen abuja kuwa shirye shirye ake tayi bana wasa ba ana wancen ana wancen duk na shirye shiryen bikin muktar, gida abba ya gina masa manya guda biyu a hade gidan suke gate zaka gani guda biyu irin daya komai na gidan iri daya ne, daya na kaisa daya kuma na nasree , su momy ba shiga ba fita ta gama gayawa kawayen ta matan manya kaf akwai auren shalelen ta, bakincikin ta daya ashine auren nan harda kaisa BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 29 na BABY ZAHRA Duk farincikin da takeyi daga zaran ta tuna auren nan har da kaisa aciki sai taji ranta yayi mummunar baci tsaki taja sannan tanemi gu ta kwanta...momy kenan Tunda sakon auren kaisa yasami goggo indo, take ta shirye-shirye ba kakkautawa, tayi murna sosae dajin cewa kaisa muktar zata aura, tunda taji su biyu za a hada su sannan taji wancen in er sarki ce, shikenan kuwa goggo indo ba zama, duk wani kaya datasan anawa yarinya er gata to sun hada karfi da karfe ita da abban abuja sun ma kaisa ko su momy basu san iya kudin da abba yabayar don ayiwa kaisa kayan daki ba, kasancewar dakunan ta guda uku ne to haka aka cika mata su da kaya tamm gado uku aka mata kuma dukka royal bed ne, parloun ta kuwa wasu luntsuma luntsuman kujeru aka saka mata,ga TV nan plasma LG, anythings dai da ake sakawa a palour to sun saka mata, dayake auren nagida ne, ana siyan kayan direct gidan ake kaiwa ko muktar in bai sani ba balle su momy, abba ne da goggo indo suketa kaiwa da komowar su, don haka ko su kaisa ma basu san abinda ke tafiya ba abban jajere ne kawai yake sane da abinda ke tafiya, kayan kitchens kuwa ba irin wanda goggo indo bata siya mata ba matukar muna amfani da shi a gida Nigeria, saboda kitchen in nata babba ne sosai, shiyasa sukaji dadin cika kaya aciki, gida yayi kyau nagani nafada, mata kawai yake jira....Allah dai yakaimu lokacin auren nan BABY ZAHRA [9:11PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 30 na BABY ZAHRA Kwance take shame shame har da karin ruwa na karya da ake saka mata, mai martaba ne da fulani da waziri da Dr adam akan ta, Dr adam ne ke musu bayani, gsky ranka shi dade yarinyar nan tana cikin hatsari fa, ya juya ya kalli fulani yace ranki shi dade shin ko akwai abinda yake damun gimbiya ne, shiru fulani tayi, Dr adam yaci gaba da bayani gsky to zuciyarta yana gabb da harbuwa, sakamakon yawan tunani da takeyi, inda hali yakamata a kwantar mata da hankali don samun kwanciyar hankalin zuciyar ta, ko zai daina harbawa da sauri da sauri, maimartaba ne ya juya ya kalle fulani yace mata ko kinsan abinda ke damun 'yata, a hankali momy tace masa a'a yace to abamu guri da ita zamu gana, kowa da kowa ya fita yabasu guri zama yayi abakin gadon yakamo hannun nasreen yace babyn daddy me yake damun ki, hawaye ne ya gangaro ta gefen idanun ta, maimartaba yace a'a banna son kuka kawai kigaya min meke damun ki, a hankali ta budi baki cikin murya irin na marasa lafiya tace daddy fulani ce tace wai bazan auri muktar ba ni kuma shi nake so, cikin shagwaba ta furta maganar, daddy yace bangane bazaki aure shi ba saboda me, nasreen tace wai don saboda anmishi alkawari da wata er uwar sa, shine akace mai sai dai ya aure mu tare, da nima ban yarda ba to amma daya min bayani shine na yarda naso in fahimtar da fulani amma taki sai fada take min wai tun kafin inshiga gidan shi wai harya min kishiya, murmushi maimartaba yayi sannan yace ki kwantar da hankalin ki bbyn daddy auren ki da muktar kamar anyi angama ki watstsatsake ki fara shirye shiryen bikin ki nan da sati shidda 6weeks in Allah ya kaimu,cikin jin dadin abinda daddy yafada nasreen ta hau dariya tana godiya wa daddyn ta har ta mance da zancen wani ciwo, girgiza kai kawai daddy yayi yatashi yafito BABY ZAHRA
Friday, 22 April 2016
Popular Posts
-
Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka barkanmu da sake saduwa daku a cikin sabon shirin namu wadda yake zuwa muku kai tsaye daga shafin “Abba...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 76 BY MIEMIEBEE Hannunsu ta had’a tana murzawa a hankali, “I’m ready Habeebi.” Har yanzu ya kasa yarda, “Flower are...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 56 BY MIEMIEBEE Wani irin tausayin daya jima be mata irinsa ba ya soma jimata yau, azabarcaccen k...
-
[9:09PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA page 1 na BABY ZAHRA Kayatatciyar daki ne mai dauke da ko mai na more rayuwa, alarm ce ke bu...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 89 BY MIEMIEBEE Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani s...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 68 BY MIEMIEBEE Kasa koda amsashi tayi wani kunya taji ya rufeta, she can’t believe abinda ta aikata sede kuma ...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 74 BY MIEMIEBEE D’ayan hannunsa ya aza a hab’arta tare da d’ago fuskartata. “Flower you don’t have to be sorry baki...
-
TANA TARE DA NI... TANA TARE DA NI... PAGE 61 BY MIEMIEBEE ★‡★‡★‡ PRISON HOUSE MAIDUGURI, BORNO STATE. K’aramin gate ne ya bud’u...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 75 BY MIEMIEBEE Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, buf...
-
TANA TARE DA NI... PAGE 01 BY MIEMIEBEE ANAS K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno. Da yammacin ranan Asab...
About Me
- Muhammad Abba Gana
- Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).
Blog Archive
-
▼
2016
(217)
-
▼
April
(35)
- WAYE SANADI?? 2
- WAYE SANADI 1??
- Abubuwa uku
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 9B
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 9
- SAUYIN RAYUWA 71 (KARSHE)
- SAUYIN RAYUWA 66____70
- SAUYIN RAYUWA 61___65
- SAUYIN RAYUWA 56____60
- SAUYIN RAYUWA 51___55
- SAUYIN RAYUWA 46___50
- WAI ME YASA???
- SAUYIN RAYUWA 41___45
- SAUYIN RAYUWA 36__40
- SAUYIN RAYUWA 31__35
- SAUYIN RAYUWA 26___30
- SAUYIN RAYUWA 20___25
- SAUYIN RAYUWA 16__20
- SAUYIN RAYUWA 11__15
- SAUYIN RAYUWA 9 & 10
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 8
- SAUYIN RAYUWA 6-7 & 8
- SAUYIN RAYUWA 1-2-3-4 & 5
- BANA KAUNARKA!!! 50 [KARSHE]
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 7
- BANA KAUNARKA!!! 49
- BANA KAUNARKA!!! 48
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 6
- BANA KAUNARKA!!! 47
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 5
- BANA KAUNARKA!!! 46
- BANA KAUNARKA!!! 45
- WAINAR HANTA
- BANA KAUNARKA!!! 43&44
- SIRRIN ZAMA DA MIJI 4
-
▼
April
(35)
Sassa
- AMINAN JUNA
- BANA KAUNARKA HAUSA NOVEL
- DAN ALHAJI HAUSA NOVEL
- DILKA & HALWA
- DOMIN KE DA MIJINKI
- GUZIRI MAFI KYAWU
- HAUSA NOVELS
- INSIYA
- KAUNA CE SILA HAUSA NOVEL
- KUKAN KURCIYA
- MU DAUKI DARASI
- mu koyi sana'a
- MY kitchen
- NA DAINA SO HAUSA NOVEL
- RAYUWAN NIHILA
- rayuwar fauziya hausa novel
- SASHIN YAN UWA MATA
- siffofin uwa
- TSORATARWA.
- WAYE SANADI
thank
ReplyDelete