shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Wednesday, 27 April 2016

SAUYIN RAYUWA 66____70

sauyin-rayuwa.jpg

SAUYIN RAYUWA. page 66 na BABY ZAHRA
Da sallama tashigo, tasame su jigum jigum, muktar na kujera, kaisa na kasa, da sauri suka dago don ganin wake sallama, kallon junan su sukayi cikin makaki, murmushin karfin hali tayi, sannan tace nabaku makaki ko, inda kaisa take gun tanufa tazauna kusa da ita, sannan tace sister kiyi hakuri da abinda yafaru dazu nasan nayi kuskure, wlhy sharrin shaidan ne, da kuma mugun kishi dayake damuna, san......rufe mata baki kaisa tayi tace bakomai aunty nasreen komai ya wuce, ni fatana shine mu zauna lafiya a tsakanin mu, insha Allahu nasreen tace, tashi sukayi suka nufi inda mijin su yake, tsugunnawa sukayi akasa sannan suka bashi hakuri, rugumesu yayi dukkan su, sannan yasaka musu albarka....addu'o'i sukayi sannan suka shafa, suka roki Allah daya basu zaman lafiya a tsakanin su.
Wunin ranan kaf nasreen a gidan kaisa tayi shi, sukayi abinci tare suka citare, bata koma gidan taba har saida sukayi abincin dare sukaci, bayan tayi sallahr ishshane tayi musu sallama, muktar ne yarakata har gida, suna fita kaisa ta fada wanka, sama sama tadan shafa mai, ta murza powdar a fuskarta, sannan ta dakko sleeping dress brown colour iya cinyarta ya tsaya, tafeshe jikinta da turaruka masu kamshi, sannan tafito parlour a parlourn tasameshi, cikin kissa tace mai babyluv harka dawo, harara yasake mata sannan yace tun dazu nadawo har naje nayi wanka amma ke baki fito ba, kinshanyani inata zaman jiranki, ae na dauka yau inma rufe min kofar za ayi, murmushi tayi cikin kunya tace mai na isa.
BABY ZAHRA
[9:12PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 67 na BABY ZAHRA
Tace mai na isa, yau fa kai angone ko kataba ganin inda aka rufewa ango kofa, murmushin jindadi yayi, yace nasani ko za a fara akaina, zuwa tayi inda yake zaune, ta zauna akasa, da sauri yarikota sannan yace kintaba ganin inda amarya ta zauna a kasa, tace masa sosae ma kuwa, yace a'a kam ba dai amarya ta ba don haka zoki zauna akusa da angonki, rufe fuskarta tayi da tafin hannun ta, shida kanshi yadagota ta hau kujeran yajawota jikin shi, yace yanzu kinsan me zamuyi, kai kawai ta girgiza mai, yace tashi muje muyi sallah ko, too tace mai, sannan suka tashi suka shige cikin dakinta,
Bayan sun idar da sallahr ne yafito mata da ledar kaza cikin mamaki tace kai harda wani kaza sai kace wata amarya, cikin sauri yace mata to ae gashi kinfadi sunan da bakinki, murmushi kawai tayi, sannan yabude musu ledar ya yanko namar yasaka mata abaki takarba, itama ta yanko tasakamai yakarba, a hakan suka ciyar da junan su har suka koshi, bayan sun koshine suka koma falo suka saka film suna kallo, tana kwance ajikin sa, sai wasa sukeyi, tanata dan koke koke na shagwaba, cen dai misalin karfe 11:00pm, yatashi yakashe komai yakulle ko ina, cakk ya dauketa saboda jikinta duk ya mutu, dakinta suka nufa, yajiyeta akan gado, sannan ya hau aiki, (nidai danaga abin yafi karfin ganina falo nadawo na manna kunnena ajikin kofar kukan kaisa nake jiyowa tanata mai magiya amma ina muktar kam yayi nisa, Allah sarki kaisa taban tausayi bana kadan ba, kamar inshiga inkarbeta amma ina, yana iya masoyane suna son junan su) misalin karfe 4:00am ne yataimaka mata tashiga toilet tayi wanka, shi da kanshi ya gasamata jiki sosae, sannan yadawo da ita ya kwantar nan da nan bacci ya dauketa
BABY ZAHRA
[9:13PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 68 na BABY ZAHRA
Misalin 11:00am ta farka ido biyu sukayi da shi yana zaune ya hada tagumi, yanaga nin ta bude ido yazo da sauri, hannun ta yarike yace bbyluv kin tashi, harara ta galla mai sannan ta fisge hannun ta tajuya mai baya, murmushi yayi yace haba babyna gwiwata a kasa ayimun afuwa, ba donni ba, kuka tasake masa cikin hanzari ya hauro gadon ya rungume ta yanata lalla shinta, dayaga taki tayi shiru ne yace mata to tunda kinki yin shiru bari kawai mukara wani inyaso sai kiyi kukan da tushe, a razane tamike ta hau tattare tattaren kayanta ta nufi ban daki, takama wankan da bata shirya ba, dariyar mugunta yayi sannan yatashi ya hado mata abin karyawa, tana fitowa ta zauna don daman yunwa takeji, abaki yarinka bata harta koshi
A haka dai RAYUWAR su ta SAUYA daga ki zuwa so

Bayan sunyi wata daya ne ranan jumma'a suka shirya don zuwa gaida su momy, a gidan nasreen sukayi girke-girken da za su kaimusu, basket uku sukayi daya na abba daya na momy dayan kuma na aunty rukkaya,
Suna isa zara'u tafito ta rungumi nasreen, amma bata cewa kaisa ko sannu ba, don haka abinda tayin yabatawa nasreen rai, sai tace mata kanwata ga sister na baki mata sannu da zuwa ba ko baki ganta bane, abin yabawa zarah mamaki, sai kawai ta basar tace sannu da zuwa, yauwa kawai kaisa tace mata, dakin momy suka nufa, momy datagan su tare tasha mamaki, gashi sai wasa sukeyi da dariya, wai me yake faruwa ne, nan da nan wata zuciyar tace mata to ke ina ruwan ki, me na damuwa, tunda suma sun hada kai kam meye naki na damuwa, daga kafada tayi alamar ko ajikin ta, don haka ta karbesu hannu bibbiyu, bayan sun gaisa da momy ne suka sake dunguma sukayi dakin aunty rukkaya, nan ma itama tayi murna da ganin su haka, tayi musu addu'ar fatan alkhairi,falon abba suka nufa, bakaramin albarka ya kwararamusu ba, sannan daga bisani suka koma gidan su,
* * * *
Gida mai kyau nagani nafada abban abuja yasayawa abban jajere a cikin garin jalingo,ya kuma danka masa halak malak, don hakane ma aka saka sunan abban jajere ajikin takardun gidan, nan da nan suka tattara suka koma cen, don haka yanzu haka iyayen kaisa sun dade da koma cikin jalingo da zama
* * **
Nasreen na kwance yau kwata kwata bata ganewa jikin taba, tun safe take ta amai komai tasaka abakinta sai ta amayar da shi tarasa meyakeyi mata dadi, gashi taki tagayawa muktar, tana cikin tunanin ne sai gashi yashigo yasameta acikin bargo sai rawar dari takeyi
BABY ZAHRA
[9:13PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 69 na BABY ZAHRA
Subhanallah yace sannan yakaraso gurinta da sauri yadafa kanta yace sweet meyake faruwa kasa magana tayi, sai hawayene kawai ke zuba a idon ta, da sauri ya dakko waya yakira Dr sa yayi mai bayani yace masa gasanan zuwa, Dr na isowane daya dan dudduba jikinta yace tayi fitsari takawo, bayan falmata tariketa takaita bayan gidane, takawowa Dr fitsarin yatafi dashi yace abashi 15mnt yana zuwa......ba yan yadawo ne yake tabbatar wa da muktar cewa nasreen ciki ne da ita amma za asaka mata ruwa, bakaramin murna muktar yayi ba, har da kyauta yabawa likitan, shikenan aka shiga tattalin ciki
Da murnarsa ya zo yaga yawa kaisa cewa nasreen cikine da ita, itama tayi murna banawasa ba, sannan taboye masa nata cikin, saboda kaisa irin mutanen nan ne wanda basa laulayi, sai dai dan abinda baza arasa ba, amma kuma tana da dauriya shiyasa ma bata bari yasani ba
* * * *
Haka dai suka cigaba da renon ciki, muktar da nasreen basu tashi sanin kaisa nada ciki ba sai da ya kai wata 5mnth da sukaga abu yafara fitowa, da suka titsiyeta sai tace itama batasan tana da shiba sai da taga yafara fitowa kafin tasani, a hakan kuma suka yarda
Da watan haihuwar su yakama ne goggo indo tadawo gidan kaisa, nasreen kuwa dama already tanada masu kula da ita amma duk da haka goggo indo na kula dasu dukkan su
BABY ZAHRA
[9:13PM, 3/18/2016] baby zahra: SAUYIN RAYUWA. page 70 na BABY ZAHRA
Ranan alhamis ne nasreen tatashi da nakuda, goggo indo ce takaita asibiti da muktar, hankalin kaisa duk Ya tashi, bayan 1hr ne sai gasu da santaleliyar yarinya mai kama da uwarta sak, murna agun kaisa kamar zatayi yaya, kwanan ta uku da haihuwa gidan yacika da jama'a, en fada sunzo mota uku,
Ranar suna ne yarinya taci sunan momy wato hafsat ana kiranta da HAIFA anci ansha,
Aranar da akayi sunan ne kuma kaisa a asibiti ta kwana, har sai washe gari tasamu ta haihu, ta haifa santalelen yaron ta mai kama da uban sak, bayan an fito da yaron ne, ana shirin yanka cibine kuma wata sabuwar nakudan ta tasowa kaisa, bakaramin mamaki likitocin sukayi ba don ba wata alama da tagwada en biyu ne acikin kaisa, amma sae me....santaleliyar yarinya ce ta biyo baya da hancinta irin na uwarta sak, da aka fito aka gayawa su goggo indo da muktar basu yarda ba, sun dai ce dai kawai inta haihu agaya musu, likitanne yace abokina da gske nake muna needing wani kayar jariyar da za sakawa dayar, goggo indo ce tafita da gudu bakin asibitin taje tasiya agurin masu sayarwa, ta dawo da gudu ta basu, muktar baitashi yarda ba sai da yagansu da idon sa, sujjada yayi agurin, yana mai godewa Allah daya bashi irin wannan kyautar, kara duba su yayi mace ce da namiji, rungume su yayi sosae, cen saiga kaisa ta fito goggo indo ce ke rike da ita dakyar take iya tafiya, muktar kamar zai hadiyeta yakeji, suka shiga motar sukayi gida
Kowa yasha mamakin haihuwar kaisa, gida ya kacame da murna...
Ranan suna ne yara sukaci sunan abban abuja da kuma innar kaisa, wato usman da amina, usman ana kiransa da aarif, ita kuma amina ana kiranta da aafreen
BABY ZAHRA
Share:

5 comments:

 1. UMMU AMATURRAHAMAN28 April 2016 at 00:45

  ALLAH YA KARA MAKA BASIRA DA FATAN DA ACI GABA MUNA JIRA {PRINCE}

  ReplyDelete
 2. Allah ya karo basira

  ReplyDelete
 3. Haka yayi kyau

  ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).