shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Friday, 27 May 2016

WAYE SANADI?? 17---20

waye-sanadi.jpg

WAYE SANADI?

17


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

taso muje ki rakani gurin ummanki oh mama ita ma yanxu ta tahi daga nan zo muje dakin daddy kinga shima saiku gaisa ta mike ta jawo hannuna muka nufi wani barin daban shima waje ne mai kyau yana zaune kan kapet ummansu tana hada masa tea yana ganina ya hau murmushi safiyya har kin yi shirin makaranta banyi magana ba har muka karasa gabansa nace antashi lafiya lafiya klau ya kan naji sauki yanzu dakyar na danne zuciyata nace mata sannu da aiki sannan ta dago fuskarta a daure ta dago kai ke za'a yiwa sannu ta mai da kanta taci gaba da juya shayi yadda fuskar maryam da na daddynta sun nuna basu ji dadi ba, a zuciya ta nace kar ma ki damu ni da kaina zan yi maganinki duk abinda ta taka nima shina taka na mike zan tafi makaranta. to safiyya ungo ki hau mota nasa a nemo miki direban da zai dinga kai ki da dauko ki tunda muka zauna zanyi break maryam dasu abba suke ta jana da hira ban basu wani cikakkiyar amsa ba daga E sai a'a na mike zan tafi abba ya mike nana bara na karbo key na kaiki ba dan naso ba na amsa masa da toh tunda muka tafi yake ta jana da hira ina kokarin kauce amsa dan dukansu haushinsu nake ji "nana safiyya tunanin me kikeyi? ina ta magana kinyi shiru,bbu tunanin da nake kawai dai maganar ce bana sonyi kamar ance juya naga sadiya a tsaye a titi ka sauke ni anan ga kawata can sai kawai mu karasa haba ya za a yi na bar kanwata a nan bari ita ma na dauke ta sai na kaiku tana ganin mota ta tsaya a gabanta ta dauke kai daga wajen ganin an bude yasa ta fara tafiya ina kuma zaki? jin murya ta yasa ta juyowa lalala safy kece daman kinga lokacin yana tafiya kizo mu karasa school ta shiga baya,sannu ina kwana lafiya klau ya karatu? har muka karasa bbu wanda ya kara magana yayi parking sadiya ta fita har na yunkura zan fita naji maganar abba sufy sunan ya min dadi sosai gashi kya yi break ka barshi daddynku ya ban nasan ya isheni kan yayi magana na fice banko tsaya ba rufe masa murfin ba na karasa wajen sadiya. sufy daman shine darling din amma gaskiya kun dace ya sunansa? Allah ke wani lokaci dariya kike ban kawai daga kinga mutum sai wani surutu kike nifa duka yau na fara ganinsa kuma wallahi haushinsa nake ji kamar na kashe shi dama daurewa kikai kenen 'daina yi min tadin shi"


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

18


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz


gaskiya sufy baki da mutunci to me yasa kika shiga motarsa har ma kuma ya akai ya sanki,kinga bara nayi miki a takaice wannan aban dan mijin ummatane,dan ni bana kaunar maganarsa nakeba,kai suffy Allah ya gyara miki na zaro waya ta kira na gani har guda uku sai kuma message daya zuciyata ta kasa samun nutsuwa hankalina ya kasa tattatuwa waje daya har sai da naji muryar yarinya kin tashi lafiya? kiransa ne ya shigo ban karasa karantawa ba nayi saurin dagawa cikin hargagi nace wai kai baka da hankali kana kiran matar aure banza.na kashe waya uhum wallahi nana kibi a hankali ba ayi wa namiji haka"na juyo ina hararanta ke kin cika abin haushi goya mazan zanyi bara kiji ni a tsarina dana kula namiji gara na zauna ban magana da kowa ba saboda me? kai tsaye na bata amsa saboda bana kaunarsu meye dalilinki? sadiya ni kaina ba zan iya kawo miki dalili ba illa dai kullum zuciyata tana gayan namiji bai da wani buri na gari akan mata shi dai burinsa daya ya cuceki ya gudu ya barki tsanata ta dada karfi akan namiji tuna na karanta wani littafi "yaya sunansa littafi kuwa waye yayi shi? sabon marubucine, sunan littafin NA DAINA SO wallahi sadiya naji na tsani duk wani na miji na tsane shi to an ce miki duka mazan halinsu dayane duk abin da zaki ji a littafi karya ne kawai dan a fadakar ni kam ban yarda da abinda na ke gani a littafi ba.wai wayene yayi? ina jin sunansa muhd abba"to kinga ni duk cikin marubuta bbu wanda nake jin dadin littafinta irin "hauwa jabo" labarinta yana burgeni jiya sai dana karanta sabon littafinta mai suna"hasken idaniya" yayi dadi sosai kuma dana koma zan sa a nemo min wannan din ya sunansa"NA DAINA SO. muna shiga class na dauko wayata zan kashe naga wani message nana jiki na yana gayan baki da aure ki daure muyi magana ta nutsuwa imran S. gabanane yayi mummunar bugawa waye wannan yasan sunana na shiga tambayar kaina na shiga uku kaddai ace aljani ne. lafiyarki kuwa kina ganin malami ya shigo nayi saurin kashe wayar na jefa cikin jaka tun dana koma gidan alhaji nasir naji rayuwata ta sauya kamar lokacin na fara rayuwa nayi kyau sosai lokacin na san ina da kyau gaskiya sai yanzu na san ina rayuwa me kyau kayya kam har bana iya irgawa ni da ummata duk abinda muka bukata alhaji nasir yana yi mana daidai da rana daya bai taba nuna gazawarsa ba,



Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

19


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

tsakani na da matarsa da yarsa bbu mai shiga harkar wani tunda muka yi fada da maryam shikenan babarta ta kafan kagon zuka nima bana rangawanta mata umma bata taba cemin na bari ba shima maganarsa daya nayi hakuri. yau ban shiga school ba misalin karfe sha biyu na tashi na shiga dakin alhaji nasir yana jin bbc maryam tana zaune a kusa dashi ban koh yi sallama ba na shiga na zauna a kan kujera kusa dashi na juya ina kallon fuskar maryam harara ta zabga min nayi mata murmushi na juya ina kallonsa sannu da aiki abinda bai taba jin nayi masa ba cikin mamaki ya amsan yana tambayata ko da wata matsalar ce maka zanyi ina son zan shiga islamiyya shine nake so ka yankan form kuma yanzu naiya mota da kaina ina so ka sai min mota mai kyau ta zamani. safiyya duka kwananki nawa kina koyar motar? wannan ba damuwarka bace ni dai nace ina bukatar mota shikenan safiyya zan siya miki sannan maganar islamiyyar kin taba yin wata koko a nan xaki fara? tun muna fanshekara har muka koma dorayi ko lokacin da na daina zuwa izina arba'in. shikenan safiyya in yamma tayi zan je sai na yanka miki form din. haba daddy yanzu har agola tafi mu daraja tazo maka da bukata bbu ladabi sai magan ganu kai tsaye ta zo ta zauna kusa da kai abinda ko momy ba tayi maka haka amma ita sabida ba ta da tarbiyya ta zo ta zauna kusa da kai, sannan dady nafi shekara ina cewa ka sai min mota amma baka sai min ba ko su yaya da abba ma baka sai musu ba sai tsohuwar taka ka basu amma ita tana tambaya har ka amsa mata wallahi ba zaki hau motar ba tunda ba uban.........kan ta karasa ya sakar mata mari daman baki da kunya safiya ba gaba dake take ba tashi ki bar min daki mara kunyar banza fita tayi tana rusa ihu juyowa yayi yana kallona safiyya kiyi hakuri insha Allahu gobe zan shigo miki da motarki wai ina wayarki ne ban taba ganinki da ita ba tana nan kawai dai na ajeta saboda karatu okey na mike ina zuwa daidai kofar fita naji an zabgamin mari ina dagowa banyi wata wata ba na zabge mata mari har sau biyu kururuwa ta saka da sauri ummata fito tana tambayarta lafiya zakice lafiya mana munafuka bada daurin gindinki take komai ba to wallahi bazan yarda ba agola ta dagar hannu ta mare ni har sau biyu ta juyo kan ummana nayi saurin shan gabanta ni nayi miki ba ita ba dan haka karki kuskura ki taban umma in ki kace zaki taban umma kina ganin zan rabu dake to gata nan ki taba ta batun yau nake ganin ta kun ku ke da yarki wallahi in din gudace banza jaka me kishi akan namiji.


Abbagana hausa novels @ facebook.
WAYE SANADI?

20


MUH'D*ABBA*GANA
09039016969

www.abbagana.pun.bz

naja hannun ummata mukayi daki wallahi alhaji kayi kadan ka wulakantani a gabanka yar matarka ta maren har sau biyu baka yi magana ba kuma a kanta ka mari yarka to wallahi bazan zauna ba gara na tafi in kina ganin tafiyar ta fiye miki alkairi to sai kin dawo in kuma zaki iya tsayawa ki sauraran to, yana fadar haka ya juya yayi daki tunda muka shiga daki nida umma zaune take tayi tagumi umma tun dazun na tambayeki kinyi shiru ko dan nayi fada da kishiyarki kike jin haushina' nana ba haushinki nake jiba jikina kaka nake tunani tun shekaranjiya take kwance ya kamata kije ki dubata nana tunda kika dawo gidan nan kusan wata tara kenan baki taba zuwa kun gaisa ba ya kamata ki jeki ga ya jikin nata yake. wallahi umma bbu inda zani kawai kina so kice na bar gidan mijinki saboda yana da kudi bakya so na zauna naci arziki kuma yau zan bar.gidan "na mike na shiga dakina bata koce min kala ba na shiga hada kayana har na gama na dau jakata na ganshi a tsaye, safiyya mayar da kayanki kiyi hakuri kuma gobe in zaki makaranta ki biya ki gaida baba karki min gardama Allah yayi miki albarka ya juya ya fita kawai naji yau yaban tausayi dan haka na juya na mayar da kayana bayan kwana uku ina zaune a falon umma ina kallo ya shigo ko kallonsa banyi ba umma ta fito tana yi masa sannu da zuwa,na mike zan shiga daki naji muryarsa safiyya ga alkawarinki da nayi miki na juya ina kallonsa wane alkawari na fada ina hararansa, motarki an kawo ga key din kuma naje islamiyya na yanka miki form har an cike gobe zaki fara zuwa. hannu nasa na karba nayi cikin daki umma ta juya tana kallonsa an gode Allah ya kara arziki. amin rukayya na gode da addu'arki na kuma ina adduar Allah ya barmu tare har karshen rayuwarmu keh har gidan aljanna. murmushi tayi ta sunkuyar da kai ya mike ki mikon abincina.
ni kam tunda na shiga daki nake tikar rawa yau nice nake da mota sabuwar rayuwa tazo yaya sadiya zatayi in ta ganni da mota Allah Allah nake gari ya waye na tafi school. umma ce ta turo kofar ta shiga tana hararata sannu mara kunya 'umma me kuma nayi? ban sani ba wallahi nana in baki canja wannan mugun halin naki ba bazaki taba jin dadin rayuwarki ba ace mijin mamanki ya zama makiyinki mutumin nan burinsa ya kyautata miki amma dai dai da rana daya baki taba masa godiya ba, tsakaninki da shi sai harara kamar sa'anki."


Abbagana hausa novels @ facebook.
Share:

1 comment:

  1. Abubakar Ibrahim3 June 2016 at 13:30

    Amma yarinyar nan Allah ya shirya

    ReplyDelete

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).